Shin Kun Haramta Kallon Wasu Fina-Finai ko Karanta Wasu Littattafai ko Kuma Saurarar Wasu Wakoki Ne?
A’a. Kungiyarmu ba ta bincika fina-finai ko littattafai ko kuma wakoki don ta iya tsara wa mabiyanta doka a kan irin wadanda ya kamata su kalla ba. Me ya sa?
Littafi Mai Tsarki ya karfafa kowannenmu ya horar da ‘hankalinsa’ don mu iya sanin nagarta da mugunta.—Ibraniyawa 5:14.
Nassosi sun jera wasu ka’idodi da za su iya taimaka wa Kiristoci wajen bincika kowane irin nishadi don su san wanda za su zaba. a Kamar yadda muke yi a kowane fannin rayuwarmu, burinmu shi ne mu rika “gwada abin da ke na yarda ga Ubangiji.”—Afisawa 5:10.
Mun koya daga Littafi Mai Tsarki cewa miji yana da iko bisa iyalinsa, saboda haka, zai iya tsai da shawarar a kan irin nishadi da ya kamata iyalinsa su yi. (1 Korintiyawa 11:3; Afisawa 6:1-4) Amma, babu wanda yake da ikon zaba wa wani ko wata a cikin ikilisiya a kan irin fina-finai ko wakoki ko kuma littattafan da ya kamata su rika karantawa, sai a iyalinsa kadai.—Galatiyawa 6:5.
a Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya haramta duk abin ya shafi sihiri da lalatar jima’i da kuma nuna karfi.—Kubawar Shari’a 18:10-13; Afisawa 5:3; Kolosiyawa 3:8.