Muna Gayyatar Ka Zuwa
Farin Ciki Har Abada
Taron Yanki na Shaidun Jehobah na 2026
Ka Nemi Inda Za A Yi Taron Kusa da Inda Kake
Kyauta Ake Shiga • Ba a yawo da tire don karɓan kuɗi
Wasu Abubuwan da Za A Gudanar
Jummaꞌa: Za mu bincika yadda Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana da cewa Allah da Ɗansa, Yesu suna so mu yi farin ciki.
Asabar: Za ka ga yadda bincika Huɗubar Yesu a kan Dutse zai taimaka mana mu yi farin ciki har abada.
Lahadi: A jawabin nan mai jigo “Shin Ka Sami Dukiyar Nan Mai Daraja?” za ka ga yadda gaskiyar Littafi Mai Tsarki ya sa mutane da yawa farin ciki.
Wasan Kwaikwayo
Labarin Hidimar Yesu: Sashe na 4-6
Za ku ga yadda Yesu ya koyar da mutane da yawa, da warkar da marasa lafiya da kuma ta da mutanen da suka mutu. Kowace rana a taron, za a kalli sashe ɗaya na bidiyon nan mai daɗi da kuma ban ƙarfafa.
Ka shiga dandalin jw.org/ha don ka ga duka tsarin ayyuka ka kuma kalli bidiyoyin nan:
Kalli wannan bidiyon don ka ga abin da ake yi a taron yanki na Shaidun Jehobah.
Ka ga abin da za mu koya a taron yanki na shekarar nan.
Ta yaya Yesu ya yi amfani da baiwa da yake da shi don ya taimaka wa mutane?
Ka kalli wasu sashe na bidiyon da aka kalla a taron yankin da suka gabata.

