Me Ya Sa Shaidun Jehobah Ba Sa Shiga Harkokin Siyasa?
Abin da Shaidun Jehobah suka koya daga Littafi Mai Tsarki ne ya sa ba sa shiga harkokin siyasa. Ba ma yin kamfen, ba ma yin zabe, ba ma goyon bayan wata jam’iyya, kuma ba ma yin takara. Kari ga haka, ba ma saka hannu a duk wani abin da ya shafi sauyin gwamnati. Mun yi imani cewa Littafi Mai Tsarki ya goyi bayan abin da muke yi.
Muna bin abin da Yesu ya yi ne sa’ad da yake duniya. Yesu ya ki karban mukami a gwamnati. (Yohanna 6:15) Ya koya wa mabiyansa yadda ba za su zama “na duniya ba,” kuma ya bayyana musu sarai cewa kar su saka baki a harkokin siyasa.—Yohanna 17:14, 16; 18:36; Markus 12:13-17.
Muna goyon bayan Mulkin Allah ne, wanda Yesu ya yi magana a kai sa’ad da ya ce: “Za a ba da wannan labari mai dadi na mulkin sama domin shaida ga dukan al’umma.” (Matiyu 24:14) Da yake mu wakilan Mulkin Allah ne, an ba mu aikin yin shelar zuwansa. Saboda haka, ba ma shiga harkokin siyasa a dukan kasashe, har da wanda muke zama a ciki.—2 Korintiyawa 5:20; Afisawa 6:20.
Muna iya gaya wa mutanen da suke goyon bayan jam’iyyu dabam-dabam abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da Mulkin Allah, domin ba ma saka baki a harkokin siyasa. A kullum muna nuna ta furucinmu da ayyukanmu cewa Mulkin Allah ne muke jira ya magance matsalolin ’yan Adam.—Zabura 56:11.
Da yake ba ma siyasa, ba abin da yake raba kanmu a fadin duniya. (Kolosiyawa 3:14; 1 Bitrus 2:17) Akasin haka, addinai da suke shiga harkokin siyasa suna raba kan mabiyansu.—1 Korintiyawa 1:10.
Muna girmama gwamnati. Ko da yake ba ma goyon bayan wani bangaren siyasa, muna girmama hukumomin da suke mulki a inda muke. Hakan ya jitu da abin da Littafi Mai Tsarki ya fada cewa: “Dole ne kowa ya yi biyayya ga shugabannin gwamnati.” (Romawa 13:1) Muna bin doka, muna biyan haraji, kuma muna ba gwamnati goyon baya a kokarin da take yi wajen taimaka wa talakawanta. Maimakon mu yi wani abin da zai kawo juyin mulki, muna bin umurnin da Littafi Mai Tsarki ya bayar cewa mu yi addu’a a madadin “sarakuna da dukan wadanda suke da manyan matsayi,” musamman idan suna so su tsai da shawarar da za ta shafi ’yancin yin ibada.—1 Timoti 2:1, 2.
Muna daraja ra’ayin mutane game da siyasa kuma ba ma cusa wa kowa ra’ayinmu. Alal misali, ba ma zuwa wurin zabe mu hana mutane jefa kuri’a ko mu jawo tashin hankali a wurin.
Kin shiga harkokin siyasa sabon yayi ne? A’a. Manzanni da Kiristoci a karni na farko ma ba su shiga harkokin siyasa ba. Littafin nan Beyond Good Intentions ya ce: “Ko da yake sun yi imani cewa ya kamata su girmama shugabannin gwamnati, Kiristoci a karni na farko ba su yarda da shiga harkokin siyasa ba.” Haka ma littafin nan On the Road to Civilization ya yi magana game da Kiristoci na farko cewa sun “ki su karbi mukami a gwamnati.”
Kin shiga harkokin siyasa da muke yi zai iya jawo matsalar tsaro? A’a. Mu ’yan kasa masu son zaman lafiya ne, don haka gwamnati ba ta bukatar ta ji tsoron mu. Alal misali, a wani rahoto da National Academy of Sciences of Ukraine ta bayar a shekara ta 2001, an yi magana a kan yadda muke kin shiga harkokin siyasa. Rahoton ya ce: “A yau, wasu za su iya tsanan zabin nan da Shaidun Jehobah suka yi; abin da ya sa suka sha wulakanci a hannun gwamnatin kama-karya na Nazi da kuma gwamnatocin Kwaminisanci na dā ke nan.” Amma har a lokacin da suka sha wulakanci a tarayyar Soviet, Shaidun Jehobah “sun ci gaba da bin dokar kasarsu. Sun yi aiki tukuru da zuciya daya a gonaki da kamfanoni, kuma ba su tayar wa gwamnatin Kwaminisanci da ke mulki a lokacin ba.” Haka ma a yau abubuwan da Shaidun Jehobah suka yi imani da shi da kuma ayyukansu, kamar yadda karshen rahoton ya nuna, ba sa “jawo tashin hankali, kuma ba sa zuga mutane su yi wa gwamnati tawaye.”