Shaidu Za Su Ƙaura da Hedkwatarsu
A Yuli na 2009, Shaidun Jehobah sun saye wani fili a ƙauyen New York da shirin ƙaura da hedkwatarsu. Girman filin ya kai eka 102 kuma yana da nisan kilomita 80 (wato mil 50) daga arewa maso yamma da na dā da ke Brooklyn, New York, inda suke tun 1909.
Shaidu 800 ne za su zauna kuma su yi aiki a sabon wurin da ya ƙunshi gine-ginen ofisoshi, wajen hidimomi, gidajen kwanciya. Za a kuma gina wani ƙaramin ma’adanar kayayyakin tarihi da ke ɗauke da tarihin Shaidun Jehobah.
Inda za a yi ginin zai ci eka 18 na filin da aka saya, an bar sauran wuraren da suke da itatuwa da fadama kewaye da filin. Ba za a taɓa wuraren da ke da ciyayi da itatuwa da dama ba.
Waɗanda suke zana ginin sun shirya yadda ginin ba zai ci lokaci da kuma kayan aiki ba, da zai taimaka a adana mahallin da ba za a kashe kuɗaɗe da yawa ba. Alal misali, za a yi rufin da ciyawa ne da ba za a kashe kuɗaɗe masu yawa ba kuma zai iya tare ruwan sama kuma ɗakunan za yi sanyi. An shirya ginin ofishin ta fuskar haske don a sami haske a ciki. Abin muhimmanci ne a rage ɓata ruwa.
Me ya sa aka shirya irin ginin nan? Ofisoshin reshe na Shaidun Jehobah a wasu ɓangarorin duniya yanzu suna buga Littafi Mai Tsarki da littattafan da ke bayanin Littafi Mai Tsarki da a dā a Brooklyn kaɗai ake bugawa. A shekarar 2004, an ƙaura da aikin buga littattafai da kuma tura littattafai daga Amirka zuwa Wallkill, New York, misalin kilomita 145 (wato mil 90) a arewa maso yamma na Brooklyn.
An kuma yi la’akari da zancen kuɗi. Yin aiki a Brooklyn da kuma adanawa yana cin kuɗi. Idan suka ƙaura zuwa sabon ginin, Shaidu za su iya amfani sosai da kuɗaɗe don su tallafa wa aikin ilimantarwa na Littafi Mai Tsarki.
Ana bukatar bincika yadda aikin zai shafi mahalli kafin a ba da izinin fara aikin. Idan kome ya yi daidai, za a soma ginin a shekara ta 2013 kuma za a gama shi cikin shekara huɗu.
Ban da wajen buga littattafai a Wallkill, New York, Shaidun Jehobah suna da wajen ilimantarwa a Patterson, New York. Ƙungiyar tana da ofisoshin reshe a ƙasashe da yawa. A duk duniya, Shaidun sun ɗara miliyan bakwai da rabi.