WAƘA TA 70
Ku Nemi Masu Zuciyar Kirki
(Matta 10:11-15)
-
1. Yesu Kristi ya koya mana yadda
Za mu riƙa yin wa’azi:
‘Sai ku nemi masu zuciyar kirki
Da ke so su bauta wa Allah.
In kun je gidajensu, ku gaishe su
Kuma ku ba su salamarku.
Idan mutanen sun ƙi saurarawa,
Ku bar gidan da salamarku.’
-
2. Ku yi wa’azi ga dukan mutane,
Waɗanda ke son gaskiya.
Za su bauta wa Allah tare da ku
Domin su rayu har abada.
Kar ku damu da abin da za ku ce
Don Jehobah zai taimake ku.
Idan kuna fara’a ga mutane
Za ku ratsa zuciyarsu fa.
(Ka kuma duba A. M. 13:48; 16:14; Kol. 4:6.)