WAƘA TA 62
Sabuwar Waka
(Zabura 98)
-
1. Mu rera yabo ga Allahn sama mai ƙauna.
Shela ayyukansa da waɗanda zai yi,
Yabi ikonsa, shi Allah ne Maɗaukaki.
Yana yin adalci,
A duk hukuncinsa.
(AMSHI)
Mu rera
Sabuwar waƙar nan!
Jehobah
Ya zama Sarkinmu.
-
2. Mu ɗaga murya, mu yabi Allah Sarkinmu!
Ɗaukaka sunansa da kuma ikonsa.
Mu rera yabo da dukan zuciyarmu fa.
Mu busa ƙahoni,
Mu yabi Jehobah.
(AMSHI)
Mu rera
Sabuwar waƙar nan!
Jehobah
Ya zama Sarkinmu.
-
3. Dukan halittu da ke teku su yi yabo.
Halittun duniya, su rera waƙa ma.
Ƙasa da rafi, duk za su rera ma yabo.
Duwatsu da tuddai,
Su ɗaga muryoyi.
(AMSHI)
Mu rera
Sabuwar waƙar nan!
Jehobah
Ya zama Sarkinmu.
(Ka kuma duba Zab. 96:1; 149:1; Isha. 42:10.)