WAƘA TA 21
Mu Ci Gaba da Sa Mulkin Allah Farko
(Matta 6:33)
-
1. Abin da Jehobah ke so
Da ke faranta ransa,
Mulkinsa da Ya kafa ne
Don ya cika nufinsa.
(AMSHI)
Mu biɗi Mulkin da farko
Da kuma adalcinsa.
Shaida sunansa ga kowa,
Mu bi duk umurninsa.
-
2. Kada mu riƙa damuwa
Don biyan bukatunmu.
Allah zai albarkace mu
In mun biɗi Mulkinsa.
(AMSHI)
Mu biɗi Mulkin da farko
Da kuma adalcinsa.
Shaida sunansa ga kowa,
Mu bi duk umurninsa.
-
3. Mu yaɗa bisharar Mulkin,
Mu koya wa mutane
Cewa Allahnmu kaɗai ne
Zai cire wahalarsu.
(AMSHI)
Mu biɗi Mulkin da farko
Da kuma adalcinsa.
Shaida sunansa ga kowa,
Mu bi duk umurninsa.
(Ka kuma duba Zab. 27:14; Mat. 6:34; 10:11, 13; 1 Bit. 1:21.)