WAƘA TA 17
“Na Yarda”
(Luka 5:13)
-
1. Da Kristi yake duniya,
Ya tausaya wa mutane.
Bukatun mutane
Ya biya musu;
Ya ciyar da mayunwata.
Ya warkar da naƙasassu,
Guragu har da makafi.
Kamar yadda zai yi a Mulkinsa,
Da ƙauna ya ce: “Na yarda.”
-
2. Muna yin koyi da Kristi
A rayuwarmu koyaushe.
Muna nuna ƙauna
Ga maƙwabtanmu,
Don su san Jehobah sosai.
Muna taimakon waɗanda
Suke cikin matsaloli.
In mabukata suka roƙe ka,
Da murna ka ce: “Na yarda.”
(Ka kuma duba Yoh. 18:37; Afis. 3:19; Filib. 2:7.)