Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 159

Mu Daukaka Jehobah

Mu Daukaka Jehobah

(Zabura 96:8)

  1. 1. Madaukakinmu Jehobah,

    Kana da girma sosai!

    Kai ne Mahaliccin sama,

    Duniya da dukan abu.

    Saꞌad da na kalli sama,

    Ina ganin ikonka.

    A gaskiya, ban cancanci,

    Ka kaunace ni haka ba.

    (AMSHI)

    Jehobah, ina rera ma yabo,

    Domin ka cancanta fa.

    Kai Allah ne, da Sarkin Zamanai.

    Ina daga muryata;

    Ka cancanci daukaka.

  2. 2. Na mika raina, Jehobah.

    Na kudurta niyyar yin

    Shelar kauna da girmanka,

    Har da kuma daukakarka.

    Bauta wa Allah, Jehobah,

    Yana sa ni murna fa.

    Kai ne mai taimaka mini

    Yau, gobe, da har abada.

    (AMSHI)

    Jehobah, ina rera ma yabo,

    Domin ka cancanta fa.

    Kai Allah ne, da Sarkin Zamanai.

    Ina daga muryata;

    Ka cancanci daukaka.

  3. 3. Kwari, teku, har da tuddai,

    Iska, da duk tsuntsaye,

    Sun sa mun ga darajarka,

    Da kuma kaunarka sosai.

    Ina mamaki Jehobah,

    Don yawan daukakarka.

    Dole in yabe ka, Uba,

    Kai ne ka halicce su duk!

    (AMSHI)

    Jehobah, ina rera ma yabo,

    Domin ka cancanta fa.

    Kai Allah ne, da Sarkin Zamanai.

    Ina daga muryata;

    Ka cancanci daukaka.

(Ka kuma duba Zab. 96:​1-10; 148:​3, 7.)