WAƘA TA 129
Za Mu Rika Jimrewa
(Matta 24:13)
-
1. Me zai taimaka
Mu jimre da matsaloli?
Yesu ya jimre,
Ya kafa mana misali.
Jehobah, Allah ne
Ya taimaka masa.
(AMSHI)
Sai mu riƙa jimrewa,
Mu riƙe aminci.
Jehobah na ƙaunar mu,
Za mu riƙa jimrewa har ƙarshe.
-
2. Duniyar Shaiɗan
Tana baƙanta zucinmu,
Amma nan gaba
Za mu ji daɗin aljanna.
Zama a cikinta
Ne muke ɗokin yi.
(AMSHI)
Sai mu riƙa jimrewa,
Mu riƙe aminci.
Jehobah na ƙaunar mu,
Za mu riƙa jimrewa har ƙarshe.
-
3. Shakka ko tsoro
Ba zai sa mu bar Allah ba.
Za mu ci gaba
Har sai ranar Allah ta zo.
Mu riƙa jimrewa
Domin ƙarshe ya zo.
(AMSHI)
Sai mu riƙa jimrewa,
Mu riƙe aminci.
Jehobah na ƙaunar mu,
Za mu riƙa jimrewa har ƙarshe.
(Ka kuma duba A. M. 20:19, 20; Yaƙ. 1:12; 1 Bit. 4:12-14.)