WAƘA TA 128
Ka Jimre Har Karshe
(Matta 24:13)
-
1. Duk alkawuran Allahnmu
Suna ƙarfafamu.
Abubuwan da mun koya
Dukansu gaskiya ne.
Ka zama mai bangaskiya,
Mai son yin nufin Allah
Da kuma wa’azi kullum
Domin ka yi nasara.
-
2. Kada ka manta da Allah
Don zai taimake ka,
Kuma ka riƙa jimrewa,
Da kowace wahala.
Ko kana cikin damuwa,
Kada ka ji tsoro sam.
Jehobah na tare da kai
Domin ya taimake ka.
-
3. Waɗanda suka jimre ne
Za su sami ceto.
Za su rayu har abada
Domin sun yi biyayya.
Bari mu jimre har ƙarshe
Ko muna shan wahala.
Allah zai albarkace mu
Da rai na har abada.
(Ka kuma duba Ibran. 6:19; Yaƙ. 1:4; 2 Bit. 3:12; R. Yoh. 2:4.)