WAƘA TA 107
Mu Yi Koyi da Allah a Nuna Kauna
(1 Yohanna 4:19)
-
1. Jehobah Allah ya kafa misali
Na ƙauna, na ƙauna.
Ya nuna ƙauna ga dukan ’yan Adam,
Mu ƙaunaci mutane ma.
Jehobah Uba, ya aiko da Yesu
Don ya gafarta laifofin ’yan Adam.
Babu mai ƙauna irin ta Jehobah,
Jehobah mai ƙauna ne sosai.
-
2. In mun bi misalin Allah Jehobah
Yadda ya yi ƙauna.
Za mu ƙaunaci dukan ’yan’uwanmu,
Ba ƙiyayya, ba bambanci.
Kar mu ce muna ƙaunar Maɗaukaki,
Amma mu ƙi bin dokar da ya ba mu.
Mu so ’yan’uwa duk da kasawarsu,
Mu yi ƙauna da duk zuciya.
-
3. Ƙauna tana sa mu zama tsintsiya
Mai maɗauri ɗaya.
Shi ya sa Jehobah ke gayyatar mu:
“Mu kasance da haɗin kai.”
Mu zauna tare, mu more salama,
Kalmarsa da ruhunsa na da iko.
Suna sa mu ƙaunaci ʼyan’uwanmu
Domin Jehobah na da ƙauna.
(Ka kuma duba Rom. 12:10; Afis. 4:3; 2 Bit. 1:7.)