WAƘA TA 101
Mu Rika Hidima da Hadin Kai
(Afisawa 4:3)
-
1. Mugunta da rashin ƙauna
Na shafan ’yan Adam sosai,
Amma Allah ya kawo mu
Cikin ƙungiyarsa.
Muna da haɗin kai
Da kuma ƙauna.
Mu yi wa’azi da ƙwazo,
Yesu shi ne shugabanmu.
Mu riƙa bin dokokinsa,
Muna aiki tare.
-
2. Mu roƙi Jehobah Allah
Don ya sa mu nuna ƙauna,
Da jinƙai da alheri ma
Ga dukan ’yan’uwa.
Zama da lumana
Na da kyau sosai.
In dukanmu na da ƙauna,
Allah zai taimaka mana.
Za mu zauna da haɗin kai
Don mu bauta masa.
(Ka kuma duba Mi. 2:12; Zaf. 3:9; 1 Kor. 1:10.)