Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

YADDA AKE AMFANI DA GUDUMMAWARKA

Fassara Jawaban Taron Yanki na 2020 Mai Jigo, Ku Riƙa Farin Ciki!

Fassara Jawaban Taron Yanki na 2020 Mai Jigo, Ku Riƙa Farin Ciki!

10 GA YULI, 2020

 ’Yan’uwa a duk fadin duniya za su kalli taron yanki a lokaci daya a watan Yuli da Agusta 2020. Wannan shi ne karo na farko da aka taba yin hakan. An bukaci a fassara jawaban taron da aka dauka a bidiyo zuwa yaruka fiye da 500. Irin wannan aikin yakan dauki shekara daya ko fiye da hakan. Amma domin barkewar annobar koronabairas, an ba mafassaran da suka yi aiki a kan Taron Yanki na 2020 Mai Jigo, Ku Riƙa Farin Ciki! kasa da wata hudu su fassara taron.

 Sashen da Ke Taimakon Mafassara da Sashen da Ke Yin Sayayya a Fadin Duniya da suke Hedkwatar Shaidun Jehobah ma sun taimaka a yi wannan gagarumin aiki. Sashen da Ke Taimakon Mafassara ya ga cewa mafassara da dama suna bukatar karin ingantattun makarufo da wasu abubuwa don aikin. Sashen da Ke Yin Sayayya a Fadin Duniya kuma ya shirya yadda za a sayi makarufo guda 1,000 kuma a kai wurare kusan 200.

 Don a samu a sayi makarufo din da sauki, an saye su da yawa kuma aka tura su wuri daya, daga nan aka tura wa mafassara a wurare dabam-dabam a duniya. Yadda aka sayi makarufo din da yawa ya sa kudin saya da aika makarufo guda daya ya kama wajen dala 170 (wajen naira 65,875). Da a ce daya-daya aka saye su, da kudin ya fi hakan sosai.

 Watan Afrilu da Mayu na 2020 ne Sashen da Ke Yin Sayayya a Fadin Duniya suke da shi don su sayi makarufo din kuma su aika wurare dabam-dabam. Ga shi kuma a lokacin harkokin kasuwanci sun yi wuya domin annobar koronabairas. Duk da haka, kafin karshen watan Mayu, an samu an tura makarufo zuwa yawancin ofisoshin fassara da ofisoshinmu a fadin duniya da kuma sauran wuraren da ake fassara da suke bukatar makarufo.

 Jay Swinney, wanda yake kula da Sashen da Ke Yin Sayayya a Fadin Duniya ya ce: “An sami hadin kai sosai tsakanin sassa dabam-dabam a Bethel da ’yan kasuwa da aka yi hulda da su a wannan lokacin.” Ya kuma ce: “Ruhun Jehobah ne ya taimaka mana mu yi wannan aikin da wuri, kuma mu yi amfani da gudummawa da ake bayarwa yadda ya dace don mu taimaka wa ’yan’uwanmu.”

 Nicholas Ahladis, wanda yake aiki da Sashen da Ke Taimakon Mafassara, ya ce: “A lokacin mafassaran suna zaman kulle, amma samun kayan aikin nan ya karfafa su sosai. Duk da cewa mafassaran suna kulle, sun iya sun yi aiki da abokan aikinsu, kuma sun fassara jawaban da wasannin kwaikwayon da wakokin a harsuna fiye da 500.”

 Wannan daya ne cikin ayyuka da dama da aka yi wajen shirya Taron Yanki na 2020 Mai Jigo, Ku Riƙa Farin Ciki! don ’yan’uwa a fadin duniya su amfana. Gudummawa da kuka yi ta donate.jw.org da kuma wasu hanyoyi ne suka sa aka samu aka sayi wadannan abubuwan da ake bukata.