Privacy Settings

To provide you with the best possible experience, we use cookies and similar technologies. Some cookies are necessary to make our website work and cannot be refused. You can accept or decline the use of additional cookies, which we use only to improve your experience. None of this data will ever be sold or used for marketing. To learn more, read the Global Policy on Use of Cookies and Similar Technologies. You can customize your settings at any time by going to Privacy Settings.

Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Masana Sun Gano Cewa Sarki Dauda Ya Taba Wanzuwa

Masana Sun Gano Cewa Sarki Dauda Ya Taba Wanzuwa

 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Sarki Dauda na Isra’ila ya yi rayuwa a karni na 11 kafin haihuwar Yesu, kuma zuriyarsa sun yi sarauta na daruruwan shekaru. Amma wasu mutane sun yi shakkar wannan. Sun ce labarin Sarki Dauda kage ne kawai. Amma, Sarki Dauda ya wanzu kuwa da gaske?

Wani gutsuren dutse da aka samo a Tel Dan, a arewacin Isra’ila da ke dauke da rubutun nan “Zuriyar Dauda”

 A shekara ta 1993, wani masani mai suna Avraham Biran tare da abokan aikinsa sun gano wani gutsuren dutse mai dauke da rubutun nan “Zuriyar Dauda” a Tel Dan, a arewacin Isra’ila. An yi rubutun da tsohon yaren Semitic na karni na 9 kafin zamaninmu. Babu shakka, dutsen gutsuren mutum-mutumi ne da mutanen Aramiya suka gina don su rika tunawa da yakin da suka ci a kan Isra’ilawa.

 Wani talifi a Bible History Daily ya ce: Akwai mutanen da suka yi shakkar rubutun nan ‘Zuriyar Dauda’ . . . Amma yawancin masanan Littafi Mai Tsarki da kuma masu tona kasa sun amince cewa rubutun da ke gutsuren dutsen ya tanadar da cewa Sarki Dauda wanda labarinsa ke cikin Baibul ya wanzu da gaske. Wannan yana cikin labari mafi muhimmanci da masana suka rahoto a BAR [Biblical Archaeology Review].”