Za A Taba Samun Adalci a Dukan Duniya Kuwa?
Da alama cewa babu inda ba a rashin adalci a duniyar nan. Ga misalai biyu na mutanen da aka kulle su a kurkuku sakamakon rashin adalci:
A Janairu 2018, wata alkaliya a Amirka ta sa an saki wani mutum da aka kulle shi kusan shekaru 38. Gwaje-gwajen matattarin sanin asalin halitta, wato DNA, ne ya tabbatar cewa mutumin bai aikata laifin da ake zarginsa da shi ba.
A watan Satumba 1994, an kulle wasu matasa uku a wata kasa a Afirka domin sun ki su shiga soja saboda imaninsu. A watan Satumba 2020, mutanen nan sun cika shekara 26 a kurkuku, kuma ba a shigar da kara a kansu ko a kai su kotu ba.
Idan an taba yi maka rashin adalci, watakila ka ji kamar Ayuba, wani mutumin da aka ambata a Littafi Mai Tsarki. Ayuba ya ce: “Na yi kiran neman shari’ar gaskiya, amma ban samu ba.” (Ayuba 19:7) Ko da yake ana ganin ba zai yiwu a ce an daina yin rashin adalci ba, Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa lokaci na zuwa da za a yi wa kowa adalci. Kari ga haka, Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka idan ana maka rashin adalci.
Me ke jawo rashin adalci?
Rashin bin ka’idodin Allah ne yake jawo rashin adalci. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah ne tushen adalci. (Ishaya 51:4) A Littafi Mai Tsarki, kalmomin nan “adalci” da “gaskiya” suna da alaka da juna sosai. (Zabura 33:5) Za a yi adalci idan ana yin abubuwa cikin gaskiya, wato bisa ga abin da ya dace a gaban Allah. Akasin haka, yin zunubi, wato, taka ka’idodin Allah yana jawo rashin adalci. Ga wasu misalai:
Son kai. Mugun sha’awa ce takan kai mutum ga yin zunubi. (Yakub 1:14, 15) Don su sami abin da suke so, mutane da yawa sukan cutar da wasu. Akasin haka, Allah yana so mu yi kokarin kyautata wa mutane ba kanmu ba.—1 Korintiyawa 10:24.
Rashin sani. A wasu lokuta mutane sukan yi abin da zai cutar da wasu cikin rashin sani, duk da cewa ba su sani ba, hakan zunubi ne a gaban Allah. (Romawa 10:3) Rashin sani ne ya sa aka kashe Yesu, kuma ba a taba yin rashin adalci irin wannan ba.—Ayyukan Manzanni 3:15, 17.
Kasawar ’yan Adam. Masu siyasa da ’yan kasuwa da shugabannin addini suna da’awa cewa suna yin adalci. Amma a gaskiya, su ne tushen kurakurai da rashawa da nuna bambanci da hadama da kuma tsattsauran ra’ayi. Kuma dukan wadannan abubuwan sukan jawo rashin adalci. Ko da yake wasu shugabannin suna da nufi mai kyau, amma da yake sun ki bin ja-gorancin Allah, ba za su iya yin nasara ba.—Mai-Wa’azi 8:9; Irmiya 10:23.
Allah ya damu da rashin adalci da muke gani kuwa?
E, ya tsani rashin gaskiya da duk wani abin da yake sa a yi rashin adalci. (Karin Magana 6:16-18) Allah ya sa annabi Ishaya ya rubuta cewa: “Gama ni Yahweh a ina kaunar yin gaskiya, ba na son sata da rashin gaskiya.”—Ishaya 61:8.
Dokar da Allah ya ba wa Isra’ilawa a dā ta nuna cewa yana so su rika yin adalci. Ya gaya wa alkalansu cewa su guji cin hanci da kuma abubuwan da za su sa su yin rashin adalci. (Maimaitawar Shari’a 16:18-20) Ya nuna cewa bai ji dadin yadda Isra’ilawa suka wulakanta talakawa marasa karfi ba kuma ya ki amincewa da ibadarsu don sun taka dokokinsa.—Ishaya 10:1-3.
Shin Allah zai kawo karshen rashin adalci?
E. Ta wurin Yesu Kristi, Allah zai cire zunubi wanda shi ne tushen rashin adalci kuma ya sa ’yan Adam su zama kamiltattu. (Yohanna 1:29; Romawa 6:23) Allah ya kuma kafa wani mulki wanda zai mai da duniya ta zama sabuwa kuma ya sa a rika yi wa kowa adalci. (Ishaya 32:1; 2 Bitrus 3:13) Domin ka sami karin bayani game da mulkin Allah, ka kalli bidiyon nan Mene ne Mulkin Allah?
Yaya rayuwa za ta kasance a sabuwar duniya?
Idan ana yin adalci a ko’ina a duniya, mutane za su sami salama da kwanciyar hankali. (Ishaya 32:16-18) Allah yana daukan dukan ’yan Adam da muhimmanci, don haka zai sa a rika yi wa kowa adalci. Mutane ba za su sake bakin ciki ko kuka domin rashin adalci ba, da sannu a hankali za mu manta da duk wata wahalar da aka taba sha don rashin adalci. (Ishaya 65:17; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:3, 4) Don karin bayani, ka karanta talifin nan “Mene ne Mulkin Allah Zai Yi?”
Shin da gaske Allah zai cire rashin adalci a duniya?
Kwarai kuwa. A kullum, annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suna cika kuma Littafi Mai Tsarki yana fadin gaskiya game da tarihi da kuma kimiyya. Ban da haka ma, babu sabani a cikinsa. Saboda haka, za ka iya amincewa da duk alkawuran da ke cikinsa. Bidiyoyi da talifofi na gaba sun ba da karin bayani:
Ta Yaya Za Mu San Cewa Abin da ke Littafi Mai Tsarki Gaskiya Ne? (bidiyo)
“Bari Annabcin Littafi Mai Tsarki Su Ƙarfafa Ku” (bidiyo)
“Reasons to Trust the Bible”
Shin za mu iya yakan rashin adalci yanzu?
Mutanen kirki a zamanin dā sun yi iya kokarinsu don kar a musu rashin adalci. Alal misali, an so a yi ma manzo Bulus rashin adalci da zai iya sa a kashe shi. Maimakon ya amince da rashin adalcin, manzo Bulus ya daukaka kara zuwa wurin Kaisar.—Ayyukan Manzanni 25:8-12.
Amma gaskiyar ita ce, duk kokarce-kokarcen ’yan Adam don su kawo karshen rashin adalci ba zai yi nasara ba. (Mai-Wa’azi 1:15) Mutane da yawa sun gano cewa yin imani cewa Allah zai kawo sabuwar duniya yana taimaka musu su kasance da kwanciyar hankali duk da rashin adalci da ake musu.
a Yahweh ko kuma Jehobah shi ne sunan Allah.—Zabura 83:18.