Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KU ZAUNA A SHIRYE!

Abin da Ya Faru da Shaidun Jehobah a Holocaust​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Abin da Ya Faru da Shaidun Jehobah a Holocaust​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

 A ranar 27 ga Janairu 2023, mutane da yawa za su yi Bikin Tunawa da Holocaust ta Duniya (International Holocaust Remembrance Day). Munanan abubuwan da suka faru fiye da shekaru 75 da suka shige za su iya sa ka yi mamakin dalilin da ya sa Allah ya kyale kisan kiyashin da ya faru.

 A lokacin da aka yi kisan kiyashi na Holocaust, Yahudawa sun sha wahala ba kadan ba. An kakkashe miliyoyin Yahudawa da kuma wasu mutane. Shaidun Jehobah da aka tsananta musu don imaninsu suna cikin wadanda aka kashe.

Bege da rayuwa a nan gaba

 Mutane da yawa suna tsoron cewa za a sake yin irin wannan kisan kiyashi. Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa a nan gaba, ba za a sake hakan ba.

  •   “‘Na san irin shirin da nake da shi domin ku,’ in ji Jehobah, ‘shiri ne na salama, ba na masifa ba, domin in ba ku bege da rayuwa mai maꞌana a nan gaba.’”​—Irmiya 29:​11, New World Translation.  a

 Jehobah zai cika wadannan alkawaran saꞌad da ya kawar da mugunta da dukan matsaloli da ta jawo. Nan ba da dadewa ba zai:

  •   Kawar da mugaye masu yi wa mutane mugunta.​—Karin Magana 2:22.

  •   Taimaka wa wadanda suka sha wahala.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4.

  •   Dawo da wadanda suka mutu zuwa rayuwa a duniya.​—Yohanna 5:​28, 29.

 Za ka iya amince da alkawuran da ke Littafi Mai Tsarki. Don ka san abin da ya sa zai dace ka yi hakan, za mu so mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai kyauta.

a Yahweh ko kuma Jehobah ne sunan Allah.​—Zabura 83:18.