KU ZAUNA A SHIRYE!
Mummunar Girgizar Kasa Ta Auku a Kasar Turkiya da Suriya—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
A ranar Litinin 6 ga Fabrairu, 2023, mummunar girgizar kasa ta auku a kasar Turkiya da Suriya.
A labaran Reuters a ranar 6 ga Fabrairu an ce: “Wata mummunar girgizar kasar ta kashe mutane fiye da 3,700 a wani yanki na Turkiya da arewa maso yammancin Suriya a ranar Litinin. Da yake ana sanyi sosai a wurin, hakan ya sa abin ya dada muni domin girgizar kasar ta shafi dubban mutane. Kari ga haka, sanyin ya sa ya kasance da wuya a ceto wadanda suke karkashin baraguzan gine-gine.”
Irin wadannan labaran suna sa mu bakin ciki sosai. A irin wannan lokacin, za mu dogara ga Jehobah “Allah wanda yake yi mana kowace irin taꞌaziyya!” (2 Korintiyawa 1:3) Allah yana taimaka mana ta wurin “taꞌaziyar littattafai mu zama da bege.”—Romawa 15:4, Littafi Mai Tsarki.
A cikin Littafi Mai Tsarki, mun koyi:
Abin da aka fada game da girgizar kasa.
Wurin da za mu iya samun taꞌaziyya da bege.
Yadda Allah zai kawo karshen dukan matsaloli.
Don samun karin bayani a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da wadannan batutuwan, karanta talifofin nan:
a Yahweh ko kuma Jehobah ne sunan Allah.—Zabura 83:18.