ABIN DA KE SHAFIN FARKO | SHIN YIN ADDU’A ƁATA LOKACI NE?
Akwai Mai Jin Addu’a Kuwa?
Wasu suna ji kamar yin addu’a ɓata lokaci ne don ba mai sauraron su. Wasu kuma sun gwada yin addu’a amma sun ga kamar ba wanda ya amsa musu. Wani mutum da bai gaskata da wanzuwar Allah ba ya yi wannan tunani game da Allah sai ya yi addu’a, ya ce: “Allah ka ɗan yi mini magana.” Ya ce sai Allah ya yi “tsit.”
Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa akwai Allah kuma yana jin addu’a. Allah Maɗaukaki shi ne mai jin addu’o’inmu. Littafi Mai Tsarki ya yi wannan furucin shekaru da yawa da suka wuce: “Lallai [Allah] za ya yi maka rahama yayin da ya ji muryar kukanka; sa’ad da ya ji kuwa za ya amsa maka.” (Ishaya 30:19) Wata aya kuma ta ce: “Ubangiji yana murna sa’ad da adilai suke yin addu’a.”—Misalai 15:8, Littafi Mai Tsarki.
Yesu ya yi addu’a ga Ubansa, kuma ya “amsa masa.”—Ibraniyawa 5:7
Littafi Mai Tsarki ya kuma ba da misalan mutanen da Allah ya amsa addu’o’insu. Wata aya ta ce Yesu ya yi “roƙe-roƙe . . . ga wanda yana da iko ya cece shi” kuma ya “amsa masa.” (Ibraniyawa 5:7) Za mu iya samun wasu misalai a littafin Daniyel 9:21 da 2 Labarbaru 7:1.
Me ya sa wasu suke gani kamar ba a amsa addu’o’insu? Idan muna so a amsa addu’o’inmu, ya kamata mu yi addu’a ga Allahn da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki, wato Jehobah, * ba allolin ƙarya ko kuma kakanninmu ba. Allah yana kuma so mu yi ‘roƙo daidai da nufinsa,’ wato abubuwan da yake so. Idan mun yi hakan, Allah ya ce babu shakka “yana jinmu.” (1 Yohanna 5:14) Saboda haka, idan muna so a amsa addu’o’inmu, muna bukatar mu san Jehobah da kuma nufinsa.
Mutane da yawa sun amince cewa addu’a ba ɗaya daga cikin abu da ake yi a wuraren ibada kaɗai ba ne, amma Allah yana ji da kuma amsa addu’o’i. Isaac daga ƙasar Kenya ya ce: “Na yi addu’a don in fahimci Littafi Mai Tsarki. Jim kaɗan bayan haka, sai wani ya zo wurina don ya taimaka mini.” A ƙasar Filifin, Hilda ta so ta daina shan taba. Ta yi ƙoƙari ta daina sau da yawa, amma ba ta yi nasara ba, sai maigidanta ya ce mata, “To ki yi addu’a, wataƙila Allah zai taimaka miki.” Ta bi shawararsa kuma ta ce: “Na yi mamaki sosai yadda Allah ya taimake ni. Nan da nan, sai na soma ƙyamar shan taba. Daga baya, na daina shan taba kwata-kwata.”
Shin Allah yana da niyyar taimaka maka idan bukatunka sun jitu da nufinsa?
^ sakin layi na 6 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah shi ne sunan Allah.