ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ZAI YIWU A SAKE RAYUWA—BAYAN MUTUWA?
Me Zai Iya Tabbatar Maka Cewa Matattu Za Su Sake Rayuwa?
Shin ɓata lokaci ne yin tunani cewa matattu za su sake rayuwa? Manzo Bulus bai kasance da wannan ra’ayin ba. Allah ya hure shi ya ce: “Da begenmu ga Almasihu domin wannan rai ne kaɗai, ai, da mun fi kowa zama abin tausayi. Amma ga hakika an ta da Almasihu daga matattu, shi ne ma nunan fari na waɗanda suka yi barci.” (1 Korintiyawa 15:19, 20, Littafi Mai Tsarki) Bulus yana da tabbaci sosai cewa za a ta da matattu. Tashin Yesu daga mutuwa ne ya ba da wannan tabbacin. * (Ayyukan Manzanni 17:31) Shi ya sa Bulus ya kira Yesu “nunan fari,” domin shi ne mutumi na farko da ya tashi daga mutuwa da ba zai sake mutuwa ba har abada. Idan Yesu ne na fari, to babu shakka, akwai wasu da za su biyo bayansa.
Ga wani dalili kuma da ya sa za mu iya gaskatawa da begen tashin matattu. Jehobah Allah yana faɗin gaskiya a koyaushe. “Allah . . . ba ya iya yin ƙarya.” (Titus 1:2) Jehobah bai taɓa yin ƙarya ba kuma ba zai taɓa yin hakan ba. Shin zai yiwu ya yi mana alkawarin tashin matattu, ya nuna cewa yana da ikon yin hakan, sa’an nan daga baya ya fasa cika alkawarinsa? Babu shakka, hakan ba zai yiwu ba!
Me ya sa Jehobah ya yi alkawari cewa zai ta da matattu? Domin yana ƙaunarmu. Ayuba ya yi wannan tambayar: ‘Idan mutum ya mutu za ya sake rayuwa? . . . Za ka yi kira, ni ma in amsa maka: Za ka yi marmarin aikin hannuwanka.’ (Ayuba 14:14, 15) Ayuba ya tabbata cewa Ubansa na sama zai yi marmarin tayar da shi. Shin Allah ya canja ne? Jehobah ya ce: “Ni Ubangiji ba mai-sākewa ba ne.” (Malakai 3:6) Har ila, Allah yana ɗokin tayar da waɗanda suka mutu kuma su kasance da ƙoshin lafiya da farin ciki. Abin da mahaifi mai ƙauna zai so ya faru ke nan bayan ɗansa da ya mutu. Bambancin shi ne Allah yana da ikon yin abin da ya nufa.
Mutuwa maƙiyiya ce, amma Allah zai kawar da ita
Jehobah zai ba Ɗansa iko ya sa masu makoki su yi matuƙar farin ciki. Mene ne ra’ayin Yesu game da tashin matattu? Yesu ya yi “kuka” kafin ya tayar da Li’azaru don ya ga irin baƙin ciki da ’yan’uwansa da kuma abokansa suka yi. (Yohanna 11:35) A wani lokaci kuma, Yesu ya ga wata gwauruwa a ƙauyen Nayin da ɗanta tilo ya mutu. Yesu “ya ji tausayinta, ya kuma ce mata, ‘Daina kuka.’” Nan da nan sai ya tayar da ɗanta. (Luka 7:13, LMT) Saboda haka, Yesu ba ya jin daɗin ganin mutane suna makoki da kuma mutuwa. Zai yi murna sosai sa’ad da ya sa dukan mutanen da ke makoki a duniya baki ɗaya farin ciki!
An taɓa maka rasuwa kuwa? Za ka iya ɗauka cewa ba za a iya kawar da mutuwa ba. Amma hakan ba gaskiya ba ne, Allah zai yi amfani da Ɗansa don ya tayar da mutanen da suka rasu. Ka tuna cewa Allah yana so ka shaida lokacin da za a ta da matattu. Yana so ka kasance a wurin don ka marabci ’yan’uwanka da za a tayar daga mutuwa. Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance sa’ad da mutuwa ta zama tsohon labari!
Lionel da aka ambata ɗazun ya ce: “Daga baya sai na koya cewa za a yi tashin matattu. Da farko, ban gaskata da hakan ba domin na yi shakkar mutumin da ya gaya mini. Amma da na bincika Littafi Mai Tsarki sai na ga cewa hakan gaskiya ne! Ina ɗokin sake ganin kakana.”
Za ka so ka sami ƙarin bayani? Shaidun Jehobah za su yi farin cikin nuna maka a cikin naka Littafi Mai Tsarki cewa za a ta da matattu. *
^ sakin layi na 3 Don tabbaci cewa an ta da Yesu daga mutuwa, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Nuwamba, 2014, shafi na 6, sakin layi na 11-14.
^ sakin layi na 9 Ka duba babi na 7 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah suka wallafa.