Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Wane irin rayuwa ne ’yan Adam za su more a nan gaba?

Ta Yaya Mutuwar Yesu Za Ta Sa Dukan ’Yan Adam Su So Juna?

Babu shakka, ’yan kimiyya za su ci gaba da ƙirƙiro sababbin abubuwa. Amma shin za su iya sa dukan ’yan Adam su so juna? A’a. Son kai da kwaɗayi sun zama ruwan dare a yau. Amma, Allah yana shirya wa ’yan Adam abu mai kyau.—Karanta 2 Bitrus 3:13.

Kalmar Allah ta bayyana cewa a nan gaba, dukan ’yan Adam za su so juna. Mutane za su zauna cikin kwanciyar hankali, kuma babu wani bala’in da zai auko musu.—Karanta Mikah 4:3, 4.

Ta yaya za a kawar da son kai?

Adamu bai da halin son kai sa’ad da Allah ya halicce shi. Amma bayan ya karya dokar Allah, sai ya zama ajizi. Daga wurinsa ne muka gāji wannan halin. Amma Allah zai yi amfani da Yesu wajen sa ’yan Adam su zama kamiltattu.—Karanta Romawa 7:21, 24, 25.

Allah ya aiki Yesu zuwa duniya kuma Yesu ya mutu domin ya kawar da sakamakon zunubin da mutum na farko ya yi. (Romawa 5:19) Da haka, Yesu ya sa ’yan Adam su sami begen yin rayuwa mai ma’ana a nan gaba, inda ba za su yi son kai ba.—Karanta Zabura 37:9-11.