Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Yi Aiki don Kyautata Yanayin Salama da Muke Mora

Ka Yi Aiki don Kyautata Yanayin Salama da Muke Mora

“Wurin takawar ƙafafuwana kuma zan maishe shi mai-daraja.”—ISHA. 60:13.

WAƘOƘI: 102, 75

1, 2. Mene ne ‘matashin sawu’ yake nufi a cikin Littafi Mai Tsarki?

JEHOBAH ALLAH ya ce: “Sama kursiyina ce, duniya kuwa matashin sawuna ce,” kuma hakan ya dace. (Isha. 66:1) Ya ƙara cewa zai mai da ‘wurin takawar ƙafafuwansa,’ wato matakin sawunsa wuri “mai daraja.” (Isha. 60:13) Ta yaya yake yin haka? Kuma mene ne hakan yake nufi a gare mu da yake muna zama a ‘matashin sawu’ na Allah?

2 Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa duniya ‘matashin sawu’ ne. Ƙari ga haka, an kwatanta haikali na dā da Isra’ilawa suka yi amfani da shi a matsayin matashi sawu. (1 Laba. 28:2; Zab. 132:7) A lokacin, haikalin shi ne cibiyar bauta ta gaskiya a duniya. Saboda haka, abu mai kyau ne a gaban Allah. Zaman haikalin a duniya ya mai da duniya wuri mai daraja da kuma matashin sawun Jehobah.

3. Mene ne haikali na alama, kuma yaushe ne aka soma amfani da shi?

3 A yau babu wani haikali na zahiri a duniya da ke wakiltar bauta ta gaskiya. Amma, akwai haikali na alama da yake wakiltar bauta ta gaskiya kuma yana ɗaukaka Jehobah fiye da haikali na zahiri. Haikali na alama tsari ne na yin sulhu da Allah. Hakan ya yiwu ne don hidimar da Yesu yake yi a matsayinsa na firist da kuma hadayar fansa da ya yi sa’ad da ya zo duniya. An soma bin wannan tsarin a shekara ta 29 bayan haihuwar Yesu, a lokacin da aka yi masa baftisma kuma aka shafe shi a matsayin Babban Firist na haikali na alama da Jehobah ya samar.—Ibran. 9:11, 12.

4, 5. (a) Ta yaya Zabura 99 ta kwatanta ainihin burin bayin Jehobah? (b) Wace tambaya ce ya kamata mu yi wa kanmu?

4 Muna nuna godiya ga Jehobah don wannan tsarin bauta ta gaskiya ta wajen sanar da mutane game da sunan Jehobah da kuma ɗaukaka shi saboda tanadin da ya yi mana na fansa. Muna farin ciki cewa Kiristoci na gaskiya fiye da miliyan takwas a yau suna girmama Jehobah! Wasu masu bin addini sun ɗauka cewa sai sun je sama bayan sun mutu kafin su yabi Allah, amma hakan ba gaskiya ba ne. Shaidun Jehobah sun san cewa yanzu ne kuma a nan duniya ne ya kamata mu yabi Jehobah.

5 Sa’ad da muka yabi Jehobah, muna yin koyi da bayin Jehobah masu aminci da aka kwatanta a Zabura 99:1-3, 5. (Karanta.) Wannan zaburar ta nuna cewa Musa da Haruna da Sama’ila sun tallafa wa tsarin bauta ta gaskiya a zamaninsu. (Zab. 99:6, 7) Kafin shafaffu su je sama don su yi hidima tare da Yesu a matsayin firistoci, suna bauta wa Jehobah a duniya ta wajen bin tsarin bauta ta gaskiya. Miliyoyin “waɗansu tumaki” suna goyon bayansu da aminci. (Yoh. 10:16) Shafaffu da waɗansu tumaki suna bauta wa Jehobah cikin haɗin kai a duniya duk da cewa begensu ya bambanta. Amma, ya kamata kowannenmu ya tambayi kansa, ‘Shin ina ba da cikakken goyon bayana ga tsarin bauta ta gaskiya da Jehobah ya kafa?’

SU WANE NE SUKE HIDIMA A HAIKALI NA ALAMA?

6, 7. Wace matsala ce Kiristoci na farko suka fuskanta, kuma me ya faru shekaru da yawa bayan haka?

6 An annabta cewa za a yi ridda kuma hakan ya soma faruwa kafin ikilisiyar Kirista ya kai shekara ɗari. (A. M. 20:28-30; 2 Tas. 2:3, 4) Bayan haka, gane waɗanda suke bin tsarin bauta ta gaskiya ya yi wuya. Shekaru da yawa sun wuce kafin Jehobah ya yi amfani da sabon Sarki da ya kafa wato, Yesu Kristi don ya bayyana waɗanda suke bin tsarin bauta ta gaskiya.

7 A shekara ta 1919, an bayyana waɗanda Jehobah ya amince da su da suke hidima a haikali na alama. Sun kyautata yadda suke ibada don Allah ya amince da hidimarsu. (Isha. 4:2, 3; Mal. 3:1-4) Wahayin da manzo Bulus ya gani shekaru da yawa kafin wannan lokacin ya soma cika.

8, 9. Ka bayyana sassa uku na “faradise” wato aljannar da Bulus ya gani a cikin wahayi.

8 An kwatanta wahayin Bulus a 2 Korintiyawa 12:1-4. (Karanta.) Bulus ya ga wahayi game da wani abin da zai faru a nan gaba. Sa’ad da aka “fyauce [Bulus] har sama ta uku,” wane “faradise” ko kuma aljanna ce ya gani? Aljannar da Bulus ya yi maganarta tana iya nufin aljannar da za mu mora a duniya a nan gaba. (Luk. 23:43) Tana iya nufin yanayi na cikakkiyar salama da za mu mora a sabuwar duniya. Ƙari ga haka, tana iya nufin babban gata na kasancewa tare da Jehobah a sama.—R. Yoh. 2:7.

9 Me ya sa Bulus ya ce ya “ji zantattuka waɗanda ba su faɗuwa, waɗanda ba ya halatta mutum shi furta ba”? Domin lokaci da zai bayyana abubuwan al’ajabi da ya gani a cikin wahayin bai kai ba. Amma yanzu, ya dace mu gaya wa mutane game da abubuwa masu kyau da bayin Allah suke jin daɗinsa.

10. Me ya sa yanayi na salama da bayin Allah suke mora ba ɗaya ba ne da haikali na alama?

10 Mukan yi magana game da irin yanayi mai kyau da Shaidun Jehobah suke mora yanzu. Wannan yanayin shi ne dangantaka ta kud da kud da muke mora da Allah da kuma ’yan’uwanmu. Amma kada mu ɗauka cewa yanayi na salama da muke mora ɗaya ne da haikali na alama. Haikali na alama shi ne tsarin da Allah ya yi don bauta ta gaskiya. Bayin Allah suna bin wannan tsarin shi ya sa suke moran wannan yanayi mai kyau a yau.—Mal. 3:18.

11. Wane gata ne muke da shi a yau da ya shafi yanayi na salama da muke mora?

11 Muna farin cikin sanin cewa tun shekara ta 1919, Jehobah ya ba wa ’yan Adam ajizai gatan yin aiki tare da shi wajen samar da wannan yanayi na salama, da kyautata da kuma faɗaɗa shi. Shin kana yin iya ƙoƙarinka a yin wannan aiki mai ban sha’awa? Kana nuna godiya saboda gatan yin aiki tare da Jehobah da kuma ɗaukaka shi a ‘matashin sawunsa,’ wato a duniya?

ANA DAƊA KYAUTATA TSARIN ƘUNGIYAR JEHOBAH

12. Wane tabbaci ne muke da shi game da cikar annabcin da ke Ishaya 60:17? (Ka duba hoton da ke shafi na 7.)

12 Annabi Ishaya ya annabta cewa za a yi canje-canje da gyare-gyare a sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya. (Karanta Ishaya 60:17.) Sababbin Kiristoci da kuma matasa sun karanta ko kuma sun ji labarin waɗannan canje-canjen. Amma akwai ’yan’uwa maza da mata da yawa da suka sami gatan shaida waɗannan canje-canjen masu ban al’ajabi! Waɗannan ’yan’uwa masu aminci sun tabbata cewa Jehobah yana amfani da Sarkinmu, Yesu Kristi wajen ja-gorar ƙungiyarsa! Kamar su, muna da kyakkyawan dalili na kasancewa da bangaskiya. Sa’ad da muka ji labaran waɗannan canje-canjen daga bakinsu, muna ƙara kasancewa da aminci ga Jehobah.

13. Bisa ga Zabura 48:12-14, mene ne ya wajaba mu yi?

13 Ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah ko ba mu daɗe ba, wajibi ne mu gaya wa mutane game da ƙungiyar Jehobah. Kwanciyar hankali da haɗin kai da muke mora abin ban al’ajibi ne a wannan zamanin duk da cewa duniya tana cike da mugunta da lalaci da kuma ƙiyayya. Hakika, muna farin ciki saboda gatan da muke da shi na bayyana wa “tsara mai-tasowa” game da abubuwa masu ban al’ajabi na ƙungiyar Jehobah ko kuma “Sihiyona,” da kuma gaskiya game da yanayi na salama da muke mora yanzu!—Karanta Zabura 48:12-14.

14, 15. Waɗanne canje-canje ne aka yi bayan 1970 kuma ta yaya suka amfani ƙungiyar Jehobah?

14 Waɗanda suka daɗe a cikinmu sun shaida wasu canje-canjen da suka daɗa inganta sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya. Za su iya tuna da lokacin da ɗan’uwa guda yake kula da ikilisiya maimakon rukunin dattawa da kuma lokacin da mutum ɗaya ne ke kula da ofishin Shaidun Jehobah maimakon Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Shaidun Jehobah. Ƙari ga haka, akwai lokacin da Watch Tower Society take da Shugaba kuma shi yake ba da ja-gora maimakon Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. Ko da yake wasu ’yan’uwa da dama sun taimaka wa waɗannan amintattun ’yan’uwa masu kula, amma mutum ɗaya ne ke tsai da shawarwari a cikin ikilisiya ko ofishin Shaidun Jehobah ko kuma hedkwatar Shaidun Jehobah. Bayan shekara ta 1970, an yi gyare-gyare kuma a aka ba rukunin dattawa hakkin tsai da shawarwarin gudanar da ayyuka maimakon a bar wa mutum ɗaya.

15 Waɗannan gyare-gyaren sun amfani ƙungiyar Jehobah. Me ya sa? Domin an yi su ne bisa ga ƙarin haske da ake samu game da koyarwar Littafi Mai Tsarki. Maimakon mutum ɗaya ya riƙa tsai da shawarwari, ƙungiyar tana amfana daga halaye masu kyau na dukan dattawa, wato “kyautai ga mutane” da Jehobah ya tanadar wa mutanensa.—Afis. 4:8; Mis. 24:6.

Jehobah yana tanadar da ja-gora da mutane suke bukata a dukan duniya (Ka duba sakin layi na 16 da 17)

16, 17. Waɗanne canje-canje ne suka burge ka, kuma me ya sa?

16 Ka yin tunanin canje-canje da aka yi a kwana baya game da littattafanmu, alal misali, an ƙara ƙawata da kyautata tsarin rubutun da kuma yadda ake rarraba su. Sa’ad da muke wa’azi, muna farin cikin ba da littattafai masu kyan gani da ke kyautata rayuwar mutane! Ƙari ga haka, sa’ad da muka yi amfani da fasaha ta zamani kamar dandalin jw.org wajen yaɗa koyarwar gaskiya, muna yin koyi da Jehobah don yana ƙaunar mutane shi ya sa yake tanadar da taimako da suke bukata.

17 Ban da haka, canjin da aka yi game da taronmu don mu keɓe lokacin yin Ibada ta Iyali da yamma ko kuma nazari na kanmu yana inganta rayuwarmu sosai. Ba za mu manta da canji da aka samu a yadda ake gudanar da manyan taronmu ba. Hakika, yadda ake tsara manyan taronmu yana ƙara kyau kowace shekara! Kuma idan muka yi la’akari da koyarwar da ake tanadarwa a makarantun ƙungiyar Jehobah, sai godiya muke yi. Waɗannan canje-canjen suna nuna cewa Jehobah ne yake ja-gorar ƙungiyarsa kuma yana ci gaba da kyautata yanayi na salama da muke mora yanzu.

YADDA ZA KA KYAUTATA YANAYI NA SALAMA DA MUKE MORA

18, 19. Ta yaya za mu kyautata yanayi na salama da muke mora?

18 Jehobah ya ba mu gatan taimakawa a kyautata yanayin na salama da muke mora yanzu. Muna yin haka ta yin wa’azi da himma da kuma taimaka wa mutane su zama almajiran Yesu. Duk lokacin da muka taimaka wa wani ya soma bauta wa Jehobah, muna ƙara kyautata wannan yanayi na salama da bayin Allah suke mora.—Isha. 26:15; 54:2.

19 Za mu kuma iya kyautata wannan yanayin ta inganta halayenmu na Kirista. Idan muka yi hakan, muna sa mutane da suke lura da mu su so wannan yanayi na salama da bayin Allah suke mora. A yawanci lokaci, ba sanin koyarwar Littafi Mai Tsarki ba ne yake sa mutane su soma bauta wa Jehobah ba, amma hali mai kyau da kuma kwanciyar hankali da muke jin daɗinsa ne yake sa mutane su zama mabiyan Kristi da kuma bayin Jehobah.

Kana iya saka hannu wajen kyautata wannan yanayi na salama da bayin Allah suke mora a yau (Ka duba sakin layi na 18 da 19)

20. Mene ne ya kamata ya zama muradinmu bisa ga Misalai 14:35?

20 Jehobah da Yesu suna farin ciki matuƙa sa’ad da suka ga yadda muke moran yanayi na salama a yau. Farin ciki da muke yi a yanzu sa’ad da muke yin iya ƙoƙarinmu don mu kyautata wannan yanayin soma taɓi ne na farin ciki da za mu yi a nan gaba. A lokacin za mu yi aiki don mu mai da wannan duniya ta zama aljanna na zahiri. Ya kamata mu riƙa tuna da abin da aka ambata a cikin Misalai 14:35, ta ce: “Tagomashin sarki yana fuskanta wajen baran da ke aiki da hikima.” Bari mu zama masu hikima yayin da muke aiki tuƙuru don mu kyautata yanayi na salama da muke mora!