Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DAGA TARIHINMU

Ya Ga Cewa Masu Shirya Abincin Suna Kaunar Juna

Ya Ga Cewa Masu Shirya Abincin Suna Kaunar Juna

MUNA yin farin ciki sosai a duk lokacin da muka halarci manyan taronmu. Sa’ad da mutanen Allah suka taru don samun koyarwa ta ibada, suna jin daɗin cin abinci tare da ’yan’uwansu.

Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi wani babban taron kwana 8 a birnin Cedar Point, Ohio, a Amirka a watan Satumba na shekara ta 1919. An yi shiri don baƙin su sauka a hotal dabam-dabam kuma a can za a ba su abinci, amma dubbai suka hallara fiye da yadda ake tsammani. Masu ba da abinci a hotal ɗin sun ga cewa aiki ya fi ƙarfin su saboda yawan mutanen, sai dukansu suka yi yaji nan take. Manajan ya damu sai ya yi tambaya ko akwai matasan da za su iya taimakawa daga cikin baƙin, matasa da yawa sun ba da kansu. Wata ’yar’uwa mai suna Sadie Green tana cikin waɗanda suka taimaka, ta ce: “A lokacin ne na soma aikin rarraba abinci, amma mun ji daɗin haka.”

Saliyo, 1982

Shekaru bayan haka, aka soma dahuwa a manyan taro kuma hakan ya ba wa ’yan’uwa maza da mata da yawa dama su taimaka. Yin aiki da ’yan’uwa masu bi ya taimaka wa matasa da yawa su kafa maƙasudai a bautar Jehobah. Gladys Bolton da ta yi aiki a wurin dafa abinci a wani babban taro da aka yi shekara ta 1937 ta ce: “Na haɗu da mutane daga wasu wurare kuma na ji yadda suke magance matsalolinsu. A lokacin ne na soma tunanin zama majagaba.”

Wata da ta halarci taron mai suna Beulah Covey ta ce: “Yadda masu aikin suka ba da kansu ya sa aikin yana tafiya sumul ba tare da wata matsala ba.” Ko da yake, hakan ba ya nufi cewa aikin ba ya tattare da wasu ƙalubale. Wani ɗan’uwa mai suna Angelo Manera yana isa taron sai aka gaya masa cewa shi zai kula da dahuwar. Ya ce: “Sanin haka ya sa ni fargaba sosai!” Shirye-shiryen da aka yi don taron ya haɗa da tonon lambatu mai tsawon kafa 1,320 don saka bututun iskar gas zuwa kicin!

Birnin Frankfurt, Jamus, 1951

A shekara ta 1982 a ƙasar Saliyo, ’yan’uwa masu ƙwazo sun ba da kai wajen share filin kuma suka gina wurin dafa abincin da kayayyakin da suke da shi a lokacin. A shekara ta 1951, a birnin Frankfurt da ke ƙasar Jamus, wasu ’yan’uwa masu basira sun ɗauki hayar jirgin ƙasa suka yi amfani da injinsa wajen tanadar tiririn ruwan zafi don dafa abinci a tukwane 40. Masu rarraba abinci sun ba wa mutane 30,000 abinci a cikin awa ɗaya. Masu halartan taro sun je da cokulansu da wuƙaƙensu na cin abinci kuma hakan ya rage aiki wa mutane guda 576 da ke wanke kwanuka. Masu dafa abinci a birnin Yangon da ke ƙasar Myanmar sun rage amfani da barkono masu zafi sa’ad da suke dafa abinci don baƙin da suka zo daga ƙasashen waje.

“SUNA CIN ABINCI A TSAYE”

Wata ’yar’uwa mai suna Annie Poggensee ta amfana sa’ad da take tsaye a cikin zafin rana a layin masu jiran abinci a wani taro da aka yi a Amirka a shekara ta 1950. Ta ce: “Na mai da hankalina gabaki ɗaya ga maganar da wasu ’yan’uwa mata suke yi. Waɗannan ’yan’uwan sun bi jirgin ruwa zuwa taron daga Turai.” Kowannensu ta bayyana yadda Jehobah ya taimaka mata ta halarci taron. Ta daɗa da cewa: “Babu wanda ya kai waɗannan ’yan’uwa mata biyun farin ciki . . .. Tsayawa da suka yi suna jira a layin da zafin ranar bai dame su ba ko kaɗan.”

A waɗannan manyan taron da yawa, an jera tebura masu tsayi a waɗannan wuraren cin abincin don mutane su gama cin abinci da wuri kuma su ba wa wasu dama. In ba a bi wannan tsarin ba, zai yi wuya a ciyar da dubban mutane da rana. Wani mutum da ba Mashaidi ba ya ce: “Wannan wani irin addini ne haka? Suna cin abinci a tsaye.”

Hukumomi da ma’aikatan soja sun yi mamakin yadda wannan tsarin yana tafiya sumul kuma babu cikas. Wani hafsan Sojan Amirka ya bincika wurin cin abincinmu a filin wasan Yankee da ke birnin New York kuma bayan haka, sai ya ƙarfafa wani Manjo mai suna Faulkner na hukumar tanadar da kayayyakin yaƙi na ƙasar Biritaniya ya yi irin wannan bincike. Saboda haka, shi da matarsa sun halarci taron “Triumphant Kingdom” (Mulki Mai Nasara) da aka yi a garin Twickenham, a ƙasar Ingila, a shekara ta 1955. Ya ce ya ga cewa masu shirya abincin suna ƙaunar juna.

Shekara da yawa masu ba da kai don aikin sun tanadar da abinci mai kyau da araha ga mahalartan taro. Amma, don a cim ma wannan gagaruman aikin, an bukaci ’yan’uwa da yawa su yi aiki na sa’o’i da yawa. Sakamakon haka, ba sa samun damar sauraron wasu ko kuma jawaban da aka bayar a taron. Saboda haka, aka sauƙaƙa tsarin ba da abinci a taro a wurare da yawa a shekara ta 1978. A shekara ta 1995, an gaya wa masu halartan taro su soma zuwa da abincinsu. Hakan ya taimaka wa masu dahuwa da kuma rarraba abinci su sami damar sauraron jawabai da kuma cuɗanya. *

Babu shakka, Jehobah ya ji daɗin waɗannan ’yan’uwa da suka ba da kansu don yi wa ’yan’uwansu masu bi hidima! Wasu wataƙila ba su ji daɗi ba cewa an daina dafa da kuma rarraba abinci a taronmu. Amma har ila, ƙauna tana da muhimmanci sosai a manyan taronmu.—Yoh. 13:34, 35.

^ sakin layi na 12 Har ila, akwai zarafin taimakawa a wasu sassa a manyan taro.