Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Za Ka Iya Yin Tsayayya da Shaidan Kuma Ka Yi Nasara!

Za Ka Iya Yin Tsayayya da Shaidan Kuma Ka Yi Nasara!

Ku tsaya masa fa [Shaiɗan], kuna tabbatawa cikin bangaskiyarku.”1 BIT. 5:9.

1. (a) Me ya sa yaƙinmu da Shaiɗan yake da muhimmanci yanzu? (b) Ta yaya muka san cewa za mu iya yin nasara a yaƙinmu da Shaiɗan?

SHAIƊAN yana yaƙi da shafaffu da suka rage da kuma “waɗansu tumaki.” (Yoh. 10:16) Burin Shaiɗan shi ne ya ɓata dangantakarmu da Jehobah a cikin ɗan lokacin da ya rage masa. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 12:9, 12.) Za mu iya yin nasara a yaƙinmu da Shaiɗan kuwa? Hakika! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku yi tsayayya da Shaiɗan, za ya fa guje muku.”—Yaƙ. 4:7.

2, 3. (a) Me ya sa Shaiɗan yake son mutane su gaskata cewa bai wanzu ba? (b) Ta yaya ka san cewa Shaiɗan ya wanzu da gaske?

2 Mutane da yawa ba su yarda cewa Shaiɗan yana wanzuwa ba. Suna gani cewa Shaiɗan da aljanu ƙage ne da ake faɗan labarinsu a cikin littattafai da fina-finan ban tsoro da wasannin bidiyo. A ra’ayinsu, bai kamata duk wani mutum mai tunani ya gaskata cewa akwai aljanu ba. Shin kana ganin Shaiɗan da aljanu sun damu ne da ra’ayin nan da mutane suke da shi game da su cewa ba su wanzu ba? Da kyar. Yana da sauƙi a wurin Shaiɗan ya yaudari waɗanda ba su gaskata cewa ya wanzu ba. (2 Kor. 4:4) Ra’ayin nan cewa Shaiɗan da aljanu ba su wanzu ba hanya ɗaya ne da Shaiɗan yake yaudarar mutane da shi.

3 Da yake mu Shaidun Jehobah ne, ba mu amince da wannan ƙaryar ba. Mun san cewa Shaiɗan ya wanzu kuma shi ne ya yi amfani da maciji don ya yi magana da Hawwa’u. (Far. 3:1-5) Shaiɗan ne ya zargi Jehobah game da Ayuba. (Ayu. 1:9-12) Har ila, Shaiɗan ne ya so ya jarabci Yesu. (Mat. 4:1-10) Shaiɗan ya soma “yaƙi” da shafaffu da suka rage a duniya bayan an kafa Mulkin Allah a shekara ta 1914. (R. Yoh. 12:17) Har yanzu, Shaiɗan yana yaƙi kuma burinsa shi ne ya sa shafaffun da suka rage a duniya da kuma waɗansu tumaki su ɓata dangantakarsu da Allah. Wajibi ne mu yi tsayayya da Shaiɗan kuma mu kasance da bangaskiya sosai idan muna so mu yi nasara a kan Shaiɗan. A wannan talifin, za mu tattauna hanyoyi uku da za su taimaka mana mu yi hakan.

KA GUJI GIRMAN KAI

4. Ta yaya Shaiɗan ya nuna cewa shi ya soma girman kai?

4 Shaiɗan mai girman kai ne sosai. Hakika, wannan halittar ruhu ya ƙalubalanci sarautar Jehobah kuma ya mai da kansa alla don mutane su bauta masa maimakon su bauta wa Jehobah. Hakika, Shaiɗan shi ne tushen girman kai. Saboda haka, idan muna so mu yi nasara a kan Shaiɗan, wajibi ne mu kasance da tawali’u kuma mu guji girman kai.—Karanta 1 Bitrus 5:5.

5, 6. (a) Laifi ne mutum ya riƙa ɗaukan kansa da mutunci? Ka bayyana. (b) Waɗanne misalan Littafi Mai Tsarki ne suka nuna cewa girman kai bai da kyau?

5 Ba laifi ba ne mu riƙa ɗaukan kanmu da mutunci ko kuma mu riƙa yin farin ciki don wasu abubuwan da mu ko wasu da suke kusa da mu suka cim ma ko kuma mallaka. Manzo Bulus ya gaya wa ’yan’uwa da ke Tasalonika cewa: “Muna fahariya domin ku cikin ikilisiyai na Allah, saboda hanƙurinku da bangaskiyarku cikin dukan tsanani naku da kuncin da kuke jimrewa da shi.” (2 Tas. 1:4) Saboda haka, yana da kyau mu yi farin ciki game da abubuwan da wasu suka cim ma kuma mu riƙa ganin kanmu da mutunci. Bai kamata mu riƙa gudun iyalinmu ko al’adarmu ko kuma inda muka girma ba.—A. M. 21:39.

6 Amma kuma yawan alfahari zai iya ɓata zumuncinmu da mutane da kuma dangantakarmu da Jehobah. Yawan alfahari zai iya sa mu ɓata rai idan aka ba mu shawara ko kuma mu ƙi shawara. (Zab. 141:5) Yawan alfahari shi ne girman kai ko kuma takama da mutane suke yi don suna ganin cewa sun fi wasu mutunci ko da hakan ba gaskiya ba ne. Jehobah ya ƙi jinin “girman kai.” (Ezek. 33:28; Amos 6:8, Littafi Mai Tsarki) Shaiɗan yana farin ciki idan ya ga mutane suna fariya da girman kai don suna koyi da shi. Babu shakka, Shaiɗan ya yi farin ciki sosai sa’ad da mutane kamar su Nimrod da Fir’auna da kuma Absalom suka nuna girman kai! (Far. 10:8, 9; Fit. 5:1, 2; 2 Sam. 15:4-6) Ƙari ga haka, girman kai ne ya sa Kayinu ya ɓata dangantakarsa da Allah. Jehobah ne da kansa ya yi masa gargaɗi, amma girman kai ya sa ya yi watsi da gargaɗin. Hakan ya kai shi ga yin zunubi.—Far. 4:6-8.

7, 8. (a) Mene ne bambancin launin fata, kuma ta yaya yake da alaƙa da girman kai? (b) Ka bayyana yadda girman kai zai iya sa a daina kasancewa da salama a cikin ikilisiya.

7 A yau, mutane da yawa suna nuna girma kai a hanyoyi dabam-dabam. A wani lokaci, girman kai yana da alaƙa da nuna bambancin launin fata. Wani ƙamus ya ce nuna bambancin launin fata yana nufin “wariya ko kuma ƙiyayya da ake nuna wa mutane don launin fatarsu dabam ne” da kuma “ra’ayin nan cewa baiwar mutum ya dangana ne ga launin fatarsa da kuma cewa wasu jinsin mutane sun fi wasu.” Bambancin launin fata ya haddasa zanga-zanga da yaƙe-yaƙe, har ma da kisan ƙare dangi.

8 Mun san cewa bai kamata irin waɗannan abubuwan su faru a cikin ikilisiyar Kirista ba. Duk da haka, bambancin ra’ayi da ake samu a wasu lokatai tsakanin ’yan’uwa saboda girma kai zai iya haifar da mugun sakamako. Kiristoci na ƙarni na farko sun taɓa samun kansu a irin wannan yanayi kuma shi ya sa Yaƙub ya yi musu wannan tambaya mai muhimmanci: “Me ke haddasa gāba da husuma tsakaninku?” (Yaƙ. 4:1, LMT) Hakika, idan mun ƙi jinin wasu kuma muka ɗauka mun fi su, za mu iya yin magana ko kuma yi wani abin da zai ɓata musu rai. (Mis. 12:18) Hakan ya nuna cewa girma kai zai iya sai a daina kasancewa da salama a cikin ikilisiya.

9. Ta yaya Littafi Mai Tsarki yake taimaka mana mu guji girman kai da kuma fariya? (Ka duba hoton da ke shafi na 14.)

9 Idan muna gani cewa mun fi wasu, ya kamata mu tuna cewa: “Ubangiji yana ƙin kowane mutum da ke fariya.” (Mis. 16:5, LMT) Zai dace mu bincika yadda muke ɗaukan waɗanda suka fito daga wani jinsi ko ƙasa ko kuma al’ada. Idan muna nuna bambancin launin fata ko kishin ƙasa, ba ma la’akari cewa “daga tushe ɗaya kuwa [Allah] ya yi dukan al’umman mutane.” (A. M. 17:26) Tushen dukan mutane ɗaya ne don dukanmu ’ya’yan Adamu ne. Saboda haka, ra’ayin nan cewa wasu launin fata sun fi wasu wauta ne. Irin wannan ra’ayin shi ne abin da Shaiɗan yake so, don ba ya son mu so juna kuma mu kasance da haɗin kai. (Yoh. 13:35) Idan muna son mu yi tsayayya da Shaiɗan kuma mu yi nasara, wajibi ne mu guji girman kai ko kuma fariya.—Mis. 16:18.

KA GUJI SON ABIN DUNIYA

10, 11. (a) Me ya sa yake da sauƙi mutum ya soma son abin duniya? (b) Ta yaya Dimas ya nuna cewa yana son abin duniya?

10 Shaiɗan shi ne “mai-mulkin wannan duniya.” (Yoh. 12:31; 1 Yoh. 5:19) Saboda haka, yawancin abubuwan da ake ɗaukakawa a wannan duniyar sun saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Amma, ba dukan abubuwan da ke duniya ne ba su da kyau ba. Duk da haka, ya kamata mu san cewa Shaiɗan zai yi amfani da wannan duniyar don ya rinjaye mu mu yi zunubi ko kuma mu soma son abin duniya kuma mu yi watsi da ibada.—Karanta 1 Yohanna 2:15, 16.

11 Wasu Kiristoci a ƙarni na farko sun so abin duniya. Alal misali, manzo Bulus ya ce: “Dimas ya yashe ni, yana ƙaunar wannan zamani na yanzu.” (2 Tim. 4:10) Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai ambata ainihin abin da Dimas ya so da ya sa ya bar Bulus ba. Wataƙila Dimas ya soma son abin duniya fiye da ibadarsa ga Jehobah. Idan haka ne, ya yi watsi da gata a hidimar Jehobah kuma ya yi hakan don abin duniya. Shin abin duniya zai kai albarkar da zai samu a matsayinsa na mai hidima tare da Bulus a bautar Jehobah ne? Ko kaɗan!—Mis. 10:22.

12. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya faɗa wa tarkon “ruɗin dukiya”?

12 Irin wannan abin zai iya faruwa da mu. Da yake mu Kiristoci ne, ya dace mu yi tanadi don biya wa kanmu da kuma iyalinmu bukata. (1 Tim. 5:8) Idan muka yi la’akari da yanayi mai kyau da Jehobah ya tanadar wa Adamu da Hawwa’u, za mu san cewa yana son mu ji daɗin rayuwa. (Far. 2:9) Amma Shaiɗan zai iya yaudararmu da “ruɗin dukiya.” (Mat. 13:22) Mutane da yawa suna gani cewa kuɗi da abin duniya za su sa su farin ciki da kuma ci gaba. Irin wannan tunanin ba ƙaramin yaudara ba ne, kuma zai iya sa mu rasa abin da ya fi muhimmanci a rayuwarmu, wato dangantakarmu da Jehobah. Yesu ya yi wa mabiyansa gargaɗi cewa: “Ba wanda ke da iko shi bauta wa ubangiji biyu: gama ko shi ƙi ɗayan, shi ƙaunaci ɗayan: ko kuwa shi lizimci ɗayan, shi rena ɗayan. Ba ku da iko ku bauta wa Allah da dukiya ba.” (Mat. 6:24) Idan muka saka biɗan dukiya kan gaba a rayuwarmu, kamar mun daina bauta wa Jehobah kuma abin da Shaiɗan yake so mu yi ke nan. Kada mu taɓa barin kuɗi ko kuma abin duniya ya kasance mana da muhimmanci fiye da ibadarmu ga Jehobah. Wajibi ne mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kuɗi da abin duniya idan muna so mu yi nasara a gwagwarmayarmu da Shaiɗan.—Karanta 1 Timotawus 6:6-10.

KA GUJI YIN ZINA

13. Ta yaya duniyar nan take ɗaukaka mummunan ra’ayi game da aure da kuma jima’i?

13 Zina wata tarko ce da Shaiɗan yake amfani da ita. A yau, mutane da yawa suna gani cewa riƙon amana a aure tsohon yayi ne kuma yana hana mutum sakewa. Alal misali, wata sananniyar ’yar wasan fim ta ce: “Bai dace namiji ya auri mata ɗaya ba ko kuma tamace ta auri miji ɗaya kawai ba. Ban taɓa ganin mace ko mijin da bai taɓa cin amana ko kuma wanda ba ya son ya yi hakan ba.” Wani sanannen ɗan wasan fim ya ce: “Ban tabbata ba cewa an yi mu don mu zauna da mutum ɗaya kawai a rayuwarmu ba.” Shaiɗan yana farin ciki idan sanannun mutane suna sūkar tsarin aure da Allah ya kafa wa ’yan Adam. Shaiɗan ba ya son mutane su bi tsarin auren mace ɗaya da miji ɗaya da Allah ya kafa ya yi nasara. Idan muna son mu yi nasara a yaƙinmu da Shaiɗan, wajibi ne mu bi tsarin aure da Allah ya kafa.

14, 15. Ta yaya za mu guji yin zina?

14 Ko da muna da aure ko a’a, wajibi ne mu yi iya ƙoƙarinmu mu guje wa kowace irin lalata. Shin hakan yana da sauƙi ne? A’a. Idan kai matashi ne, za ka iya jin abokan makarantarka suna fariya game da yin zina da duk wanda suka ga dama ko kuma aika saƙon hotunan batsa ta wayar salula. A wasu wurare, laifin aika hotunan batsa ɗaya ne da na yin amfani da ƙananan yara don batsa. Littafi Mai Tsarki ya ce duk wanda ya yi “fasikanci yana yi wa jiki nasa zunubi.” (1 Kor. 6:18) Mutane da yawa suna wahala da kuma mutuwa saboda cututtuka da ake samu ta wurin lalatar jima’i. Wani bincike ya nuna cewa yawancin matasa marasa aure da suka yi jima’i sun ce sun yi da-na-sani saboda hakan. Masu fina-finai suna so mu gaskata cewa idan mun ƙarya dokar Allah ba abin da zai faru. Irin wannan ra’ayin ne yake sa mutane su faɗa wa “yaudarar zunubi.”—Ibran. 3:13, LMT.

15 Idan kana fuskantar gwajin yin zina a kowane lokaci, mene ne ya kamata ka yi? Ka fahimci cewa kana da kasawa. (Rom. 7:22, 23) Ka roƙi Allah ya ba ka ƙarfin hali. (Filib. 4:6, 7, 13) Ka guje wa yanayin da zai kai ga yin zina. (Mis. 22:3) Kuma idan ka fuskanci jaraba, ka guje wa jarabar nan da nan.—Far. 39:12.

16. Ta yaya Yesu ya mai da martani ga gwajin da Shaiɗan ya yi masa, kuma wane darasi ne za mu koya daga wannan misali?

16 Yesu ya kafa misali mai kyau a yin tir da gwaji. Bai yarda Shaiɗan ya rinjaye shi ba, kuma bai tsaya ya yi tunani a kan alkawuran da Shaiɗan ya yi masa ba. A maimakon haka, ya mai da martani da waɗannan kalaman: “An rubuta.” (Karanta Matta 4:4-10.) Yesu ya san Kalmar Allah, kuma hakan ya taimaka masa ya ɗauki mataki kuma ya yi ƙaulin nassosi sa’ad da ya fuskanci gwaji. Idan muna so mu yi nasara a yaƙinmu da Shaiɗan, kada mu taɓa yarda mu faɗa wa jarabar yin zina.—1 Kor. 6:9, 10.

ZA KA YI NASARA IDAN KA JURE

17, 18. (a) Waɗanne tarkuna ne kuma Shaiɗan yake amfani da su, kuma me ya sa hakan ba abin mamaki ba ne a gare mu? (b) Mene ne zai faru da Shaiɗan nan ba da daɗewa ba, kuma ta yaya hakan yake sa ka jimrewa?

17 Shaiɗan yana amfani da girman kai da son abin duniya da kuma zina don ya saka mana tarko. Ban da waɗannan, akwai wasu da yawa. Alal misali, wasu Kiristoci suna fuskantar ƙiyayya daga mambobin iyalinsu, ko abokan makarantarsu suna musu ba’a ko kuma gwamnati tana hana yin wa’azin bishara a yankinsu. Waɗannan abubuwan ba abin mamaki ba ne a gare mu, don Yesu ya gaya wa almajiransa cewa: “Za ku zama abin ƙi ga dukan mutane sabili da sunana: amma wanda ya jimre har matuƙa, shi ne za ya tsira.”—Mat. 10:22.

Za a halaka Shaiɗan kwata-kwata (Ka duba sakin layi na 18)

18 Ta yaya za mu yi tsayayya da Shaiɗan kuma mu yi nasara? Yesu ya gaya wa almajiransa cewa: “Ta cikin haƙurinku za ku sami rayukanku.” (Luk. 21:19) Ba abin da ɗan Adam zai yi da zai hana mu samun rai na har abada. Ba wanda zai iya hana mu kasancewa da dangantaka da Jehobah sai dai idan mun yarda. (Rom. 8:38, 39) Ko da wasu bayin Jehobah sun rasa rayukansu, hakan ba ya nufin cewa Shaiɗan ya yi nasara, don Jehobah zai ta da su daga mutuwa. (Yoh. 5:28, 29) Amma kuma, za a halaka Shaiɗan nan ba da daɗewa ba. Bayan an kawo ƙarshen wannan mugun zamani, za a jefar da Shaiɗan cikin rami marar matuƙa na tsawon shekara dubu. (R. Yoh. 20:1-3) A ƙarshen shekara dubun, za a ‘saki Shaiɗan daga maɗaurarsa’ na ƙanƙanin lokaci kuma a ba shi dama ta ƙarshe don ya yaudari kamiltattun mutane. (R. Yoh. 20:7-10) Hakika, za a halaka Shaiɗan nan ba da daɗewa ba, amma kuma kana da damar yin rayuwa har abada! Saboda haka, ka yi tsayayya da Shaiɗan, kuma ka kasance da aminci. Za ka iya yin tsayayya da Shaiɗan kuma ka yi nasara!