Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ku Auri “Mai Bin Ubangiji” Kadai, Umurnin Yana da Amfani Har Ila?

Ku Auri “Mai Bin Ubangiji” Kadai, Umurnin Yana da Amfani Har Ila?

“Ban sami wanda zan aura a ƙungiyar Jehobah ba, ina tsoro kada in tsufa ban yi aure ba.”

“Wasu maza da ba Shaidu ba suna da hankali da farin jini kuma suna nuna sanin yakamata. Ba za su hana ni zuwa taro ba, ina ganin sun fi wasu a ƙungiyar Jehobah hankali.

Wasu bayin Jehobah da ba su yi aure ba sun yi irin wannan maganar. Duk da haka, sun san shawarar da manzo Bulus ya bayar cewa a auri “mai bin Ubangiji” kaɗai. Kuma ya kamata dukan Kiristoci su bi wannan shawarar. (1 Kor. 7:39, Littafi Mai Tsarki) To, me ya sa suke irin wannan furucin?

ABIN DA YA SA WASU SUKE SHAKKA

Waɗanda suke yin irin wannan kalamin suna ji cewa ’yan’uwa mata marasa aure sun fi ’yan’uwa maza da ba su yi aure ba yawa. Haka yake a ƙasashe da yawa. Ka yi la’akari da misalai biyu: A ƙasar Koriya, a cikin Shaidu 100 da ba su yi aure ba, guda 57 ’yan’uwa mata ne, 43 kuma ’yan’uwa maza ne. Ƙasar Kolombiya ta ba rahoto cewa kashi 66 na Shaidu da ke wurin mata ne, kashi 34 kuma maza ne.

A wasu ƙasashe, iyayen da ba Shaidu ba suna iya ce a ba su kayan tambaya da sadaki mai yawa, kuma hakan yana hana wasu ’yan’uwa maza ba su da kuɗi da yawa auransu. Irin waɗannan abubuwan za su iya sa ’yar’uwa da ba ta yi aure ba ta yi tunani cewa da kyar ta sami wani mai “bin Ubangiji” da za ta aura. Saboda haka, za ta iya tambaya, “Anya, zai dace in ɗauka cewa zan sami wanda zan aura a ƙungiyar Jehobah kuwa?” a

DOGARA GA JEHOBAH YANA DA MUHIMMANCI

Idan kin taɓa yin irin wannan tunanin, ki kasance da tabbaci cewa Jehobah yana sane da yanayinki. Hakika, ya san yadda abin yake damunki.—2 Laba. 6:29, 30.

Duk da haka, Jehobah ya riga ya faɗa a Littafi Mai Tsarki cewa mu auri mai bin Ubangiji kaɗai. Me ya sa? Don ya san cewa hakan zai amfane mu. Yana son ya kāre bayinsa daga baƙin cikin da ke tattare da auren wanda ba Mashaidi ba kuma yana son su yi farin ciki. A zamanin Nehemiya lokacin da Yahudawa suke auren matan da ba sa bauta wa Jehobah, Nehemiya ya yi nuni ga mummunan misalin Sulemanu. Ko da yake “Allahnsa ya ƙaunace shi, . . . baren mata suka sa shi ya yi zunubi.” (Neh. 13:23-26, LMT) Allah ya umurce bayinsa su auri masu bauta wa Jehobah kaɗai don yana so su amfana ne. (Zab. 19:7-10; Isha. 48:17, 18) Kiristoci na gaske suna godiya ga yadda Jehobah yake kula da su kuma suna bin ja-gora da yake yi musu. Da yake sun dogara gare shi, hakan ya nuna cewa sun amince da shi a matsayin Maɗaukakin Sarki.—Mis. 1:5.

Babu shakka, ba ki son ki yi cuɗanya “marar-dacewa” da wanda zai sa ki bijire daga bauta wa Jehobah. (2 Kor. 6:14) Kiristoci da yawa a yau sun bi wannan doka mai kyau na Allah da yake kāre su kuma sun fahimta cewa wannan tafarkin da suka ɗauka ya dace. Amma wasu sun ƙi su bi wannan dokar.

YANA DA AMFANI HAR ILA

Wata ’yar’uwa da ke Ostareliya mai suna Maggy, b ta bayyana abin da ya faru sa’ad da ta fara fita zance da wani da ba Mashaidi ba: “Na fasa halartan wasu taro don in kasance tare da shi. A hankali dangantakata da Jehobah ta yi sanyi.” Wata ’yar’uwa a ƙasar Indiya mai suna Ratana ta soma soyayya da wani abokin ajinsu da ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Amma daga baya, sai ya nuna cewa ainihin muradinsa shi ne su yi soyayya kawai. A ƙarshe, ta bar ƙungiyar Jehobah kuma ta soma bin addininsa don ta aure shi.

Wani misali kuma shi ne na Ndenguè a ƙasar Kamaru. Tana da shekara 19 sa’ad da ta yi aure. Saurayinta ya yi alkawari cewa zai bar ta ta riƙa zuwa taro. Amma makonni biyu bayan aurensu, sai hana ta zuwa taro. Ta ce: “Na kaɗaita kuma sai kuka nake ta yi. Na ga cewa na ɓata rayuwata. Na riƙa yin da-na-sani.”

Hakika, ba dukan waɗanda ba Shaidu ba ne suke wulaƙanta matansu da kuma nuna musu rashin sanin yakamata. Duk da haka, ko da ba ki shan wahala don auren wanda ba Mashaidi ba, ta yaya hakan zai iya shafan dangantakarki da Jehobah? Yaya za ki ji da yake ba ki saurari shawarar da Jehobah yake bayarwa ba? Mafi muhimmanci ma, yaya Jehobah zai ji game da shawarar da kika tsai da?—Mis. 1:33.

’Yan’uwa a faɗin duniya sun shaida cewa auren “mai bin Ubangiji” kaɗai ne abin da ya kamata. Waɗanda ba su yi aure ba sun kuɗiri niyya za su faranta wa Allah rai ta wurin auren mutumin kirki da yake bauta wa Jehobah. Sa’ad da Michiko wata ’yar’uwa a ƙasar Japan ba ta yi aure ba, danginta sun matsa mata ta auri wanda ba Mashaidi ba. Ta ƙi bin shawararsu duk da matsin, ƙari ga haka, ta ga wasu ’yan’uwa mata suna samun waɗanda za su aura a ƙungiyar Jehobah. Ta ce: “Sai na yi tunani cewa da yake Jehobah Allah mai farin ciki ne, na tabbata cewa zan iya yin farin ciki ko ina da aure ko babu. Ina da tabbaci cewa yana ba mu abin da muke so. Saboda haka, idan muna son mu yi aure amma ba mu sami ɗan’uwa ba tukun, zai dace mu ci gaba da jira.” (1 Tim. 1:11) Daga baya, Michiko ta auri wani ɗan’uwa mai kirki, kuma ta yi farin ciki cewa ta jira.

Wasu ’yan’uwa maza sun jira don su auri waɗanda suke so. Abin da wani ɗan’uwa mai suna Bill da ke Ostareliya ya yi ke nan. Ya ce a wasu lokatai yakan yi sha’awar wasu ’yan matan da ba sa bauta wa Jehobah. Duk da haka, ya yi ƙoƙari don kada ya yi cuɗanya da ta wuce gona da iri da su. Me ya sa? Ba ya son ya yi abin da zai sa ya yi cuɗanya “marar-dacewa” da wanda ba Mashaidi ba. A cikin shekarun da suka shige, ya nemi wasu ’yan’uwa mata da aure amma bai yi dace ba. Ɗan’uwa Bill ya jira shekara 30 kafin ya sami wadda ta dace da shi. Bill ya ce: “Ban yi da-na-sani ba. Ya daɗa da cewa: “Ina jin daɗi domin muna fita wa’azi tare, muna nazari tare kuma muna bauta wa Jehobah tare. Ina farin cikin yin tarayya da abokan matata don dukansu masu bauta wa Jehobah ne. Muna inganta aurenmu ta bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.”

YAYIN DA KIKE SAURARON JEHOBAH

Mene ne za ki yi yanzu don ki yi farin ciki yayin da kike sauraron Jehobah? Ya kamata ki yi tunanin dalilin da ya sa ba ki yi aure ba. Idan dalilin shi ne don kina son ki bi abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da auren “mai bin Ubangiji” kaɗai, kina yin abin da ya dace. Ki tabbata cewa Jehobah yana farin cikin kuɗirin da kika yi na yi masa biyayya. (1 Sam. 15:22; Mis. 27:11) Ki ci gaba da faɗa ma Allah dukan damuwarki sa’ad da kike yin addu’a. (Zab. 62:8) Sa’ad da kika ci gaba da yi wa Jehobah addu’a babu fasawa, dangantakarki da Jehobah zai daɗa danƙo. Yayin da kike kasancewa da aminci duk da matsi da kike fuskanta, za ki ci gaba da inganta dangantakarki da Jehobah kowace rana. Ki tabbata cewa Allah Maɗaukaki yana ƙaunar dukan bayinsa masu aminci kuma kina da daraja a gabansa. Ya san abin da kike bukata da abin da kike so. Bai yi alkawari cewa zai ba wa kowane ɗan’uwa ko ’yar’uwa da take neman aure abokin aure ba. Duk da haka, idan kina so ki yi aure, Allah ya san yadda zai biya bukatarki.—Zab. 145:16; Mat. 6:32.

Wataƙila a wasu lokatai kina ji kamar sarki Dauda, sa’ad da ya ce: “Ka yi hanzari ka amsa mini, ya Ubangiji; ruhuna duk ya yi kasala; kada ka ɓoye mini fuskarka.” (Zab. 143:5-7, 10) A waɗannan lokatan ya kamata ki ba Jehobah damar tabbatar miki da nufinsa a gare ki. Za ki iya yin hakan ta wurin karanta Kalmar Allah da kuma yin bimbini sosai a kan abin da kika karanta. Za ki ƙara fahimtar dokokinsa kuma za ki ga yadda ya taimaka wa mutane a dā. Idan kika ci gaba da sauraronsa, za ki sami ƙarfin yi masa biyayya a koyaushe.

Yan’uwa marasa aure suna da amfani a ikilisiya, a yawancin lokaci suna taimaka wa iyalai da matasa da yara

Mene ne zai iya taimaka miki kuma ki ci gaba da kasancewa da farin ciki da kuma amfani a ƙungiyar Jehobah? Ki yi amfani da wannan lokacin don ki koyi wasu halaye kamar su fahimi da karimci da yin aiki da ƙwazo da fara’a da ibada da kuma a san ki da hali mai kyau, don waɗannan halayen ne za su sa ki yi farin ciki sa’ad da kika yi aure. (Far. 24:16-21; Ruth 1:16, 17; 2:6, 7, 11; Mis. 31:10-27) Ki sa Mulkin kan gaba ta wurin zuwa wa’azi da ƙwazo da kuma yin wasu ayyuka a bautar Jehobah don yin waɗannan ayyukan za su kāre ki. Ɗan’uwa Bill da aka ambata dazun ya yi kalami a kan shekarun da yake neman aure cewa: “Shekarun sun wuce da sauri! Na duƙufa a yin hidimar majagaba.”

Hakika, auren “mai bin Ubangiji” kaɗai har ila yana da amfani. Yin biyayya da wannan shawarar zai taimaka miki ki girmama Jehobah kuma ki yi farin ciki da gaske. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai-albarka ne mutum wanda ya ke tsoron Ubangiji, wanda ya ke faranta ransa cikin dokokinsa ƙwarai. Wadata da arziki suna cikin gidansa: Adalcinsa kuma ya tabbata har abada.” (Zab. 112:1, 3) Saboda haka, ki kuɗiri niyyar yin biyayya da dokar Allah da ta ce mu auri “mai bin Ubangiji” kaɗai.

a A wannan talifin, mun mai da hankali ga yadda yanayin ya shafi ’yan’uwa mata ne, amma ƙa’idodin sun shafi ’yan’uwa maza har ila.

b An canja wasu sunayen.