Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ku Inganta Aurenku don Ku Ji Dadinsa

Ku Inganta Aurenku don Ku Ji Dadinsa

Idan ba Ubangiji ya gina gidan ba, banza magina suke aiki.ZAB. 127:1a.

1-3. Waɗanne ƙalubale ne ma’aurata suke fuskanta? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

WANI mutum da ya yi shekara 38 da aure ya ce: “Idan ka yi aiki tuƙuru don ka ji daɗin aurenka, Jehobah zai albarkace ka.” Hakika, ma’aurata za su iya yin farin ciki kuma su taimaka wa juna sa’ad da suke fama da matsaloli.—Mis. 18:22.

2 Amma, ma’aurata za su sha “wahala a cikin jiki.” (1 Kor. 7:28) Me ya sa? Domin fama da matsaloli na yau da kullum zai iya saka aure a cikin hadari. Baƙar magana zai iya sa ma’aurata su ɓata wa juna rai, su yi jayayya ko kuma su riƙa faɗa da juna. Waɗannan abubuwa za su iya kawo cikas a aure kome daɗinsa. (Yaƙ. 3:2, 5, 8) Ma’aurata da yawa suna fama da aikinsu yayin da suke renon yaransu. Damuwa da gajiya ba sa ba wasu ma’aurata damar kasancewa tare don su inganta aurensu. Matsalar kuɗi da rashin lafiya da kuma wasu abubuwa za su iya sa ma’aurata su daina ƙauna da kuma girmama juna. Bugu da ƙari, “ayyukan jiki” kamar su fasikanci da lalata da magabtaka da husuma da kishi da hasala da kuma saɓani za su iya hana ruwa gudu a aure.—Gal. 5:19-21.

3 Ƙari ga haka, mutane a wannan “kwanaki na ƙarshe” suna son zuciya kuma ba sa tsoron Allah kuma waɗannan halaye sukan gurɓata aure. (2 Tim. 3:1-4) Ban da haka, wani mugun maƙiyi ya ƙudiri niyyar ya halaka aure. Manzo Bitrus ya ce: “Magabcinku Shaiɗan, kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.”—1 Bit. 5:8; R. Yoh. 12:12.

4. Mene ne ma’aurata za su yi don su inganta aurensu kuma su yi farin ciki?

4 Wani magidanci a ƙasar Japan ya ce: “Na damu sosai don rashin kuɗi. Kuma da yake ba ma tattaunawa yadda ya dace, ita ma ta damu sosai. Ƙari ga haka, a kwanan baya, ta yi wani rashin lafiya mai tsanani. A wani lokaci, hakan ya jawo saɓani a tsakaninmu.” Hakika, ba za mu iya guje wa ƙalubale a aure ba, amma za mu iya shawo kansu. Da taimakon Jehobah, ma’aurata za su iya inganta aurensu kuma su ji daɗin zama tare. (Karanta Zabura 127:1.) Za mu tattauna abubuwa biyar da za su inganta aure don ya dawwama. Bayan haka, za mu tattauna yadda ƙauna za ta daɗa sa ma’aurata su yi farin ciki a aurensu.

KU BI ƘA’IDODIN JEHOBAH A AURENKU

5, 6. Ta yaya mata da miji za su bi ƙa’idodin Jehobah a aurensu?

5 Ma’aurata za su iya ƙarfafa aurensu idan suka kasance da aminci da biyayya ga wanda ya ƙafa aure. (Karanta Mai-Wa’azi 4:12.) Ma’aurata za su iya yin la’akari da Jehobah a aurensu ta wajen bin ja-gorarsa. Littafi Mai Tsarki ya ce game da mutanen Allah a dā: ‘Kunnuwanku kuma za su ji magana daga bayanku, tana cewa, Wannan ita ce hanya, ku bi ta; yayinda kuke juyawa ga dama, da yayinda kuke juyawa ga hagu.’ (Isha. 30:20, 21) Ma’aurata za su iya ‘jin’ muryar Jehobah ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki tare. (Zab. 1:1-3) Za su daɗa ƙarfafa aurensu idan suna sa Ibada ta Iyalinsu ta kasance da daɗi da kuma ban ƙarfafa. Bugu da ƙari, yin addu’a tare kowace rana yana da muhimmanci wajen ƙarfafa aure kuma hakan zai sa mu jimre da matsalolin da muke fuskanta a duniyar Shaiɗan.

Ta wajen bauta wa Jehobah tare, ma’aurata za su kusaci Allah da juna kuma su ji daɗin aurensu (Ka duba sakin layi na 5 da 6)

6 Gerhard da ke Jamus ya ce: “Duk lokacin da matsaloli ko kuma rashin fahimta ya sa ba ma farin ciki, shawarwarin Kalmar Allah sun taimaka mana mu riƙa haƙuri da kuma gafarta wa juna. Waɗannan halayen suna da muhimmanci idan muna so mu yi farin ciki a aurenmu.” Idan ma’aurata suka yi iya ƙoƙarinsu don su yi la’akari da Allah a aurensu ta wajen yin abubuwan da suka shafi ibada tare, za su kusaci Allah kuma za su ƙaunaci juna. Ƙari ga haka, za su ji daɗin aurensu.

MAGIDANTA, KU NUNA ƘAUNA GA MATANKU A YADDA KUKE BI DA SU

7. Ta yaya ya kamata magidanta su ja-goranci iyali?

7 Yadda maigida yake ja-gora a cikin iyali zai iya ƙarfafa aurensu kuma ya sa su yi farin ciki. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kan kowane namiji Kristi ne; kan mace kuma namiji ne.” (1 Kor. 11:3) Hakan yana nufin cewa ya kamata maigida ya bi da matarsa kamar yadda Kristi ya bi da almajiransa. Yesu ba mai zalunci ba ne, amma a koyaushe yana nuna ƙauna da alheri da sanin ya kamata da tawali’u kuma shi ba mai fahariya ba ne.—Mat. 11:28-30.

8. Mene ne maigida zai yi don matarsa ta so shi kuma ta girmama shi?

8 Magidanta Kiristoci ba sa bukatar su riƙa tuna wa matansu cewa ya kamata su yi musu ladabi da biyayya. Maimakon haka, su ‘zauna da matayensu bisa ga sani.’ Su “ba da girma ga mace, kamar ga wadda ta fi rashin ƙarfi.” (1 Bit. 3:7) Ya kamata magidanta su nuna cewa suna ɗaukan matansu da mutunci ta yadda suke magana da kuma bi da su a cikin jama’a da kuma a cikin gida. (Mis. 31:28) Hakan zai sa matar ta ƙaunaci mijinta kuma ta girmama shi, kuma Allah zai albarkace su.

MATA, KU YI LADABI DA BIYAYYA

9. Ta yaya mace za ta yi ladabi da biyayya?

9 Idan muka ƙaunaci Jehobah da kuma ƙa’idodinsa, hakan zai taimaka mana mu ƙasƙantar da kanmu a gabansa. (1 Bit. 5:6) Hanya ɗaya mai muhimmanci da mata mai ladabi take yin biyayya ga ikon Jehobah ita ce ta wajen ba wa mijinta haɗin kai da kuma taimaka masa a cikin iyali. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku mata, ku yi zaman biyayya da maza naku, abin da ya kamata ke nan cikin Ubangiji.” (Kol. 3:18) Hakika, ba dukan shawarwari da mijinta ya yanke mace za ta so ba. Amma, idan ba su saɓa wa dokokin Allah ba, mata mai yin biyayya za ta kasance a shirye ta bi shawarwarin da mijinta ya yanke.—1 Bit. 3:1.

10. Me ya sa ladabi da biyayya suke da muhimmanci?

10 Mata tana da matsayi mai daraja a cikin iyali, ita ce ‘abokiyar zaman’ mijinta. (Mal. 2:14) Idan ana so a tsai shawara a cikin iyali, tana faɗin ra’ayinta da yadda take ji da ladabi. Miji mai hikima zai saurari ra’ayin matarsa. (Mis. 31:10-31) Yin ladabi da biyayya za su sa iyalin ta kasance da farin ciki da salama da kuma haɗin kai. Ƙari ga haka, hakan zai sa mata da miji su gamsu domin sun san cewa suna faranta wa Allah rai.—Afis. 5:22.

KU RIƘA GAFARTA WA JUNA

11. Me ya sa gafartawa yake da muhimmanci?

11 Idan ma’aurata suna son aurensu ya dawwama suna bukatar su riƙa gafarta wa juna. Mata da miji za su ƙarfafa aurensu idan suna ‘haƙuri da juna, suna gafarta ma juna’ kuma. (Kol. 3:13) Amma sa’ad da ma’aurata suka ƙi gafarta wa juna kuma idan suna riƙe juna a zuci, za su ɓata aurensu. Kamar yadda ginin da ya tsatsage ba zai daɗe ba, zai yi wuya ma’aurata da suke yawan fushi da riƙon juna a zuci su gafarta wa juna. Amma, idan ma’aurata suna gafarta wa juna kamar yadda Jehobah yake gafarta musu, aurensu zai kasance da inganci.—Mi. 7:18, 19.

12. Ta yaya ƙauna take sa a yafe “tulin zunubai”?

12 Ƙauna ta gaske ba ta “nukura.” Maimakon haka, ƙauna tana sa a yafe “tulin zunubai.” (1 Kor. 13:4, 5; karanta 1 Bitrus 4:8.) Hakan yana nufin cewa mutum mai ƙauna ba ya lissafin yawan laifin da aka yi masa. Sa’ad da manzo Bitrus ya tambayi yawan lokaci da ya kamata ya gafarta wa wani, Yesu ya ce: “Har bakwai bakwai so saba’in.” (Mat. 18:21, 22) Yesu yana nufin cewa Kirista ya riƙa gafarta wa mutane ba iyaka.—Mis. 10:12. *

13. Ta yaya za mu shawo kan halin ƙin gafarta wa mutane?

13 Annette ta ce: “Idan ma’aurata ba sa son su gafarta wa juna, ƙiyayya da kuma rashin yarda za su kasance a auren kuma hakan zai ɓata auren. Amma idan ma’aurata suna gafarta wa juna za su inganta aurensu kuma su kusaci juna.” Idan ma’aurata suna gode wa juna, hakan zai sa su riƙa gafarta wa juna. Saboda haka, ku riƙa yaba wa juna a kowane lokaci. (Kol. 3:15) Idan kuka yi hakan, za ku sami kwanciyar hankali da haɗin kai da kuma albarkar da Allah yake ba wa waɗanda suke gafarta wa mutane.—Rom. 14:19.

KU BI DA ABOKIN AURENKU YADDA ZA KU SO SU BI DA KU

14, 15. Wace shawara ce Yesu ya ce a bi, kuma yaya take taimakawa a aure?

14 Babu shakka, za ka so a bi da kai cikin ladabi da mutunci. Kana farin ciki sa’ad da wasu suka saurare ka kuma suka yi la’akari da ra’ayinka. Amma ka taɓa jin wani ya ce: “Bari zan yi maganinsa”? Ko da yake a wani lokaci mukan yi fushi, amma Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Kada ka ce, sai in yi masa kamar yadda ya yi mani.’ (Mis. 24:29) A maimakon haka, Yesu ya ba da shawara mai kyau game da magance matsaloli, ya ce: “Kamar yadda kuke so mutane su yi maku, ku yi masu hakanan kuma.” (Luk. 6:31) Yesu yana nufi cewa ya kamata mu bi da mutane yadda za mu so su bi da mu kuma kada mu rama mugunta da mugunta. Hakan yana nufin cewa mu bi da abokin aurenmu yadda muke so ya bi da mu.

15 Ma’aurata suna ƙarfafa dangantakarsu idan suka mai da hankali don su fahimci yanayin abokin aurensu. Wani maigida a Afirka ta Kudu ya ce: “Mun yi ƙoƙari mu bi da juna kamar yadda muke so a bi da mu. Hakika, akwai wasu lokatan da muke fushi, amma mun yi ƙoƙari mu bi da juna cikin ladabi da mutunci.”

16. Mene ne bai kamata ma’aurata su yi wa juna ba?

16 Bai kamata ku riƙa gaya wa mutane kasawar abokin aurenku ba, kuma bai dace ku riƙa gunaguni game da halayensa da ke ɓata muku rai ba. Aure ba gasar sanin wanda ya fi ƙarfi ko wanda ya iya ta da murya ko iya baƙar magana ba. Hakika, dukanmu mukan yi kuskure, kuma muna ɓata wa mutane rai a wani lokaci. Amma bai kamata ma’aurata su riƙa zagin juna, ko su yi riƙa wa juna baƙar magana ko su riƙa dukar juna ba.—Karanta Misalai 17:27; 31:26.

17. Ta yaya maigida zai bi da matarsa yadda yake so ta bi da shi?

17 Ko da yake a wasu wurare ana wa maza masu wulakanta ko kuma dūkan matansu kallon jarumai, Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Mai-jinkirin fushi ya fi masu-iko kyaun hali: Wanda ya mallaki ruhunsa kuma ya fi wanda ya ci birni.’ (Mis. 16:32) Mutum yana bukatar ƙarfin hali don ya kame kansa kamar yadda Yesu Kristi ya yi. Mutumin da yake wulaƙanta ko kuma dūkan matarsa ba jan namiji ba ne kuma zai ɓata dangantakarsa da Jehobah. Dauda marubucin zabura jarumi ne mai ƙarfin hali, ya ce: “Ku ji tsoro [yi fushi, NW], kada kuwa ku yi zunubi: ku yi shawara da zuciyarku a bisa shimfiɗarku, ku yi shuru.”—Zab. 4:4.

KU NUNA “ƘAUNA” A DUKAN AL’AMURANKU

18. Me ya sa yake da muhimmanci a ci gaba da nuna ƙauna?

18 Karanta 1 Korintiyawa 13:4-7. Ƙauna ta fi kome muhimmanci a aure. “Ku yafa zuciya ta tausai, nasiha, tawali’u, ladabi, jimrewa; gaba da dukan waɗannan kuma ku yafa ƙauna, gama ita ce magamin kamalta.” (Kol. 3:12, 14) Ƙauna irin ta Kristi za ta sa ma’aurata su kasance da dangantaka na kud da kud, kamar yadda kwaɓaɓɓiyar ƙasa take sa gini ya yi ƙwari sosai. Hakan zai sa auren ya dawwama duk da kurakurai ko ciwo mai tsanani ko rashin kuɗi da kuma matsaloli da suka shafi surukai.

19, 20. (a) Ta yaya ma’aurata za su inganta aurensu kuma su ji daɗi? (b) Mene ne za a tattauna a talifi na gaba?

19 Hakika, ma’aurata suna bukatar su nuna ƙauna da aminci kuma su yi iya ƙoƙarinsu don su inganta aurensu. Maimakon ma’aurata su yi watsi da aurensu sa’ad da suke fuskantar matsaloli, zai dace su yi iya ƙoƙarinsu don su ji daɗin zaman auren, ba wai kawai su riƙa zaman haƙuri ba. Idan ma’aurata suna ƙaunar Jehobah kuma suna son juna, za su so su sasanta matsalolinsu kome yawansu, don “ƙauna ba ta ƙarewa.”—1 Kor. 13:8; Mat. 19:5, 6; Ibran. 13:4.

20 A wannan “miyagun zamanu,” ma’aurata suna bukata su yi aiki tuƙuru idan suna son su inganta aurensu kuma su ji daɗi. (2 Tim. 3:1) Da taimakon Jehobah, za su yi nasara. Har ila, ma’aurata za su yi fama a wannan duniyar da ake ɗaukaka ɗabi’un banza. Talifi na gaba zai nuna abin da ma’aurata za su yi don su kāre aurensu.

^ sakin layi na 12 Ya dace ma’aurata su riƙa gafarta wa juna kuma su riƙa yin sulhu, amma idan ɗaya daga cikinsu ya yi zina, marar laifin zai iya tsai da shawara ko zai gafarci wanda ya yi zinan ko kuma ya kashe auren bisa ga shawarar Littafi Mai Tsarki. (Mat. 19:9) Ka duba rataye nan “Ra’ayin Littafi Mai Tsarki Game da Kisan Aure da Kuma Rabuwa” da ke shafi na 219-221 a cikin littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah.”