TARIHI
Albarkun da Muka Samu da Kuma Darussan da Muka Koya a Hidimarmu ga Jehobah
DA NAKE yaro, a duk lokacin da na ga jirgin sama, sai in ji kamar in shiga jirgin in je wata ƙasa. Amma a ganina, hakan ba zai taɓa faruwa ba.
Iyayena sun bar Estoniya saꞌad da ake Yaƙin Duniya na Biyu kuma suka koma Jamus. A wurin ne aka haife ni. Bayan sun haife ni, sai suka soma shirin ƙaura zuwa Kanada. Gidan da muka fara zama yana kusa da Ottawa, babban birnin Kanada. Ƙaramin gida ne kuma ana kiwon kaji a wurin. Mu talakawa ne sosai amma mukan ci kwai da safe.
Wata rana, Shaidun Jehobah sun karanta wa mahaifiyata Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:3, 4. Abin da suka karanta ya sa ta farin ciki sosai da har ta soma hawaye. Mahaifina da mahaifiyata sun ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki kuma suka yi baftisma cikin ƙanƙanin lokaci.
Iyayena ba su iya Turanci sosai ba, amma suna da ƙwazo na bauta wa Jehobah. Duk da cewa babana yakan kwana yana aiki a wani kamfani da ke sarrafa wani ƙarfe da ake kira nickel a garin Sudbury da ke Ontario, kusan kowace ranar Asabar, yakan fita waꞌazi tare da ni da ƙanwata mai suna Sylvia. Kuma kowane mako, dukanmu a iyalin muna nazarin Hasumiyar Tsaro tare. Iyayena sun taimaka mini in ƙaunci Jehobah sosai. Da nake shekara goma, na yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma na yi baftisma a 1956. Idan na tuna da yadda suke ƙaunar Jehobah, abin yakan ƙarfafa ni in ci gaba da bauta masa.
Bayan na gama makaranta, sai na daina bauta wa Jehobah yadda ya kamata. Na ɗauka cewa idan na zama majagaba, ban zan taɓa samun isashen kuɗin da zan iya cim ma burina na zuwa ƙasashe ta jirgin sama ba. Na samu aikin saka waƙa, wato DJ a wani gidan rediyo, kuma na so aikin sosai. Amma da yamma ne nake zuwa aikin, don haka ba na halarta taro a-kai-a-kai, kuma na soma tarayya da waɗanda ba sa ƙaunar Jehobah. Daga baya, zuciyata ta soma damu na kuma hakan ya sa na canja rayuwata.
Sai na ƙaura zuwa garin Oshawa da ke Ontario. A wurin, na haɗu da Ɗanꞌuwa Ray Norman, da ƙanwarsa Lesli da wasu majagaba. Sun ƙaunace ni sosai. Da na ga yadda suke farin ciki, sai na soma tunani a kan abin da nake so in yi da rayuwata. Sun ƙarfafa ni in soma hidimar majagaba, kuma na soma a watan Satumba, 1966. Hidimar ta sa ni farin ciki kuma ta sa na ji daɗin rayuwata. A lokacin, ban san cewa akwai wasu abubuwa da za su faru da za su canja rayuwata ba.
IDAN JEHOBAH YA CE KA YI WANI ABU, KA YI ƘOƘARI KA YI SHI
Da nake makaranta, na cika fom ɗin yin hidima a Bethel da ke birnin Toronto a Kanada. Yayin da nake
hidimar majagaba, an ce in zo in yi hidima a Bethel na shekara huɗu. Amma a lokacin, son Lesli ya riga ya shiga zuciyata. Don haka na ji tsoro cewa idan na je Bethel, ba zan ƙara ganin ta ba. Bayan na yi adduꞌa sosai game da batun, sai na amince da hidimar kuma na yi bakwana da Lesli, duk da cewa ban so mu rabu ba.A Bethel, na yi aiki a inda ake wanki da guga. Daga baya, sai na yi aikin sakatare. Lesli kuma ta zama majagaba na musamman a birnin Gatineau, a Quebec. Nakan yi tunani game da ita sosai. A wani lokaci ma, nakan yi shakka ko shawarar da na yanke ta dace. Ana nan sai wani abin ban mamaki ya faru. An gayyaci Ray, ɗanꞌuwan Lesli zuwa Bethel kuma ya zama abokin ɗakina. Abin ya burge ni ba kaɗan ba. Ta wurinsa ne na sake soma abokantaka da Lesli. Mun yi aure a ranar 27 ga Fabrairu 1971. A ranar ce na kammala hidimata a Bethel bayan na yi shekara huɗu a wajen.
An tura ni da Lesli mu yi hidima a wata ikilisiya da ake Farasanci a Quebec. Bayan ꞌyan shekaru, an naɗa ni mai kula da daꞌira. Na yi mamaki, domin shekaruna 28 ne kawai a lokacin. A ganina, ni matashi ne kuma ban cancanci in zama mai kula da daꞌira ba. Amma abin da ke Irmiya 1:7, 8 ya ƙarfafa ni. Ƙari ga haka, Lesli ta yi hatsarin mota sau da yawa kuma ba ta iya yin barci da kyau. Saboda haka, mun zata ba za mu iya yin aikin mai kula da daꞌira ba. Amma Lesli ta ce min, “Idan Jehobah ya ce mu yi wani abu, ba ka ganin ya kamata mu yi ƙoƙarin yin sa?” Sai muka amince da hidimar, kuma mun ji daɗin ta har na shekaru 17.
Da na zama mai kula da daꞌira, ayyuka sun yi min yawa har ba na yawan samun lokacin kasancewa da Lesli. Hakan ya sa na koyi wani darasi. Wata rana da sassafe, an ƙwaƙwasa ƙofarmu. Da na fito, ban ga kowa ba, kwando kawai na gani. A cikin kwandon akwai ƙyale, da ꞌyaꞌyan itatuwa, da abinci, da ruwan inabi, da kofi, da kuma takardar da aka rubuta cewa: “Ka ɗauki matarka ku je ku ɗan shakata.” A lokacin, yanayin yana da kyau don rana tana haskawa. Na gaya wa Lesli cewa ina da jawaban da nake so na shirya. Don haka, ba zan iya fita ba. Ta fahimce ni amma ba ta ji daɗi ba. Da na zauna, sai zuciyata ta soma damu na. Na tuna da Afisawa 5:25, 28. Ina ganin Jehobah ya yi amfani da ayoyin nan don ya tuna mini yadda ya kamata in kula da matata. Bayan na yi adduꞌa, sai na ce wa Lesli: “Mu je mu shakata.” Ta ji daɗi sosai! Mun je wani wuri mai kyau kusa da rafi, muka yi shimfiɗa kuma muka shakata abinmu. Wannan yana cikin ranakun da muka fi jin daɗin kasancewa tare. Kuma duk da haka, na samu lokacin shirya jawabaina.
Mun ji daɗin yin hidimar mai kula da daꞌira sosai kuma mun je wurare da dama a Kanada, daga can gabashin ƙasar zuwa yammacin ƙasar. Dā ma tun ina yaro, na so yin tafiye-tafiye. Yanzu abin nema ya samu. Na taɓa yin tunanin zuwa makarantar Gilead, amma ba na so a tura ni wata ƙasa. Ban da haka, ina ganin cewa masu waꞌazi a ƙasashen waje mutane ne
na musamman kuma ni ban cancanci wannan hidimar ba. Ƙari ga haka, ina tsoron kar a tura ni wata ƙasa a Afirka, inda akwai cututtuka kuma ana yaƙe-yaƙe. Ba na son in bar Kanada domin ina jin daɗin hidimata a wurin.AN GAYYACE MU ZUWA ESTONIYA DA YANKIN BALTIC BA ZATO
A shekara ta 1992, Shaidun Jehobah sun sami damar sake yin waꞌazi a wasu ƙasashen da ke tarayyar Soviet. Don haka, an tambaye mu ko za mu je ƙasar Estoniya mu zama masu waꞌazi a ƙasashen waje. Abin ya ba mu mamaki sosai, amma mun yi adduꞌa game da batun. A wannan karon ma, mun tambayi kanmu cewa: ‘Idan Jehobah ya ce mu yi wani abu, ba zai dace mu yi ƙoƙarin yin sa ba?’ Sai muka yarda kuma na ce wa kaina: ‘Tun da ba Afirka za mu ba, ai ba laifi.’
Nan da nan sai muka soma koyan yaren Estoniya. Bayan mun yi ꞌyan watanni a ƙasar, sai aka ce mu soma hidimar mai kula da daꞌira. Za mu ziyarci ikilisiyoyi wajen 46 da wasu rukunoni a Estoniya da Latvia da Lisuwaniya da kuma birnin Kaliningrad da ke Rasha. Hakan yana nufin cewa za mu yi ƙoƙari mu koyi yaren Latvia da Lisuwaniya da kuma Rasha. Abin bai da sauƙi, amma ꞌyanꞌuwan sun yi farin ciki cewa muna ƙoƙarin koyan yarensu, kuma sun taimaka mana. A 1999, an kafa reshen ofishinmu a Estoniya. An naɗa ni in zama Memban Kwamitin da ke Kula da Ofishinmu na Estoniya tare da wasu ꞌyanꞌuwa. A cikinsu akwai Ɗanꞌuwa Toomas Edur, da Lembit Reile, da kuma Tommi Kauko.
Hidimarmu ta sa mun san ꞌyanꞌuwa da yawa da aka saka a kurkuku a Saberiya. ꞌYanꞌuwan nan sun sha wahala sosai a kurkuku kuma an raba su da iyalansu. Amma da suka dawo, ba su riƙa yin fushi ko baƙin ciki ba. Sun ci gaba da farin ciki, da yin ƙwazo a hidimarsu. Misalinsu ya nuna mana cewa, za mu iya yin farin ciki kuma mu jimre yanayi mai wuya da muke fama da shi.
Mun yi shekaru da yawa muna aiki sosai, kuma ba ma samun lokacin hutawa. Ana nan, sai Lesli ta soma fama da gajiya. Ba mu san cewa tana fama da wata cuta da ake kira fibromyalgia ba. Ashe cutar ce take jawo mata yawan gajiya. Hakan ya sa mun soma tunanin barin hidimar don mu koma Kanada. Da aka gayyace mu zuwa Makaranta a Patterson da ke a Amirka, don a ƙara horar da mu, na ɗauka cewa ba za mu iya zuwa ba. Amma mun yi adduꞌa sosai, sai muka yarda mu je kuma Jehobah ya yi mana albarka. Domin da muke makarantar ne Lesli ta samu jinyar da take bukata. Daga baya, Lesli ta warke kuma muka soma hidimarmu yadda muka saba.
AN TURA MU WATA NAHIYA DABAM BABU ZATO
A shekara ta 2008, saꞌad da muke hidima a Estoniya, an kira ni daga hedkwatarmu kuma aka ce ko za mu so mu je hidima a Kwango. Abin ya ba ni mamaki sosai musamman ma da suka ce in ba su amsa washegari. Da farko, ban gaya wa Lesli ba domin na san cewa in ta ji, ba za ta iya yin barci ba. Ni ne na kwana ina adduꞌa don ina tsoron zuwa Afirka.
Washegari, na gaya wa Lesli, kuma muka ce wa kanmu: “Jehobah yana so mu je Afirka. Idan ba mu gwada ba, ta yaya za mu san cewa ba za mu ji daɗin sa ba?” Bayan mun yi shekaru 16 a Estoniya, sai muka shiga jirgi zuwa Kinshasa da ke Kwango. Ofishinmu da ke Kwango yana da lambu mai kyau sosai. Koꞌina shuru, kallon wurin ma kawai yana kwantar wa mutum hankali. Ɗaya daga cikin abubuwa na farko da Lesli ta saka a ɗakinmu shi ne, wata takarda da aka ba mu tun lokacin da za mu bar Kanada. A takardar, an rubuta cewa: “Ku yi farin ciki a duk inda kuke hidima.” Da muka haɗu da ꞌyanꞌuwa, muka soma nazari da mutane kuma muka ga yadda hidima a ƙasar waje take da daɗi, hakan ya sa mun ƙara farin ciki. Mun sami damar zuwa ofisoshinmu guda 13 a wasu ƙasashen Afirka. Hakan ya sa mun iya haɗuwa da mutane dabam-dabam. Tsoron da na ji game da Afirka ya ɓace kuma mun gode wa Jehobah da ya turo mu nan.
A Kwango, an ba mu abinci iri-iri har da kwari, abin da ban taɓa tsammanin zan iya ci ba. Amma da muka ga ꞌyanꞌuwanmu suna jin daɗin cin abubuwan nan, sai mu ma muka gwada ci kuma mun ji daɗin sa.
Mun yi tafiya zuwa gabashin ƙasar don mu taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu kuma mu ba su abubuwan da suke bukata. A wurin, akwai ꞌyan taꞌadda da suke kai wa mata da yara hari. Yawancin ꞌyanꞌuwan talakawa ne. Duk da haka, sun gaskata da tashin matattu, suna ƙaunar Jehobah kuma sun manne wa ƙungiyarsa. Ganin hakan ya ƙarfafa mu sosai. Ya sa mu tunani a kan dalilin da ya sa muke bauta wa Jehobah, kuma mun ƙara gaskata da shi. Wasu daga cikin ꞌyanꞌuwan sun rasa gidajensu da gonakinsu. Hakan ya tuna min cewa za mu iya rasa dukiyarmu a kowane lokaci. Amma dangantakarmu da Jehobah ce ta fi muhimmanci. Duk da wahalar nan, ꞌyanꞌuwan ba su yi guna-guni ba. Halinsu ya ƙarfafa mu mu kasance da ƙarfin zuciya, kuma mu jimre namu matsalolin.
MUN SAMU WATA SABUWAR HIDIMA A ASIYA
Ana nan, sai wani abin ban mamaki ya faru. An gaya mana mu koma yin hidima a ofishinmu da ke Hong Kong. Ba mu taɓa tunanin cewa za mu je Asiya ba. Mun amince da wannan hidimar domin mun
riga mun ga yadda Jehobah ya taimaka mana a sauran hidimomi da muka yi. A 2013, mun zub da hawaye saꞌad da za mu bar Afirka da ꞌyanꞌuwanmu. Ga shi ba mu san abin da ke jiran mu a gaba ba.Zama a Hong Kong bai yi sauƙi ba, domin babban birni ne da ke cike da mutane daga ƙasashe dabam-dabam a duniya. Koyan yaren China ya yi mana wuya, amma ꞌyanꞌuwan sun marabce mu sosai kuma mun ji daɗin abincinsu. Ana samun ci gaba sosai, don haka da bukatar a faɗaɗa ofishin, amma kuɗin gida da fili sai ƙaruwa yake yi. Saboda haka, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta sayar da yawancin gine-ginenmu da ke wurin kuma ta ƙaurar da wasu sassan ofishin. Jim kaɗan bayan haka, a 2015, an ƙaurar da mu zuwa Koriya ta Kudu, inda muka ci gaba da hidima. A wurin ma, muna bukatar mu koyi yaren. Ko da yake ba mu iya yaren da kyau ba, ꞌyanꞌuwan sun ƙarfafa mu kuma sun gaya mana cewa muna ƙoƙari.
DARUSSAN DA MUKA KOYA
Samun sabbin abokai bai da sauƙi. Amma mun gano cewa idan ka gayyaci mutane zuwa gidanka, hakan zai sa ka yi saurin sabawa da su. Mun kuma gano cewa ko da yake mun fito daga wurare dabam-dabam, akwai alaƙa a tsakaninmu. Kuma Jehobah ya halicce mu yadda za mu iya nuna wa mutane da yawa ƙauna.—2 Kor. 6:11.
Mun ga muhimmancin ɗaukan mutane yadda Jehobah yake ɗaukan su, da kuma yin ƙoƙarin ganin yadda Jehobah yake mana ja-goranci da nuna mana ƙauna. A duk lokacin da muke baƙin ciki, ko muna shakka ko ꞌyanꞌuwanmu suna ƙaunar mu da gaske, mukan karanta kati ko wasiƙu masu ban ƙarfafa da ꞌyanꞌuwa suka tura mana. Mun ga yadda Jehobah ya amsa adduꞌoꞌinmu da yadda ya nuna mana ƙauna, kuma ya ba mu ƙarfin jimrewa.
A cikin shekarun nan, ni da Lesli mun koyi cewa, komin yawan ayyukan da muke yi, yana da muhimmanci mu nemi lokacin kasancewa tare. Mun kuma ga cewa ba laifi ba ne idan muka yi wa kanmu dariya saꞌad da muka yi kuskure, musamman ma saꞌad da muke koyan sabon yare. Abu ne ma da ya kamata mu riƙa yi. Ƙari ga haka, kowace dare mukan yi tunanin abubuwan da muka more a ranar kuma mu gode wa Jehobah.
A gaskiya, ban taɓa tsammanin zan zama mai waꞌazi a ƙasashen waje, ko in je in zauna a wata ƙasa ba. Amma yanzu na ga cewa kome mai yiwuwa ne da taimakon Jehobah. Kuma hakan ya sa ni farin ciki. Na tuna abin da annabi Irmiya ya ce: “Ya Yahweh, ka ruɗe ni.” (Irm. 20:7) Ya yi mana albarkun da ba mu taɓa zata ba har da cika burina na yin tafiya ta jirgin sama. Mun je ƙasashen da ban taɓa tsammanin zan je ba saꞌad da nake yaro, kuma mun ziyarci ofisoshinmu a nahiyoyi biyar. Ƙari ga haka, ina godiya sosai don yadda Lesli ta taimaka mini a duka hidimomin nan da na yi.
A koyaushe, mukan tuna wa kanmu cewa muna yin abubuwa ne domin muna ƙaunar Jehobah. Abubuwan da muka more sun nuna mana yadda rayuwa za ta yi daɗi a aljanna, saꞌad da Jehobah zai “bayar hannu sake” kuma ya “ƙosar da kowane mai rai bisa ga bukatarsa.”—Zab. 145:16.