TALIFIN NAZARI NA 31
“Ku Tsaya Daram, Ku Kafu”
“ꞌYanꞌuwana waɗanda nake ƙauna, ku tsaya daram, ku kafu.”—1 KOR. 15:58.
WAƘA TA 122 Mu Tsaya Daram, Babu Tsoro!
ABIN DA ZA A TATTAUNA a
1-2. Me ya sa za mu iya cewa Kirista yana kama da gini mai tsayi sosai? (1 Korintiyawa 15:58)
A SHEKARA ta 1978, an yi wani gini mai tsawo da ya kai hawa 60 a birnin Tokyo da ke Jafan. Mutane sun yi mamaki da suka ga ginin don akan yi girgizar ƙasa sosai a birnin. Suna ganin ginin ba zai kai labari ba. Me ya taimaka wa ginin? Maginan sun gina shi yadda zai yi ƙarfi sosai, kuma sun yi shi da ɗan danƙo. Zai iya tanƙwarewa kaɗan saꞌan nan ya miƙe, amma ba zai rushe ba. Kiristoci kamar wannan gini mai tsayi suke. Me ya sa muka ce haka?
2 Kamar yadda ginin yake da ƙarfi, haka ma ya kamata Kirista ya tsaya daram. Bai kamata ya bar kome ya hana shi bin dokokin Jehobah da kuma ƙaꞌidodinsa ba. Amma kuma, kamar yadda ginin yake iya tanƙwarewa, haka ma ya kamata Kirista ya zama mai sanin yakamata. (Karanta 1 Korintiyawa 15:58.) Ya zama mai “sauƙin kai,” wato mai saurin yin biyayya a koyaushe. Amma har ila, zai dace ya zama mai “hankali,” wato mai sanin yakamata, idan zai yiwu ko kuma idan da bukata. (Yak. 3:17) Idan Kirista ya iya daidaita tunaninsa tsakanin abubuwa biyun nan, ba zai zama mai nacewa a kan raꞌayinsa kawai ba, kuma ba zai zama mai halin ko-in-kula ba. A talifin nan, za mu ga yadda ya kamata mu tsaya daram. Za mu kuma tattauna abubuwa biyar da Shaiɗan yake amfani da su don ya sa mu sanyin gwiwa da yadda za mu yi tsayayya da shi.
ME ZA MU YI DON MU TSAYA DARAM?
3. Waɗanne dokoki ne Allahnmu wanda ya fi kowa ikon kafa doka ya ba mu a Ayyukan Manzanni 15:28, 29?
3 Jehobah yana da ikon kafa dokoki fiye da kowa kuma yakan bayyana su yadda kowa zai fahimta. (Isha. 33:22) Misali, a zamanin Kiristoci na farko, hukumar da ke kula da ayyukansu ta ambaci fannoni uku da ya zama dole Kiristoci su tsaya daram: (1) kada su bauta wa gumaka, su bauta wa Jehobah shi kaɗai, (2) su bi dokar Jehobah game da rai da jini, (3) su guji yin lalata, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce. (Karanta Ayyukan Manzanni 15:28, 29.) Ta yaya Kiristoci a yau za su tsaya daram kuma su yi abubuwa ukun nan?
4. Ta yaya za mu nuna cewa Jehobah ne kaɗai muke bauta wa? (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11)
4 Kada mu bauta wa gumaka, mu bauta wa Jehobah kaɗai. Jehobah ya dokaci Israꞌilawa cewa shi kaɗai za su yi wa sujada. (M. Sha. 5:6-10) Kuma da Shaiɗan ya jarabci Yesu, Yesu ya ce Jehobah ne kaɗai ya kamata mu bauta wa. (Mat. 4:8-10) Don haka, ba ma bauta wa gumaka. Ƙari ga haka, bai kamata mu bauta wa mutane ba. Misali, bai kamata mu riƙa daraja shugabannin addinai ko na gwamnati ko shahararru a fannin wasannin nishaɗi har ya zama kamar muna bauta musu ba. Maimakon haka, Jehobah ne kaɗai za mu bauta wa don shi ne ya “halicci kome da kome.”—Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11.
5. Me ya sa ba ma wasa da bin dokar Jehobah game da rai da kuma jini?
5 Mu bi dokar Jehobah game da rai da jini. Me ya sa bai kamata mu yi wasa da jini ba? Domin Jehobah ya ce jini yana wakiltar rai, wanda kyauta ne mai daraja da ya ba mu. (L. Fir. 17:14) Da Jehobah ya ba wa mutane izini su ci dabbobi, ya ce kada su ci jinin. (Far. 9:4) Ya sa an ambata hakan a dokar da ya ba wa Israꞌilawa ta hannun Musa. (L. Fir. 17:10) Ya kuma umurci hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a ƙarni na farko su gaya wa dukan Kiristoci su ‘kiyaye kansu daga . . . jini.’ (A. M. 15:28, 29) Muna bin wannan dokar sosai idan muna zaɓan irin jinyar da za a yi mana. b
6. Me za mu yi don mu iya bin dokar Jehobah game da yin lalata?
6 Mu guji yin lalata, kamar yadda Jehobah ya umurta. (Ibran. 13:4) Manzo Bulus ya shawarce mu cewa mu “kashe halin shaꞌawace-shaꞌawacen duniya,” wato mu yi duk wani abin da ya kamata don mu guji halaye marasa kyau. Don haka, za mu guji kallo ko kuma yin duk wani abin da zai kai ga yin lalata. (Kol. 3:5; Ayu. 31:1) Idan aka jarabe mu, nan da nan ya kamata mu ƙi yin abin da zai ɓata dangantakarmu da Jehobah, kada ma mu yi tunaninsa.
7. Me ya kamata ya zama ƙudurinmu kuma me ya sa?
7 Jehobah yana so mu riƙa yin biyayya da ‘dukan zuciyarmu.’ (Rom. 6:17) Abin da yake gaya mana don amfanin kanmu ne kuma ba za mu iya canja dokokinsa ba. (Isha. 48:17, 18; 1 Kor. 6:9, 10) Don haka, mu yi iya ƙoƙarinmu mu faranta masa rai, kuma mu zama kamar marubucin Zabura da ya ce: “Na miƙa zuciyata ga bin ƙaꞌidodinka . . . har abada.” (Zab. 119:112) Amma Shaiɗan zai yi iya ƙoƙarinsa ya ga cewa mun ƙasa yin hakan. Waɗanne abubuwa ne Shaiɗan yake amfani da su?
ME SHAIƊAN YAKE YI DON YA SA MU SANYIN GWIWA?
8. Ta yaya Shaiɗan yake amfani da tsanantawa don ya sa mu yi sanyin gwiwa?
8 Tsanantawa. Shaiɗan yakan sa a ci zalinmu ko kuma a matsa mana. Burinsa shi ne ya “cinye” mu, wato ya ɓata dangantakarmu da Jehobah. (1 Bit. 5:8) An yi wa Kiristoci a ƙarni na farko barazana, an yi musu dūka har ma an kashe wasu domin sun nace a kan bangaskiyarsu. (A. M. 5:27, 28, 40; 7:54-60) A yau ma, Shaiɗan yana amfani da tsanantawa. Shi ya sa maƙiya suke cin zalin ꞌyanꞌuwanmu a Rasha da ma wasu ƙasashe. Ban da haka ma, a duk duniya, maƙiyanmu suna tsananta wa ꞌyanꞌuwanmu a hanyoyi dabam-dabam.
9. Ka ba da misalin da ya nuna cewa Shaiɗan yana amfani da rinjaya da wayo.
9 Rinjaya da wayo. Ban da tsanantawa, Shaiɗan yana amfani da “dabaru.” (Afis. 6:11) Alal misali, akwai wani ɗanꞌuwa mai suna Bob da aka kwantar da shi a asibiti don a yi masa tiyata. Ya gaya wa likitan da zai yi tiyatar cewa, ko da me zai faru, ba zai amince a yi masa ƙarin jini ba, kuma likitan ya yarda. Amma da dare kafin ranar da za a yi masa tiyatar, sai wani likita ya zo ya sami Ɗanꞌuwa Bob bayan ꞌyan iyalinsa sun koma gida. Ya ce masa mai yiwuwa ba za a sa masa jini ba, amma za a samo jini a ajiye kusa don a yi amfani da shi idan bukata ta taso. Da alama, likitan ya zata Bob zai canja raꞌayinsa idan ꞌyan iyalinsa ba sa nan. Amma Ɗanꞌuwa Bob ya tsaya a kan bakansa. Ya ce ko da me zai faru, kada a sa masa jini.
10. Me ya sa bin raꞌayin mutane yake da haɗari sosai? (1 Korintiyawa 3:19, 20)
10 Raꞌayin mutane. Idan muka bi raꞌayin mutane, hakan zai iya sa mu yi banza da umurnin Jehobah. (Karanta 1 Korintiyawa 3:19, 20.) A yawancin lokuta, “hikimar wannan duniya” takan zuga mutane su ƙi bin umurnin Jehobah. Wasu Kiristoci a ikilisiyar Birgamum da Tiyatira sun bi raꞌayin mutanen birninsu game da lalata da kuma bautar gumaka. Yesu ya ja musu kunne sosai don yadda suke ƙyale halin lalata a ikilisiyarsu. (R. Yar. 2:14, 20) A yau ma, ana matsa mana mu bi raꞌayoyi marasa kyau. ꞌYan iyalinmu ko kuma abokanmu za su iya ce mana yadda muke bin dokokin Jehobah ya wuce gona da iri. Misali, za su iya cewa yin abin da zuciyarka take so ba laifi ba ne, kuma abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da lalata tsohon yayi ne.
11. Yayin da muke ƙoƙari mu tsaya daram, wane hali ne ya kamata mu guje wa?
11 Wani lokaci za mu iya yin tunanin cewa, umurnin da Jehobah ya ba mu bai isa ba. Ƙila ma mu ji kamar gwamma mu “wuce abin da aka rubuta.” (1 Kor. 4:6) Zunubin da shugabannin addini a zamanin Yesu suka yi ke nan. Sun yi ta ƙara nasu raꞌayi a kan dokar da Jehobah ya bayar, kuma hakan ya sa ya yi wa mutane wuya su bi. (Mat. 23:4) A yau, Jehobah yakan gaya mana abin da yake so mu yi dalla-dalla, ta wurin Kalmarsa da kuma ƙungiyarsa. Bai kamata mu ƙara gishiri a kan umurninsa ba, ko kaɗan. (K. Mag. 3:5-7) Don haka, ba za mu wuce abin da aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki ba, ko mu kafa ma ꞌyanꞌuwa dokoki a kan abin da Jehobah bai ce ba.
12. Ta yaya Shaiɗan yake amfani da “yaudarar wofi”?
12 Yaudara. Shaiɗan yana amfani da “yaudarar wofi” da kuma “alꞌadun duniyar nan” don ya ruɗi mutane kuma ya raba kansu. (Kol. 2:8, Mai Makamantu[n] Ayoyi) A ƙarni na farko, waɗannan alꞌadun sun haɗa da ilimin duniya da ke bisa ga raꞌayin mutane da kuma koyarwar mutane da ba sa cikin Littafi Mai Tsarki. Da raꞌayin nan cewa dole ne Kiristoci su bi dokar Musa. Dukan abubuwan nan yaudara ne domin sun ɗauke hankalin mutane, sun hana su mai da hankali ga Jehobah, wanda shi ne Tushen hikima ta gaske. A yau, Shaiɗan yana amfani da kafofin yaɗa labarai da na sada zumunta don ya yaɗa jita-jita da kuma labaran ƙarya da shugabannin gwamnati suke ƙullawa. An yi ta yaɗa irin waɗannan jita-jitan da ƙararrayi sosai a lokacin annobar korona. c Amma waɗanda suka bi ja-gorancin ƙungiyarmu ba su yi fama da yawan damuwa kamar waɗanda suka saurari ƙararrayin ba.—Mat. 24:45.
13. Me ya sa yake da muhimmanci kada mu bari a raba hankalinmu?
13 Abubuwan raba hankali. Ya kamata mu ci gaba da mai da hankali ga “abin da ya fi kyau.” (Filib. 1:9, 10) Amma abubuwan raba hankali za su iya cinye lokacinmu kuma su ɗauke hankalinmu daga abubuwan da suka fi muhimmanci. Abubuwa kamar ci da sha, da yin nishaɗi, da kuma aiki za su iya raba hankalinmu idan muka sa su farko a rayuwarmu. (Luk. 21:34, 35) Ban da haka ma, kowace rana ana cika mu da labaran rikice-rikicen da ake yi da kuma harkokin siyasa. Kada mu bar abubuwan nan su raba hankalinmu. In ba haka ba, za mu soma goyon bayan wani ɓangare a cikin zuciyarmu. Shaiɗan yana amfani da abubuwan da muka ambata don ya sa mu sanyin gwiwa kuma mu kasa yin abin da ya dace. Yanzu bari mu bincika abin da za mu yi don mu yi tsayayya da shi kuma mu ci gaba da tsayawa daram.
ABUBUWAN DA ZA SU TAIMAKA MANA MU TSAYA DARAM
14. Wane abu ne zai iya taimaka mana mu ci gaba da bin Jehobah?
14 Ka tuna alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma da ka yi. Kana so ka ci gaba da bin Jehobah, shi ya sa ka ɗauki waɗannan matakan. Don haka, ka tuna abin da ya tabbatar maka cewa wannan ita ce hanyar gaskiya. Da ka koyi gaskiya game da Jehobah, hakan ya sa ka soma daraja shi kuma ka ƙaunace shi a matsayin Ubanka na sama. Ka ba da gaskiya kuma hakan ya sa ka tuba. Ka daina yin abubuwan da Jehobah ba ya so kuma ka soma yin abin da zai faranta masa rai. Da ka ga cewa Allah ya yafe maka zunubanka, ka ji daɗi sosai. (Zab. 32:1, 2) Ka soma zuwa taro, da gaya wa mutane abubuwa masu kyau da ka koya. Yanzu ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma. Kana bin hanyar da za ta kai ga samun rai kuma ka ƙudura cewa ba za ka bar ta ba.—Mat. 7:13, 14.
15. Me ya sa yin nazari da yin tunani mai zurfi a kan abin da muke karantawa yake da muhimmanci?
15 Ka dinga nazarin Kalmar Allah da kuma tunani mai zurfi a kai. Idan bishiya tana da jijiyoyin da suka shiga can cikin ƙasa, ba za ta faɗi ba. Haka ma, idan muna da bangaskiya sosai, za mu tsaya daram. Idan bishiya tana girma, jijiyoyinta ma sukan ƙara shiga ƙasa kuma su yaɗu. Haka ma idan muna nazari da yin tunani mai zurfi, bangaskiyarmu za ta ƙaru kuma za mu ƙara zama da tabbaci cewa bin umurnin Jehobah ne ya fi kyau. (Kol. 2:6, 7) Ka yi tunani a kan yadda bayin Jehobah suka amfana daga umurnan Jehobah da shawararsa da kuma kāriyarsa. Alal misali, Ezekiyel ya natsu sosai yana lura da yadda malaꞌika ya yi ta gwada wurare da dama a haikalin da aka nuna masa a wahayi. Wannan wahayin ya ƙarfafa Ezekiyel kuma ya koya mana darussa masu kyau game da yadda za mu bauta wa Jehobah a hanyar da yake so. d (Ezek. 40:1-4; 43:10-12) Mu ma idan muka natsu, muka yi nazari, kuma muka yi tunani mai zurfi a kan koyarwar Littafi Mai Tsarki masu wuyar fahimta, za mu amfana sosai.
16. Ta yaya Ɗanꞌuwa Bob ya amfana don zuciyarsa ta kafu? (Zabura 112:7)
16 Ka sa zuciyarka ta kafu. Sarki Dauda ya nuna cewa ba zai taɓa daina ƙaunar Jehobah ba. Ya ce: “Zuciyata ta kafu daram, ya Allah.” (Zab. 57:7) Mu ma za mu iya sa zuciyarmu ta kafu daram ta wajen dogara ga Jehobah da dukan zuciyarmu. (Karanta Zabura 112:7.) Abin da ya taimaka wa Ɗanꞌuwa Bob da muka ambata ɗazu ke nan. Da aka ce masa za a ajiye jini kusa domin a yi amfani da shi idan bukata ta taso, nan take ya gaya musu cewa idan har akwai abin da zai sa su sa masa jini, zai bar asibitin ba tare da ɓata lokaci ba. Daga baya, Ɗanꞌuwa Bob ya ce: “Ban yi shakkar matakin da na ɗauka ba, kuma ban damu da abin da zai iya faruwa ba.”
17. Mene ne labarin Bob ya koya mana? (Ka kuma duba hoton.)
17 Me ya taimaka wa Ɗanꞌuwa Bob ya kasance da irin wannan ƙarfin zuciyar? Ya riga ya tsai da shawara cewa zai tsaya daram tun kafin ya je asibitin. Ta yaya? Na ɗaya, ya yi niyyar yin abin da zai faranta wa Jehobah rai. Na biyu, ya natsu ya yi nazarin abin da Littafi Mai Tsarki da littattafanmu suka ce game da rai da kuma jini. Na uku, yana da tabbaci cewa idan ya bi abin da Jehobah ya ce, Jehobah zai ba shi lada. Mu ma ko da wace irin matsala ce muka fuskanta, za mu iya sa zuciyarmu ta kafu.
18. Ta yaya labarin Barak ya koya mana muhimmancin dogara ga Jehobah? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)
18 Ka dogara ga Jehobah. Barak ya yi nasara sosai domin ya bi umurnin Jehobah. Duk da cewa a duk faɗin ƙasar, babu garkuwa ko mashi, Jehobah ya ce ya je ya yaƙi sojojin Kanꞌana da suke ƙarƙashin ja-gorancin Sisera. Sojojin Sisera kuwa suna da kayan yaƙi sosai. (Alƙa. 5:8) Annabiya Deborah ta ce wa Barak ya gangara zuwa filin da Sisera yake. Sisera yana tare da karusansa guda 900. A filin, zai yi wa Israꞌilawa wuya su yaƙi mutanen da ke karusan, domin karusan suna gudu sosai. Barak ya san da hakan, amma ya yi biyayya. Da Israꞌilawan suke gangarawa daga Tudun Tabor, sai Jehobah ya sa aka yi ruwan sama sosai. Hakan ya sa karusan suka maƙale a taɓo, kuma Jehobah ya sa Barak ya ci yaƙin. (Alƙa. 4:1-7, 10, 13-16) Mu ma Jehobah zai sa mu yi nasara idan muka dogara gare shi kuma muka bi umurnin da yake ba mu ta ƙungiyarsa.—M. Sha. 31:6.
KA ƘUDIRI NIYYAR TSAYAWA DARAM
19. Me ya sa kake so ka ci gaba da tsayawa daram?
19 Muddin muna kwanakin ƙarshe, dole ne mu ci gaba da yin ƙoƙari don mu tsaya daram. (1 Tim. 6:11, 12; 2 Bit. 3:17) Bari mu ƙudura cewa ba za mu bar tsanantawa ko dabarun Shaiɗan ko raꞌayin mutane ko yaudara ko kuma abubuwan raba hankali su hana mu yin biyayya ga Jehobah ba. (Afis. 4:14) A maimakon haka, mu tsaya daram, mu ci gaba da ƙaunar Jehobah da kuma bin umurninsa. Amma kuma, zai dace mu zama masu sanin yakamata. A talifi na gaba, za mu tattauna yadda Jehobah da Yesu suka nuna sanin yakamata sosai don mu koya.
WAƘA TA 129 Za Mu Riƙa Jimrewa
a Tun lokacin su Adamu da Hauwaꞌu har yau, Shaiɗan yana ƙoƙarin sa mutane su ga cewa ba sa bukatar wani ya gaya musu abin da yake da kyau da marar kyau, don za su iya yin hakan da kansu. Yana so mu ma mu zama da wannan raꞌayin game da dokokin Jehobah da kuma umurnan da muke samu daga ƙungiyarsa. Mutane a duniyar nan sun fi so a bar su su yi abin da suka ga dama. Talifin nan zai taimaka mana mu guji wannan raꞌayin kuma mu ƙudiri niyyar yin biyayya ga Jehobah.
b Don ƙarin bayani a kan yadda Kirista zai bi abin da Jehobah ya ce game da jini, ka duba darasi na 39 na littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!
c Ka duba talifin nan, “Protect Yourself From Misinformation” da ke jw.org.
d Don ƙarin bayani, ka kalli jawabin nan mai jigo, “Wahayin Ezekiyel na Haikali da Yadda Ya Shafe Ka” a Taron Shekara-Shekara na 2017, kuma ka karanta darasi na 13 da 14 na littafin nan, Pure Worship of Jehovah—Restored At Last!