TALIFIN NAZARI NA 23
WAƘA TA 2 Jehobah Ne Sunanka
Sunan Jehobah Yana da Muhimmanci a Gare Mu
“Ni Yahweh na ce, ‘ku ne shaiduna.’”—ISHA. 43:10.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga yadda za mu nuna cewa Jehobah Allah ne mai tsarki, da kuma cewa duka abubuwan da Shaiɗan ya faɗa game da shi ƙarya ne.
1-2. Ta yaya muka san cewa Yesu yana ɗaukan sunan Jehobah da muhimmanci?
SUNAN Jehobah ne abu mafi muhimmanci a wurin Yesu. Yesu ne ya fi taimaka wa mutane su san game da sunan Jehobah. A talifin da ya wuce, mun koyi cewa Yesu ya ba da kome, har da ransa, don ya nuna cewa Jehobah yana da tsarki, da kuma cewa dukan abubuwan da yake yi daidai ne. (Mar. 14:36; Ibran. 10:7-9) Kuma a ƙarshen Sarautar Yesu na Shekara Dubu, Yesu zai mayar wa Jehobah dukan ikon da yake da shi domin Allah ya zama kome da kome. (1 Kor. 15:26-28) Abubuwan da Yesu ya yi don sunan Jehobah sun nuna cewa yana ƙaunarsa sosai.
2 Yesu ya zo duniya ne don ya gaya wa mutane dukan abin da Jehobah yake so su sani. (Yoh. 5:43; 12:13) Ya taimaka wa mabiyansa su ƙara sanin sunan Ubansa. (Yoh. 17:6, 26) Saꞌad da yake koyar da mutane da kuma yin abubuwan ban mamaki, ya nuna sarai cewa Jehobah ne ya ba shi hikima da kuma ikon yin abubuwan. (Yoh. 10:25) Kuma a lokacin da yake adduꞌa, ya roƙi Jehobah cewa ya lura da mabiyansa don ‘ikon sunansa.’ (Yoh. 17:11) Babu shakka, ba abin da ya fi sunan Jehobah muhimmanci a wurin Yesu. To, tun da haka ne, yaya mutum zai ce shi Kirista ne amma bai san sunan Allah ba, kuma ba ya amfani da shi?
3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
3 A matsayinmu na Kiristoci na gaske, muna koyi da Yesu ta wurin ƙauna da kuma daraja sunan Jehobah. (1 Bit. 2:21) A wannan talifin, za mu ga dalilin da ya sa ake kiran masu shelar ‘labari mai daɗi na Mulkin sama’ da sunan Jehobah. (Mat. 24:14) Za mu kuma tattauna dalilin da ya sa zai dace kowannenmu ya ɗauki sunan Jehobah da muhimmanci.
“JAMAꞌA TASA”
4. (a) Mene ne Yesu ya gaya wa almajiransa jim kaɗan kafin ya koma sama? (b) Wace tambaya ce za mu tattauna?
4 Jim kaɗan kafin Yesu ya koma sama, ya gaya wa almajiransa cewa: “Za ku sami iko saꞌad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku zama shaiduna a Urushalima, da cikin dukan yankin Yahudiya, da Samariya, har zuwa iyakar duniya.” (A. M. 1:8) Hakan ya nuna cewa almajiransa za su yi waꞌazi a koꞌina, ba a ƙasar Israꞌila kawai ba. Kuma hakan zai ba wa mutane a faɗin duniya damar zama mabiyan Yesu. (Mat. 28:19, 20) Amma Yesu ya ce: “Za ku zama shaiduna.” Shin, waɗanda za su zama almajiran Yesu, za su yi shelar sunansa kaɗai ne, ko suna bukatar su san sunan Jehobah kuma su yi shelar sa? Abubuwan da suka faru a Ayyukan Manzanni sura 15 sun taimaka mana mu amsa wannan tambayar.
5. Ta yaya manzanni da dattawa da ke Urushalima suka nuna cewa dukan mutane suna bukatar su san sunan Jehobah? (Ka kuma duba hoton.)
5 A shekara ta 49 bayan haihuwar Yesu, manzanni da dattawa da suke Urushalima, sun haɗu don su tattauna ko waɗanda ba Yahudawa ba suna bukatar su yi kaciya kafin su zama Kiristoci. A ƙarshen tattaunawarsu, ɗanꞌuwan Yesu Yakub ya ce: “[Bitrus] ya ba da labari yadda Allah ya fara ziyarci Alꞌummai, domin shi ciro wata jamaꞌa daga cikinsu domin sunansa.” Sunan waye ne Yakub yake magana a kai? Don ya amsa wannan tambayar, ya yi ƙaulin abin da ke littafin Amos. Ya ce: “Domin sauran mutanen duniya su nemi Ubangiji, da dukan Alꞌummai, waɗanda an kira sunana a bisansu, in ji Ubangiji,” wato Jehobah. (A. M. 15:14-18, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Waɗanda za su zama almajiran Yesu, suna bukatar su koya game da sunan Jehobah. Amma ba shi ke nan ba. Za su zama waɗanda za a sani da sunan. Hakan yana nufin cewa za su gaya wa mutane game da sunan kuma mutane za su san su a matsayin wakilan mai sunan.
A wani taron da ꞌyanꞌuwa masu ja-goranci suka yi a ƙarni na farko, sun gano sarai cewa wajibi ne Kiristoci su zama mutanen da aka sani da sunan Allah (Ka duba sakin layi na 5)
6-7. (a) Me ya sa Yesu ya zo duniya? (b) Ban da ceton ꞌyanꞌadam, wane dalili mafi muhimmanci ne ya sa Yesu ya zo duniya?
6 Sunan Yesu yana nufin “Jehobah Ne Mai Ceto,” kuma Jehobah ya yi amfani da Yesu wajen ceton dukan mutane da suka ba da gaskiya gare shi da kuma Ɗansa. Yesu ya zo duniya ne don ya ba da kansa a madadin ꞌyanꞌadam. (Mat. 20:28) Hakan ya ba mu damar samun gafarar zunubanmu da kuma rai na har abada.—Yoh. 3:16.
7 Amma me ya sa ꞌyanꞌadam suke bukatar fansar Yesu? Abin da ya faru a lambun Adnin ne ya sa muke bukatar fansar. Kamar yadda muka gani a talifin da ya wuce, Adamu da Hauwaꞌu sun yi wa Allah tawaye, kuma hakan ya sa suka rasa damar yin rayuwa har abada. (Far. 3:6, 24) Amma, Yesu ya zo duniya don ya yi wani abu da ya fi ceton ꞌyanꞌadam muhimmanci. Me ke nan? Shaiɗan ya tabka ƙarya dabam-dabam game da Jehobah. (Far. 3:4, 5) Saboda haka, ꞌyanꞌadam suna bukatar su san cewa Jehobah bai yi wani laifi ba, da kuma cewa shi Uba ne mai ƙauna. Abin da ya sa Yesu ya zo duniya ke nan, don ya taimaka wa ꞌyanꞌadam su san hakan. Babu wanda zai iya yin hakan fiye da Yesu domin shi wakilin Jehobah ne, kuma ya yi dukan abin da Jehobah ya ce masa ya yi babu kuskure.
Yaya mutum zai ce shi Kirista ne amma bai san sunan Allah ba, kuma ba ya amfani da shi?
8. Mene ne duka mabiyan Yesu suke bukatar su sani?
8 Duka mabiyan Yesu, da Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba suna bukatar su san ainihin wanda ya sa suka sami ceto, wato Jehobah Uban Yesu Kristi. (Yoh. 17:3) Ƙari ga haka, kamar yadda aka yi wa Yesu, za a kira duka mabiyansa masu aminci da sunan Jehobah. Ban da haka ma, za su bukaci su san muhimmancin tsarkake sunan Jehobah. Yin hakan ne zai sa su sami ceto. (A. M. 2:21, 22) Don haka, duk mabiyan Yesu masu aminci suna bukatar su san game da Jehobah da kuma Yesu. Ba mamaki, wannan ne dalilin da ya sa Yesu ya kammala adduꞌarsa da ke Yohanna sura 17 da cewa: “Na kuma sanar musu da sunanka, zan kuma sanar da shi; domin wannan ƙauna wadda ka ƙaunace ni da ita ta zauna cikinsu, ni kuma a cikinsu.”—Yoh. 17:26, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.
“KU NE SHAIDUNA”
9. Idan muna so mu zama mabiyan Yesu, mene ne muke bukatar mu yi?
9 Daga abubuwan da muka tattauna, mun ga cewa idan muna so mu zama mabiyan Yesu, wajibi ne mu tsarkake sunan Allah. (Mat. 6:9, 10) Muna bukatar mu ɗauka sunan Jehobah da muhimmanci fiye da kome a rayuwarmu. Don haka, me za mu yi don mu tsarkake sunan Jehobah kuma mu nuna cewa dukan abubuwan da Shaiɗan ya faɗa game da Jehobah ƙarya ne?
10. Mene ne littafin Ishaya sura 42 zuwa 44 suka koya mana? (Ishaya 43:9; 44:7-9) (Ka kuma duba hoton.)
10 A littafin Ishaya sura 42 zuwa 44, mun ga abin da za mu iya yi don mu tsarkake sunan Jehobah. A surorin nan, Jehobah ya kira waɗanda suke bauta ma wasu alloli su fito su nuna ko allolinsu na gaske ne. Kamar yadda ake yi a kotu, ya ce idan akwai wanda zai iya yin hakan, ya fito ya ba da shaida. Amma babu wanda ya fito!—Karanta Ishaya 43:9; 44:7-9.
A kome da muke yi da kuma faɗa, muna nuna cewa Jehobah ne Allah na gaskiya (Ka duba sakin layi na 10-11)
11. Bisa ga Ishaya 43:10-12, mene ne Jehobah ya gaya wa mutanensa?
11 Karanta Ishaya 43:10-12. Jehobah ya gaya wa mutanensa cewa: “Ku ne shaiduna, . . . ni kaɗai ne Allah.” Kuma ya gaya musu su amsa wannan tambayar: “Ko akwai wani Allah ban da ni?” (Isha. 44:8) Mu ma a yau, muna da babban gatar amsa wannan tambayar. Ta wurin abubuwan da muke faɗa da kuma abubuwan da muke yi, za mu nuna cewa Jehobah ne kaɗai Allah na gaskiya. Za mu kuma nuna cewa sunansa ne ya fi kowane suna. Ƙari ga haka, yadda muke rayuwa zai nuna cewa muna ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarmu, da kuma cewa za mu ci gaba da bauta masa ko da Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya hana mu yin hakan. Ta hakan, mu ma za mu sami damar tsarkake sunansa.
12. Ta yaya annabcin da ke Ishaya 40:3, 5 ya cika?
12 Idan mun goyi bayan sunan Jehobah, ko muka yi ƙoƙarin wanke sunansa daga zargi, muna koyi da Yesu ke nan. Annabi Ishaya ya annabta cewa wani zai “shirya wa Yahweh hanya.” (Isha. 40:3) Ta yaya hakan ya cika? Yohanna Mai Baftisma ya shirya wa Yesu hanya, wanda ya zo cikin sunan Jehobah, kuma ya yi magana cikin sunan Jehobah. (Mat. 3:3; Mar. 1:2-4; Luk. 3:3-6) Annabi Ishaya ya ƙara da cewa: “Ɗaukakar Yahweh za ta bayyana.” (Isha. 40:5) Ta yaya hakan ya cika? Saꞌad da Yesu ya zo duniya, ya wakilci Allah sosai babu kuskure, har kamar Jehobah da kansa ne ya zo duniya.—Yoh. 12:45.
13. Ta yaya za mu bi misalin Yesu?
13 Kamar Yesu, mu Shaidun Jehobah ne. An san mu da sunansa, kuma muna gaya wa kowa game da abubuwan ban mamaki da ya yi. Amma don mu iya yin hakan da kyau, dole ne mu gaya wa mutane dukan abubuwan da Yesu ya yi don ya tsarkake sunan Jehobah. (A. M. 1:8) Babu wanda ya ba da shaida game da Jehobah kamar yadda Yesu ya yi, kuma muna bin misalinsa. (R. Yar. 1:5) Amma a waɗanne hanyoyi ne kuma za mu nuna cewa muna daraja sunan Jehobah?
WASU HANYOYIN DA ZA MU NUNA CEWA MUNA ƊAUKAN SUNAN JEHOBAH DA MUHIMMANCI
14. Bisa ga Zabura 105:3, yaya muke ji game da sunan Jehobah?
14 Muna taƙama da sunan Jehobah. (Karanta Zabura 105:3.) Jehobah yana jin daɗi sosai idan muna taƙama da sunansa. (Irm. 9:23, 24; 1 Kor. 1:31; 2 Kor. 10:17) Babban gata ne gaya wa mutane cewa Jehobah Allah ne mai tsarki, kuma kome da yake yi daidai ne. Saboda haka, ba za mu taɓa jin kunyar gaya wa abokan aikinmu, da ꞌyanꞌajinmu, da maƙwabtanmu, da kuma wasu mutane cewa mu Shaidun Jehobah ne ba! Shaiɗan yana so mu daina gaya wa mutane game da sunan Jehobah. (Irm. 11:21; R. Yar. 12:17) Shi da masu yaɗa ƙarya sun fi so mutane su mance da sunan Jehobah. (Irm. 23:26, 27) Amma mu muna ƙaunar sunan Jehobah. Don haka, muna yabonsa kowane lokaci.—Zab. 5:11; 89:16.
15. Mene ne ake nufi da kiran sunan Jehobah?
15 Mu ci gaba da kiran sunan Jehobah. (Yow. 2:32; Rom. 10:13, 14) Kiran sunan Jehobah, ba ya nufin kira da yin amfani da sunan kawai. Ya ƙunshi sanin Allah da kyau, da dogara gare shi, da kuma neman taimako da ja-gorancinsa. (Zab. 20:7; 99:6; 116:4; 145:18) Kira ga sunan Jehobah ya kuma ƙunshi gaya wa mutane game da sunansa da kuma halayensa masu kyau. Za mu kuma taimaka musu su canja halayensu marar kyau zuwa halayen da suka jitu da raꞌayin Jehobah.—Isha. 12:4; A. M. 2:21, 38.
16. Ta yaya za mu nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne?
16 Muna shirye mu sha wahala don mu ɗaukaka sunan Jehobah. (Yak. 5:10, 11) Idan muka riƙe aminci ga Jehobah a lokacin da muke shan wahala, muna nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. A zamanin Ayuba, Shaiɗan ya yi wa bayin Allah sharri cewa: “Mutum zai iya ba da dukan abin da yake da shi domin ya ceci ransa.” (Ayu. 2:4) Shaiɗan ya yi daꞌawa cewa mutane za su bauta wa Jehobah kawai lokacin da abubuwa suke tafiya sumul a rayuwarsu. Amma idan abubuwa suka taɓarɓare, za su daina bauta masa. Amma Ayuba ya nuna cewa wannan abin da Shaiɗan ya faɗa ba gaskiya ba ne. Mu ma a yau, za mu iya nuna cewa wannan abin da Shaiɗan ya faɗa ba gaskiya ba ne, ta wajen ci gaba da bauta wa Jehobah. Za mu yi hakan ko da Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya sa mu sanyin gwiwa, ko kuma idan muna cikin yanayi mai wuya. Muna da tabbaci cewa Jehobah zai ci gaba da lura da mu don sunansa.—Yoh. 17:11.
17. Bisa ga 1 Bitrus 2:12, a wace hanya ce kuma za mu iya sa a yabi sunan Jehobah?
17 Mu yi iya ƙoƙarinmu don mu sa a yabi sunan Jehobah. (K. Mag. 30:9; Irm. 7:8-11) Da yake mutane sun san cewa mu Shaidun Jehobah ne, halinmu zai iya sa su yabi sunan Jehobah ko kuma su ƙi yin hakan. (Karanta 1 Bitrus 2:12.) Saboda haka, mu yi iya ƙoƙarinmu wajen yabon sunan Jehobah ta wurin maganganunmu da halayenmu. Idan muka yi hakan, duk da cewa mu ajizai ne, za mu sa mutane su yabi Jehobah.
18. A wace hanya ce kuma za mu iya nuna cewa muna ɗaukan sunan Jehobah da muhimmanci? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)
18 Muna ɗaukaka sunan Jehobah ko da mutane suna son hakan ko aꞌa. (Zab. 138:2) Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Domin a yawancin lokaci, idan muna yin abubuwan da Jehobah yake so, mai yiwuwa mutane ba za su so hakan ba, kuma suna iya yin munanan maganganu game da mu. a Alal misali, saꞌad da Yesu ya mutu, mutane sun ɗauka cewa shi mai laifi ne kuma sun tsane shi. Amma Yesu ya gwammaci ya mutu a wulaƙance don ya girmama sunan Jehobah. Bai mai da hankali a kan yadda mutane za su riƙa ganinsa ba. (Ibran. 12:2-4) A maimakon haka, ya mai da hankali ne ga yin nufin Allah.—Mat. 26:39.
19. Yaya kake ji game da sunan Jehobah, kuma me ya sa?
19 Muna alfahari da sunan Jehobah, kuma babban gata ne cewa ana kiran mu Shaidun Jehobah. Don haka, za mu ci gaba da ɗaukaka sunansa ko da mutane suna ganin cewa mu ba kome ba ne. Sunan Jehobah yana da muhimmanci fiye da kome da kome a rayuwa, har da mu kanmu. Saboda haka, bari mu ci gaba da yabon sunan Jehobah ko da Shaiɗan yana so ya hana mu. Idan muka yi hakan, za mu nuna cewa sunan Jehobah ne ya fi muhimmanci a gare mu, kamar yadda Yesu Kristi ya yi.
WAƘA TA 10 Mu Yabi Jehobah Allahnmu!
a Duk da cewa Ayuba mutum ne mai aminci, lokacin da abokansa uku suka gaya masa cewa laifin da ya yi ne ya sa yake shan wahala, ya mai da hankali a kan yadda mutane suke ɗaukansa. Da farko, saꞌad da ya rasa ꞌyaꞌyansa da dukiyoyinsa, “Ayuba bai yi zunubi ba, bai kuwa ba Allah laifi ba.” (Ayu. 1:22; 2:10) Amma, da aka zarge shi cewa ya yi laifi ne, ya “yi saurin magana.” Maimakon ya daraja Jehobah, Ayuba ya mai da hankali wajen kāre kansa da mutuncinsa.—Ayu. 6:3; 13:4, 5; 32:2; 34:5.