ABUBUWAN DA ZA KU IYA YIN NAZARI A KAI
Yadda Za Mu Jimre Rashin Adalci
Ku Karanta Farawa 37:23-28; 39:17-23 don ku koyi darasi daga yadda Yusufu ya jimre rashin adalci da aka yi masa.
Ku bincika labarin sosai. Me ya sa aka yi ma Yusufu rashin adalci? (Far. 37:3-11; 39:1, 6-10) Yaya tsawon lokacin da Yusufu ya yi yana jimre wannan rashin adalci? (Far. 37:2; 41:46) A lokacin, mene ne Jehobah ya yi masa, kuma mene ne Jehobah bai yi ba?—Far. 39:2, 21; w23.01 17 sakin layi na 13.
Ku nemi ƙarin bayani. Duk da cewa ƙarya ne matar Fotifar ta yi a kansa, Littafi Mai Tsarki bai ce Yusufu ya faɗi wani abu don ya kāre kansa ba. Mai yiwuwa Yusufu bai ce kome ba, ko kuma ƙila Littafi Mai Tsarki ne bai gaya mana dukan abin da ya faru ba. Ko da mene ne ya faru, nassosin da ke gaba za su taimaka mana mu yi tunani a kan abin da wataƙila ya sa. (K. Mag. 20:2; Yoh. 21:25; A. M. 21:37) Waɗanne halaye ne suka taimaka ma Yusufu ya jimre?—Mik. 7:7; Luk. 14:11; Yak. 1:2, 3.
Ku yi tunani a kan abubuwan da kuka koya. Kowa ya tambayi kansa:
-
‘Wane rashin adalci ne za a iya yi mini don ina bin Yesu?’ (Luk. 21:12, 16, 17; Ibran. 10:33, 34)
-
‘Ta yaya zan yi shiri don in iya jimrewa idan aka yi mini rashin adalci?’ (Zab. 62:7, 8; 105:17-19; w19.07 2-7)