Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 34

WAƘA TA 107 Mu Yi Koyi da Allah a Nuna Ƙauna

Yadda Za A Nuna wa Mai Zunubi Kauna da Jinkai

Yadda Za A Nuna wa Mai Zunubi Kauna da Jinkai

‘Nufin alherin Allah shi ne ya jawo ka ga tuba.’ROM. 2:4.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda dattawa suke ƙoƙari su taimaka ma waɗanda suka yi zunubi mai tsanani su tuba.

1. Mene ne za a iya yi ma wanda ya yi zunubi mai tsanani?

 A TALIFIN da ya gabata, mun ga abin da manzo Bulus ya ce wa ꞌyanꞌuwa da ke ikilisiyar Korinti su yi saꞌad da wani ya yi zunubi mai tsanani. Da ɗanꞌuwan bai tuba ba, an cire shi daga ikilisiya. Amma kamar yadda nassin da muke tattaunawa ya nuna, za a iya taimaka ma wanda ya yi zunubi mai tsanani ya tuba. (Rom. 2:4) Ta yaya dattawa za su taimaka wa mai zunubi ya tuba?

2-3. Idan mun san cewa wani ko wata a ikilisiya ta yi zunubi mai tsanani, me ya kamata mu yi, kuma me ya sa?

2 Kafin dattawa su san yadda za su taimaka wa mai zunubi, suna bukatar su san abin da ya faru. Don haka, idan mun san cewa wani ko wata a ikilisiya ta yi zunubi mai tsanani, me ya kamata mu yi? Mu ƙarfafa mutumin ya gaya wa dattawa su taimaka masa.—Isha. 1:18; A. M. 20:28; 1 Bit. 5:2.

3 Idan kuma mutumin ya ƙi ya gaya wa dattawa fa? Mu da kanmu mu je mu gaya wa dattawa, don su taimaka masa. Yin haka ƙauna ne, domin dattawa za su taimaka wa mai zunubin sosai. Ƙari ga haka, idan mutumin ya ci-gaba da yin zunubin, zai ɓata dangantakarsa da Jehobah. Zai kuma ɓata sunan ikilisiya. Don haka, ko da ba zai yi mana sauƙi ba, mu je mu gaya wa dattawa, saboda ƙaunar da muke yi wa Jehobah da kuma ꞌyanꞌuwanmu.—Zab. 27:14.

YADDA DATTAWA ZA SU TAIMAKA MA WAƊANDA SUKA YI ZUNUBI MAI TSANANI

4. Mene ne burin dattawa idan suka zauna da wanda ya yi zunubi mai tsanani?

4 Idan wani ya yi zunubi mai tsanani, dattawa za su zaɓi mutum uku a cikinsu, da za su yi aiki a matsayin kwamiti. a Waɗanda aka zaɓa suna bukatar su nuna halin sauƙin kai da sanin kasawarsu. Za su yi iya ƙoƙarinsu su taimaka wa mai zunubin ya tuba, amma sun san cewa ba za su iya tilasta masa ya tuba ba. (M. Sha. 30:19) Dattawa sun san cewa ba kowane mai zunubi ne zai tuba kamar yadda Sarki Dauda ya yi ba. (2 Sam. 12:13) Wataƙila wasu su ƙi amincewa da taimakon Jehobah. (Far. 4:​6-8) Duk da haka, burin dattawa shi ne su taimaka wa mai zunubin ya tuba. Me zai taimaka musu su yi nasara?

5. Wace shawara ce dattawa za su bi idan za su zauna da wanda ya yi zunubi? (2 Timoti 2:​24-26) (Ka kuma duba hoton.)

5 Dattawa sun san cewa Jehobah yana ƙaunar wanda ya yi zunubin. (Luk. 15:​4, 6) Saboda haka idan dattawa suka zauna da mai zunubin, za su yi masa magana da alheri, ba cikin fushi ko ɓacin rai ba. Kuma ba za su sa shi a gaba suna masa tambayoyi kawai ba. A maimakon haka, za su bi shawarar da ke 2 Timoti 2:​24-26. (Karanta.) Ƙoƙarinsu shi ne su taimaka masa ya canja halinsa, don haka za su yi masa magana a hankali, kuma cikin natsuwa.

Dattawa za su yi iya ƙoƙarinsu su taimaki wanda ya yi zunubi, kamar yadda makiyaya suke neman ɗan ragon da ya ɓata (Ka duba sakin layi na 5)


6. Ta yaya dattawa suke yin shiri don su zama da raꞌayin Jehobah kafin su zauna da wanda ya yi zunubi? (Romawa 2:4)

6 Dattawa sukan yi shiri don su zama da raꞌayin Jehobah. Sukan sa abin da manzo Bulus ya faɗa a zuciyarsu, cewa: ‘Nufin alherin Allah shi ne ya jawo ka ga tuba.’ (Karanta Romawa 2:4.) Dattawa su tuna cewa su makiyaya ne a ƙarƙashin Yesu, don haka suna bukatar su bi ja-gorancinsa kuma su yi koyi da shi. (Isha. 11:​3, 4; Mat. 18:​18-20) Kafin dattawa su zauna da mai zunubi, sukan yi adduꞌa ga Jehobah, su roƙe shi ya sa su iya taimaka wa mai zunubin ya tuba. Za su yi bincike a kan batun a Nassosi da littattafanmu, kuma su roƙi Jehobah ya taimaka musu su fahimci mutumin da kuma abin da ya faru. Za su kuma tattauna abin da wataƙila ya sa mutumin ya yi zunubin.—K. Mag. 20:5.

7-8. Ta yaya dattawa za su zama masu haƙuri kamar Jehobah idan suna tattaunawa da wanda ya yi zunubi?

7 Dattawa za su zama masu haƙuri kamar Jehobah. Sukan tuna da yadda Jehobah ya yi ta ƙoƙarin taimaka wa masu zunubi a dā. Alal misali, Jehobah ya yi haƙuri da Kayinu. Ya gaya masa abin da zai faru idan bai canja halinsa ba, kuma ya ce idan ya canja zai sami albarka. (Far. 4:​6, 7) Jehobah ya aiki annabi Natan ya gargaɗi Dauda. Kuma Natan ya ba wa Dauda wani misali da ya taimaka masa ya tuba. (2 Sam. 12:​1-7) Ban da haka ma, Jehobah ya “yi ta aika” wa Israꞌilawa annabawa, duk da cewa sun yi masa taurin kai. (Irm. 7:​24, 25) Jehobah bai jira sai sun tuba kafin ya taimaka musu ba. A maimakon haka, saꞌad da suke kan yin zunubin, ya yi ta ƙarfafa su su tuba.

8 Dattawa ma suna yin koyi da Jehobah saꞌad da suke ƙoƙarin taimaka wa wanda ya yi zunubi mai tsanani. Za su yi ƙoƙari su fahimtar da mutumin “da iyakacin haƙuri” kamar yadda 2 Timoti 4:2 ta ce. Wato, wajibi ne dattijo ya kasance mai haƙuri da kuma natsuwa, don ya iya ƙarfafa mai zunubin ya yi abin da ya kamata. Idan dattijo ya ɓata rai, zai yi wuya mai zunubin ya bi shawararsa ko ya tuba.

9-10. Ta yaya dattawa za su taimaki wanda ya yi zunubi ya ga abin da ya kai shi ga yin zunubin?

9 Dattawa za su yi ƙoƙari su fahimci abin da ya kai mutumin ga yin zunubin. Alal misali, za su bincika su san abin da ya sa bangaskiyarsa ta yi sanyi. Ya daina yin nazari yadda ya kamata ne, ko ya daina yin waꞌazi? Ya rage yadda yake yin adduꞌa ne, ko ya soma yin ta sama-sama kawai? Ya soma biye ma shaꞌawoyi marasa kyau ne? Akwai nishaɗin da yake yi da bai kamata ba? Ta yaya irin abubuwan nan suka shafe shi? Ya fahimci cewa abin da ya yi ya ɓata ma Jehobah rai sosai kuwa?

10 Zai yi kyau dattawa su yi masa tambayoyin da za su taimaka masa ya yi tunani a kan abin da ya kai shi ga yin wannan zunubin. Su yi hakan da alheri, kuma ba sai sun ce masa ya gaya musu wasu abubuwan da za su sa ya ji kunya ba. (K. Mag. 20:5) Ƙari ga haka, za su iya yin amfani da tambayoyi su taimaki wanda ya yi zunubin ya fahimci cewa abin da ya yi bai dace ba, kamar yadda Natan ya yi da Dauda. Wataƙila a zamansu na farko mutumin zai soma ganin kuskurensa, ko kuma ya tuba.

11. Ta yaya Yesu ya taimaka wa masu zunubi?

11 Dattawa za su yi ƙoƙari su yi koyi da Yesu. Alal misali, don Yesu ya taimaki Shawulu ya tuba, ya yi masa wata tambaya. Ya ce: “Shawulu, don me kake tsananta mini?” Wannan tambayar ta taimaka masa ya ga cewa abin da yake yi bai dace ba. (A. M. 9:​3-6) Kuma game da “macen nan Yezebel,” Yesu ya ce: “Na ba ta zarafi domin ta tuba.”—R. Yar. 2:​20, 21.

12-13. Ta yaya dattawa za su ba ma wanda ya yi zunubi zarafi don ya tuba? (Ka kuma duba hoton.)

12 Kamar Yesu, dattawa ba za su yi saurin kammala cewa wanda ya yi zunubi ba zai taɓa tuba ba. Wasu sukan tuba a zama na farko da dattawa suka yi da su, amma wasu suna bukatar a ba su lokaci. Don haka, dattawan za su iya su shirya yadda za su tattauna da wanda ya yi zunubin fiye da sau ɗaya. Wataƙila bayan zamansu na farko, mai zunubin zai yi tunani a kan abin da suka gaya masa. Mai yiwuwa ma ya ƙasƙantar da kansa ya roƙi Jehobah ya yafe masa. (Zab. 32:5; 38:18) Shi ya sa wani lokaci idan dattawa suka sake zama da mai zunubi, sai su ga cewa ya canja raꞌayinsa.

13 Don dattawa su taimaki wanda ya yi zunubin ya tuba, za su nuna masa ƙauna da tausayi. Za su roƙi Jehobah ya taimake su su yi nasara, kuma za su yi ta sa ran cewa ɗanꞌuwansu zai koma cikin hankalinsa.—2 Tim. 2:​25, 26.

Dattawa za su iya zama da wanda ya yi zunubi fiye da sau ɗaya, don su ba shi zarafi ya tuba (Ka duba sakin layi na 12)


14. Idan mai zunubi ya tuba, wa ya kamata a yaba wa, kuma me ya sa?

14 Idan wanda ya yi zunubi ya tuba, abin farin ciki ne sosai! (Luk. 15:​7, 10) Amma wa ya kamata a yaba wa? Dattawan ne? Aꞌa. Ka tuna abin da Bulus ya ce game da masu zunubi, ya ce: “Wataƙila Allah zai ba su dama su tuba.” (2 Tim. 2:25) Allah ne yake taimaka wa mutum ya tuba, ba wani ba. Don haka shi za a yaba wa. Bulus ya kuma ambaci amfanin da tuba yake kawowa. Ya ce yana sa mai zunubin ya ƙara fahimtar gaskiyar da ke Kalmar Allah, ya koma cikin hankalinsa, kuma ya kuɓuta daga tarkon Shaiɗan.

15. Ta yaya dattawa za su ci-gaba da taimakon wanda ya tuba?

15 Bayan mai zunubi ya tuba, dattawa za su ci-gaba da ziyartarsa suna ƙarfafa shi. Idan suka ziyarce shi, za su taimaka masa ya ci-gaba da ƙauce ma jarrabobin Shaiɗan, da kuma yin abin da zai faranta ma Jehobah rai. (Ibran. 12:​12, 13) Dattawa ba za su gaya ma wani zunubin da mutum ya yi ba. Amma akwai abin da za su iya gaya wa ikilisiya idan ya kama. Me ke nan?

“TSAWATA MUSU A GABAN JAMAꞌA”

16. Su waye ne “jamaꞌa” da Bulus ya yi zancensu a 1 Timoti 5:20?

16 Karanta 1 Timoti 5:20. Bulus ya gaya wa Timoti wanda shi ma dattijo ne, cewa ya tsawata wa masu zunubi “a gaban jamaꞌa.” Shin, wannan yana nufin cewa dole ne a sanar wa dukan ikilisiya matakin da dattawa suka ɗauka? Aꞌa. Waɗanda tun dā ma sun san abin da mutumin ya yi ne Bulus yake nufi da “jamaꞌa” a nan. Wataƙila sun ga abin da ya faru da idonsu, ko kuma wanda ya yi zunubin ne ya gaya musu. Su ne kaɗai dattawa za su gaya musu cewa sun ɗauki mataki a kan mutumin kuma an yi masa horo.

17. Idan ꞌyanꞌuwa da yawa sun riga sun san da zunubi mai tsanani da mutum ya yi, ko kuma akwai alamar cewa za su sani, wane sanarwa za a yi, kuma me ya sa?

17 A wasu lokuta mutane da yawa a ikilisiya sun riga sun san da zunubin da mutumin ya yi, ko kuma akwai alamar cewa za su sani daga baya. A irin wannan yanayin za a sanar da ikilisiya gabaki ɗaya, domin sun dace da “jamaꞌa” da Bulus ya yi magana a kai. Saboda haka a taron ikilisiya, wani dattijo zai sanar da cewa an yi wa ɗanꞌuwan ko ꞌyarꞌuwar horo. Bulus ya kuma gaya mana dalilin hakan. Ya ce: “Domin sauran su ji tsoro,” wato su guji yin irin wannan zunubi.

18. Idan yaro da ya yi baftisma ya yi zunubi mai tsanani, me dattawa za su yi? (Ka kuma duba hoton.)

18 Idan yaro da ya yi baftisma amma bai kai shekara 18 ba, ya yi zunubi mai tsanani kuma fa? Dattawa za su tura biyu daga cikinsu su tattauna da yaron da iyayensa idan su shaidun Jehobah ne. b Dattawa biyun za su tambayi iyayen yaron su ji matakan da suka ɗauka don su taimaki yaron ya canja halinsa kuma ya tuba. Idan yaron yana bin abin da suka gaya masa kuma ya soma canja halinsa, dattawa biyun za su iya tsai da shawara cewa ba a bukatar ɗaukan wani mataki fiye da wannan. Domin tun dā ma iyaye ne Jehobah ya ba wa hakkin yi wa yaransu gyara. (M. Sha. 6:​6, 7; K. Mag. 6:20; 22:6; Afis. 6:​2-4) Bayan haka, dattawa biyun za su ci-gaba da tattaunawa da iyayen yaron jifa-jifa, don su tabbata cewa suna taimaka wa yaron. Idan yaron ya ƙi ya canja halinsa fa? Wannan karo, kwamitin dattawa ne za a sa su zauna da yaron da kuma iyayensa.

Idan yaro da ya yi baftisma ya yi zunubi mai tsanani, dattawa biyu za su tattauna da yaron da iyayensa idan su Shaidu ne (Ka duba sakin layi na 18)


“[JEHOBAH] MAI JINƘAI NE, MAI YAWAN TAUSAYI KUMA”

19. Ta yaya dattawa suke bin halin Jehobah idan suna shaꞌani da wanda ya yi zunubi mai tsanani?

19 Jehobah ya ba wa dattawa hakkin tsare ꞌyanꞌuwa a ikilisiya daga mugun halin waɗanda ba sa so su bi dokokinsa. (1 Kor. 5:7) Amma za su yi iya ƙoƙarinsu su taimaki mutumin ya tuba. Kuma yayin da suke taimaka wa mai zunubi, za su yi ta sa ran cewa zai tuba. Me ya sa? Domin suna koyi da Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ce shi “mai jinƙai ne, mai yawan tausayi kuma.” (Yak. 5:11) Manzo Yohanna shi ma ya nuna wa ꞌyanꞌuwa ƙauna. Shi ya sa ya ce musu: “Ya ku ꞌyaꞌyana waɗanda nake ƙauna, ina rubuta muku wannan ne domin kada ku yi zunubi. Amma in har wani ya yi zunubi, to, muna da mai tsaya mana a gaban Uba, wato Yesu Almasihu mai adalci.”—1 Yoh. 2:1.

20. Me za mu tattauna a talifi na ƙarshe da ke wannan jerin talifofi?

20 Abin baƙin cikin shi ne, wani lokaci wanda ya yi zunubi yakan ƙi ya tuba. Kuma idan hakan ya faru, wajibi ne a cire shi daga ikilisiya. Ta yaya dattawa za su bi da irin wannan yanayin? Abin da za mu tattauna ke nan a talifi na ƙarshe da ke wannan jerin talifofi.

WAƘA TA 103 Jehobah Ya Yi Tanadin Makiyaya

a A dā ana ce da su kwamitin shariꞌa. Amma da yake yin shariꞌa ɗaya ne kawai daga cikin aikin da suke yi, ba za mu sake kiran su kwamitin shariꞌa ba. A maimako, za mu ce da su kwamitin dattawa kawai.

b Idan iyayen yaron ko masu kula da shi ba Shaidu ba ne, wani danginsa, ko mai nazari da shi, ko wani Mashaidi da yaron ya saba da shi, ya kasance tare da yaron a lokacin tattaunawar. Wanda zai kasance tare da yaron ya zama wanda ya kai shekaru 18 ko fiye da haka.