Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 15

WAƘA TA 124 Mu Kasance da Aminci

Ka Ƙara Yarda da Ƙungiyar Jehobah

Ka Ƙara Yarda da Ƙungiyar Jehobah

“Ku tuna da [‘waɗanda suke muku ja-goranci,’ NWT] waɗanda suka faɗa muku kalmar Allah.”IBRAN. 13:7.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu koyi yadda za mu ƙara nuna godiya don ƙungiyar Jehobah, mu ƙara yarda da ita, kuma mu ci-gaba da yin hakan.

1. Ta yaya aka tsara ƙungiyar Jehobah a ƙarni na farko?

 A DUK lokacin da Jehobah ya ba wa mutanensa aiki, yana so su yi aikin a matsayin ƙungiya kuma su yi shi cikin tsari. (1 Kor. 14:33) Alal misali, Jehobah yana so a yi waꞌazin mulkinsa a dukan faɗin duniya. (Mat. 24:14) Jehobah ya naɗa Yesu ya ja-goranci wannan aikin. Kuma Yesu ya ɗau mataki don a iya yin aikin cikin tsari. A ƙarni na farko, saꞌad da aka kafa ikilisiyoyi a wurare dabam-dabam, an naɗa dattawa don su yi ja-goranci. (A. M. 14:23) A Urushalima, akwai hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a lokacin, hukumar ta ƙunshi manzanni da dattawa. Su ne suke yanke shawarwari, kuma an bukaci dukan ikilisiyoyi su bi ja-gorancinsu. (A. M. 15:2; 16:4) Ikilisiyoyin sun bi shawarwarin, shi ya sa “suka ƙara ƙarfi cikin bangaskiya, suna ƙara yawa kowace rana.”—A. M. 16:5.

2. Tun daga 1919, ta yaya Jehobah yake wa bayinsa ja-goranci da kuma koya musu Kalmarsa?

2 A yau ma, Jehobah ya ci-gaba da tsara mutanensa a matsayin ƙungiya. Tun daga 1919, Yesu, wanda Jehobah ya naɗa, yana amfani da ƙaramin rukuni na shafaffun Kiristoci don ya ja-goranci waꞌazin da muke yi, kuma ya koya wa mabiyansa Kalmar Allah a daidai lokaci. a (Luk. 12:42) Ba shakka, Jehobah yana sa albarka a aikin da ꞌyanꞌuwan nan suke yi.—Isha. 60:22; 65:​13, 14.

3-4. (a) Ka ba da kwatanci da ya nuna yadda muke amfana don yadda muke yin abubuwa cikin tsari. (b) Me za mu tattauna a wannan talifin?

3 Da a ce ba ma yin abubuwa cikin tsari, da ba za mu iya yin aikin da Yesu ya ba mu ba. (Mat. 28:​19, 20) Alal misali, a ce ꞌyanꞌuwan ba su tsara inda kowace ikilisiya za ta riƙa yin waꞌazi ba, kowa zai iya yin waꞌazi a duk inda ya ga dama. Idan hakan ya faru, za a riƙa yin waꞌazi a wasu yankuna a-kai-a-kai. A wasu wurare kuma ba za a yi waꞌazi ba. Ka kuma yi tunanin wasu hanyoyin da muke amfana don muna yin abubuwa cikin tsari.

4 Kamar yadda Yesu ya tsara mabiyansa saꞌad da yake duniya, ya ci-gaba da tsara bayin Jehobah a yau. A wannan talifin, za mu ga misalan da Yesu ya kafa mana da kuma yadda ƙungiyarmu take bin misalinsa. Za mu kuma tattauna hanyoyin da za mu iya nuna godiyarmu don ƙungiyar Jehobah kuma mu nuna cewa mun yarda da ita.

ƘUNGIYARMU TANA BIN MISALIN YESU

5. Ka ambaci hanya ɗaya da ƙungiyarmu take bin misalin Yesu. (Yohanna 8:28)

5 Yesu ya koyi abin da zai yi da abin da zai faɗa daga wurin Ubansa. Kamar yadda Yesu ya yi, ƙungiyarmu tana amfani da Kalmar Allah don ta yi mana ja-goranci, kuma ta koya mana abin da ke da kyau da abin bai da kyau. (Karanta Yohanna 8:28; 2 Tim. 3:​16, 17) A kullum ana tuna mana muhimmancin karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin abin da muka koya. Mene ne za mu iya amfani da shi mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ta yaya hakan zai amfane mu?

6. Ka bayyana hanya ɗaya da muke amfana idan muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki.

6 Idan muka yi amfani da littattafanmu muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki, mukan amfana sosai. Alal misali, hakan yana taimaka mana mu ga ko abin da ƙungiyarmu ta ce ya yi daidai da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa. Idan muka ga cewa abin da suka faɗa a littattafanmu ya yi daidai da abin da ke Littafi Mai Tsarki, hakan yana sa mu ƙara yarda da su.—Rom. 12:2.

7. Wane abu ne Yesu ya yi waꞌazin sa, kuma ta yaya ƙungiyarmu take bin misalinsa?

7 Yesu ya yi waꞌazin ‘labari mai daɗi na Mulkin Allah.’ (Luk. 4:​43, 44) Ya kuma umurci almajiransa su yi waꞌazi game da Mulkin Allah. (Luk. 9:​1, 2; 10:​8, 9) A yau, kowa a ƙungiyar Jehobah yana yin waꞌazin Mulkin Allah, ko da a ina yake zama kuma kome yawan ayyuka da yake yi a ƙungiyar Jehobah.

8. Wane gata ne aka ba mu?

8 Babban gata ne aka ba mu da aka ce mu yi waꞌazin Mulkin Allah! Ba kowa ne aka ba wa wannan gatan ba. Alal misali, saꞌad da Yesu yake duniya, bai yarda aljanu su ba da shaida game da shi ba. (Luk. 4:41) A yau, kafin mutum ya soma yin waꞌazi tare da Shaidun Jehobah, dole ne ya nuna cewa ya cancanci samun wannan gatan. Idan muna yin waꞌazi a koꞌina da kuma kowane lokaci, za mu nuna cewa muna godiya don wannan gata da aka ba mu. Kamar Yesu, mu ma niyyarmu shi ne mu yi waꞌazi kuma mu koya wa mutane gaskiyar da ke Kalmar Allah.—Mat. 13:​3, 23; 1 Kor. 3:6.

9. Ta yaya ƙungiyarmu ta sanar da sunan Allah?

9 Yesu ya koya wa mutane sunan Allah. Da yake adduꞌa ga Ubansa, ya ce: “Na kuma sanar musu da sunanka.” (Yoh. 17:​26, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Ƙungiyar Jehobah tana yin iya ƙoƙarinta don ta taimaka wa mutane su san sunan Allah kamar yadda Yesu ya yi. Hanya ɗaya da ƙungiyarmu ta yi hakan ita ce ta wurin juyin New World Translation. A juyin an maido da sunan Jehobah a wuraren da sunan ya bayyana a asalin yaren da aka rubuta Littafi Mai Tsarki. An fassara wannan juyin zuwa yaruka 270. Wasu daga cikin yarukan, duka Littafi Mai Tsarki ne aka fassara, wasu kuma wani sashe ne aka fassara. A Appendix A4 da Appendix A5 na juyin New World Translation, za ka ga dalilan da suka sa aka maido da sunan Allah. Appendix C kuma da ke Study Bible, ya ƙara ba da ƙarin bayani a kan dalilin da ya sa ya kamata sunan Allah ya bayyana sau 237 a Nassosin Helenanci na Kirista.

10. Mene ne ka koya daga abin da wata mata daga ƙasar Myanmar ta faɗa?

10 Kamar Yesu, muna so mu yi iya ƙoƙarinmu mu taimaka wa kowa ya san sunan Allah. Wata tsohuwa mai shekara 67 a ƙasar Myanmar ta fashe da kuka da ta ji cewa Allah yana da suna. Ta ce wa malamarta: “Wannan ne karo na farko a rayuwata da na ji cewa sunan Allah shi ne Jehobah. . . . Wannan abin da kuka koya min shi ne abu mafi muhimmanci da na taɓa koya.” Kamar yadda misalin nan ya nuna, idan mutane suka gane sunan Allah, hakan zai iya canja rayuwarsu.

KA CI-GABA DA YARDA DA ƘUNGIYAR JEHOBAH

11. Ta yaya dattawa za su nuna cewa sun yarda da ƙungiyar Jehobah? (Ka kuma duba hoton.)

11 A wace hanya ce dattawa za su iya nuna cewa sun yarda da ƙungiyar Jehobah? Idan ƙungiyarmu ta ba da umurni, zai dace su yi iya ƙoƙarinsu su fahimci umurnin da kyau kuma su bi shi. Alal misali, ban da umurnan da ake ba su game da yadda za su gudanar da taro da kuma yadda za su riƙa yin adduꞌa idan ana taro, ana kuma ba su umurni a kan yadda za su kula da tumakin Kristi. Idan dattawa sun bi umurnin da ƙungiyarmu ta ba su, ꞌyanꞌuwa a ikilisiya za su ga cewa Jehobah yana ƙaunarsu kuma yana kula da su.

Dattawa suna taimaka mana mu ga amfanin bin umurnai da ƙungiyar Jehobah take ba mu (Ka duba sakin layi na 11) b


12. (a) Me ya sa ya dace mu yi biyayya ga waɗanda suke mana ja-goranci? (Ibraniyawa 13:​7, 17) (b) Me ya sa ya dace mu mai da hankali ga halaye masu kyau na waɗanda suke mana ja-goranci?

12 Idan dattawa suka ba mu umurni, zai dace mu bi umurnin da dukan zuciyarmu. Idan mun yi haka zai yi ma dattawa sauƙi su yi aikinsu. Littafi Mai Tsarki ya ce mu yi ma waɗanda suke mana ja-goranci biyayya, kuma mu miƙa kanmu a gare su. (Karanta Ibraniyawa 13:​7, 17.) Yin hakan zai iya yi mana wuya a wasu lokuta. Me ya sa? Domin waɗanda suke yi mana ja-goranci su ma ajizai ne. Idan muna mai da hankali ga kurakurensu maimakon halayensu masu kyau, muna taimaka wa maƙiyanmu ke nan. Me ya sa muka faɗi hakan? Domin idan muna mai da hankali ga kurakuren dattawa, zai yi mana wuya mu yarda da ƙungiyar Jehobah. Kuma abin da maƙiyanmu suke so ke nan. Me za mu yi don mu iya gane ƙaryace-ƙaryace da maƙiyanmu suke yaɗawa kuma mu guje su?

KADA KA BAR MUTANE SU SA KA DAINA YARDA DA ƘUNGIYAR JEHOBAH

13. Ta yaya maƙiyan Allah suke ƙoƙarin sa mutane su ga kamar ƙungiyarsa tana yin abubuwa da ba su dace ba?

13 Maƙiyan Allah suna yin ƙoƙari su sa mutane su ga kamar abubuwa masu kyau da ƙungiyar Jehobah take yi ba su dace ba. Alal misali, Jehobah yana so mu zama da tsabta a jikinmu da ɗabiꞌunmu kuma mu riƙa bauta masa yadda shi yake so. Ya ba mu umurni cewa duk wanda ya ci-gaba da yin abin ƙazanta kuma ya ƙi ya tuba, a cire shi daga ikilisiya. (1 Kor. 5:​11-13; 6:​9, 10) Muna bin wannan umurnin da Jehobah ya ba mu. Amma saboda haka, waɗanda suke hamayya da mu suna cewa ba ma ƙaunar mutane, muna shariꞌanta mutane, kuma muna ƙin mutanen da halinsu ya yi dabam da namu.

14. Wane ne yake sa mutane su yaɗa ƙaryace-ƙaryace game da ƙungiyar Jehobah?

14 Mu san asalin wanda yake kawo mana hari. Shaiɗan ne yake yaɗa ƙaryace-ƙaryace a kan ƙungiyar Jehobah. Shi ne “uban ƙarya.” (Yoh. 8:44; Far. 3:​1-5) Don haka, bai kamata mu yi mamaki ba idan magoya bayansa suna yaɗa ƙaryace-ƙaryace game da ƙungiyar Jehobah. Abin da ya faru ke nan a ƙarni na farko.

15. Mene ne malaman addinai suka yi wa Yesu da kuma mabiyansa?

15 Duk da cewa Yesu Ɗan Allah ba ya kuskure kuma ya yi muꞌujizai da yawa, Shaiɗan ya sa mutane sun yi ta yin ƙarya a kansa. Alal misali, malaman addinai a lokacin sun gaya wa mutane cewa “sarkin aljanu” ne ya ba wa Yesu ikon da yake amfani da shi ya kawar da aljannu. (Mar. 3:22) Saꞌad da ake wa Yesu shariꞌa, malaman addinan sun zargi Yesu da yin saɓo kuma sun zuga jamaꞌa su ce a kashe shi. (Mat. 27:20) Daga baya, yayin da Kiristoci suke waꞌazin Mulkin Allah, abokan gabansu sun “zuga waɗanda ba Yahudawa ba” don su tsananta wa Kiristocin. (A. M. 14:​2, 19) Ga bayani da Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba, 1998 ta yi a kan Ayyukan Manzanni 14:​2, ta ce: ‘Duk da cewa magoya bayan Shaiɗan sun ƙi amincewa da saƙon Kiristocin, hakan bai ishe su ba. Sai da suka yaɗa ƙaryace-ƙaryace game da Kiristocin don mutane su ƙi jin saƙonsu kuma su tsane su.’

16. Me ya kamata mu tuna idan muka ji labaran ƙarya?

16 Har wa yau, Shaiɗan yana yin ƙarya. Littafi Mai Tsarki ya ce yana ‘ruɗin dukan duniya.’ (R. Yar. 12:9) Idan ka ji ana ƙarya game da ƙungiyar Jehobah da kuma ꞌyanꞌuwa da suke ja-goranci, ka tuna cewa haka maƙiyan Allah suka yi wa Yesu da kuma almajiransa a ƙarni na farko. Yesu ya ce mutane za su yi hamayya da waɗanda suke bauta wa Jehobah kuma za su ta yin ƙarya a kan su, kuma abin da yake faruwa ke nan a yau. (Mat. 5:​11, 12) Idan muka gane asalin wanda yake sa a yaɗa labaran ƙarya game da mutanen Allah, ba za mu yarda da su ba. Me ya kamata mu yi?

17. Ta yaya za mu kiyayi labaran ƙarya? (2 Timoti 1:13) (Ka kuma duba akwatin nan “ Abin da Za Ka Yi In Ka Ji Labaran Ƙarya.”)

17 Ka kiyayi labaran. Manzo Bulus ya gaya mana abin da muke bukata mu yi idan muka ji ƙarya. Ya gaya wa Timoti ya “gargaɗi waɗansu mutane . . . kada su ba da hankalinsu ga tatsuniyoyi” amma su “yi nesa da tatsuniyoyin saɓo da na banza da wofi.” (1 Tim. 1:​3, 4; 4:7) Yaro ƙarami zai iya ɗaukan abu mai datti daga ƙasa kuma ya sa a bakinsa domin bai san kome ba. Amma babban mutum ba zai taɓa yi hakan ba don ya san akwai haɗari. Mu ƙi labaran ƙarya don mun san asalin wanda yake yaɗa su. Mu “riƙe koyarwar nan ta gaskiya sosai.”—Karanta 2 Timoti 1:13.

18. Ta yaya za mu nuna godiyarmu don ƙungiyar Jehobah?

18 Akwai hanyoyi da yawa da ƙungiyarmu take yin koyi da Yesu. Mun tattauna uku daga cikinsu. Yayin da kake yin nazarin Littafi Mai Tsarki, ka lura da hanyoyin da ƙungiyarmu take yin koyi da Yesu. Ka taimaka ma ꞌyanꞌuwa a ikilisiyarku su ƙara nuna godiyarsu don ƙungiyarmu kuma su ƙara yarda da ita. Ka ci-gaba da nuna godiyarka ta wajen kasancewa da aminci ga Jehobah, ka kuma kasance kusa da ƙungiyar da yake amfani da ita wajen cika nufinsa. (Zab. 37:28) Bari dukanmu mu ci-gaba da daraja gatan da aka ba mu na kasancewa cikin iyalin Jehobah, inda akwai mutane masu ƙauna da kuma aminci.

MECE CE AMSARKA?

  • A waɗanne hanyoyi ne mutanen Jehobah suke yin koyi da Yesu?

  • Ta yaya za mu ci-gaba da nuna godiyarmu don ƙungiyar Jehobah?

  • Me ya kamata mu yi idan muka ji labaran ƙarya?

WAƘA TA 103 Jehobah Ya Yi Tanadin Makiyaya

a Ka duba akwatin nan Why 1919? a littafin nan, Pure Worship of Jehovah—Restored At Last! Shafuffuka na 102-103.

b BAYANI A KAN HOTO: Bayan dattawa sun gama tattauna umurnin da ƙungiyarmu ta bayar a kan yin waꞌazi a inda Jamaꞌa suke, wani dattijo da ke kula da rukunin masu waꞌazi yana gaya ma wasu ꞌyanꞌuwa su tsaya a inda akwai katanga a bayansu.