Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yadda Za Ka Sami Salama Kuma Ka Yi Farin Ciki In Kana Cikin Damuwa

Yadda Za Ka Sami Salama Kuma Ka Yi Farin Ciki In Kana Cikin Damuwa

DAMUWA za ta iya zama kamar dutse mai nauyi a cikin zuciyar mutum. (K. Mag. 12:25) Ka taɓa fama da damuwa mai tsanani? Ka taɓa ji kamar ba za ka iya ci gaba da jimrewa ba? Hakan yana sa ka ji kamar ba za ka iya jimrewa ba? Idan haka ne, ba kai kaɗai ne ke jin hakan ba. Mai yiwuwa da yawa cikinmu muna kula da marasa lafiya ko wani namu ya mutu ko bala’i ya auko mana ko kuma muna fama da wata matsala da take sa mu gaji ko mu yi baƙin ciki ko kuma alhini. Amma mene ne zai taimaka mana mu san yadda za mu bi da damuwa? *

Za mu iya koyan yadda za mu bi da damuwa ta wajen tattauna misalin Sarki Dauda. Ya fuskanci matsaloli sosai a rayuwarsa. Har ma akwai lokutan da aka yi barazanar kashe shi. (1 Sam. 17:​34, 35; 18:​10, 11) Mene ne ya taimaka wa Dauda ya jimre sa’ad da yake damuwa? Ta yaya za mu bi misalinsa?

YADDA DAUDA YA JIMRE SA’AD DA YAKE CIKIN DAMUWA

Dauda ya fuskanci matsaloli da yawa a lokaci ɗaya. Alal misali, ka yi la’akari da abin da ya faru sa’ad da yake guje wa Sarki Shawulu. A lokacin da Dauda da mutanensa suka dawo daga yaƙi, sun yi mamaki da suka ga cewa maƙiyansu sun sace kayayyakinsu, sun ƙoƙƙone gidajensu kuma sun kwashi iyalansu. Mene ne Dauda ya yi? “Dauda da mutanensa suka fashe da kuka suka yi ta kuka har sai da ƙarfinsu ya ƙāre.” Ƙari ga hakan, mutanensa suka ce “za su jejjefe shi” da duwatsu. (1 Sam. 30:​1-6) Da hakan, Dauda ya fuskanci matsaloli uku masu tsanani a lokaci ɗaya: Iyalinsa sun fāɗa cikin haɗari, ya ji tsoro cewa mutanensa za su kashe shi, kuma har ila, Sarki Shawulu yana kan farautarsa. Ka yi tunanin yadda Dauda ya damu!

Mene ne Dauda ya yi? Nan take “ya ƙarfafa kansa gama ya dogara ga Yahweh Allahnsa.” Ta wace hanya ce Dauda ya yi hakan? Dauda ya yi abin da ya saba yi, ya yi addu’a ga Jehobah ya taimake shi kuma ya yi tunanin yadda Jehobah ya taimaka masa a dā. (1 Sam. 17:37; Zab. 18:​2, 6) Dauda ya san cewa yana bukatar ya tambayi Jehobah abin da ya kamata ya yi. Saboda haka, ya nemi ra’ayin Jehobah a kan abin da ya kamata ya yi. Bayan Dauda ya san ra’ayin Jehobah, ya ɗau mataki nan take. A sakamakon haka, Jehobah ya albarkace shi da mutanensa kuma sun dawo da iyalansu da kayayyakinsu. (1 Sam. 30:​7-9, 18, 19) Shin ka lura da abubuwa uku da Dauda ya yi? Ya yi addu’a ga Jehobah ya taimaka masa, ya yi tunanin yadda Jehobah ya taimaka masa a dā kuma ya bi umurnin Jehobah. Ta yaya za mu yi koyi da Dauda? Ga hanyoyi uku.

KA BI MISALIN DAUDA SA’AD DA KAKE CIKIN DAMUWA

1. Ka yi addu’a. A duk lokacin da muka fara damuwa, mu roƙe Jehobah ya taimaka mana kuma ya ba mu hikima. Za mu sami sauƙi idan muka gaya masa dukan abubuwan da ke damun mu. Ko kuma za mu iya yin addu’a a zuciyarmu na gajeren lokaci in iyakacin abin da za mu iya yi ke nan. A duk lokacin da muka roƙe Jehobah ya taimaka mana, muna nuna cewa mun dogara ga Jehobah kamar yadda Dauda ya yi sa’ad da ya ce: “Yahweh, dutsen ɓuyana, katangata da mai cetona. Allahna ne, dutsen ɓuyana, a wurinsa nake ɓuya.” (Zab. 18:⁠2) Shin addu’a tana taimakawa da gaske? Wata ’yar’uwa majagaba mai suna Kahlia ta ce: “Bayan na yi addu’a, nakan sami kwanciyar hankali. Addu’a tana taimaka mini in riƙa yin tunani kamar yadda Jehobah yake yi kuma in daɗa dogara gare shi.” Hakika, addu’a tanadi ne da Jehobah ya yi mana don ya taimake mu mu jimre yawan damuwa.

2. Ka tuna yadda Jehobah ya taimaka maka a dā. Za ka iya tunawa da wasu matsaloli da ka jimre a baya domin Jehobah ya taimaka maka? Idan muka yi tunanin yadda Jehobah ya taimaka mana da kuma wasu bayinsa a dā, za mu iya kasancewa da kwanciyar hankali kuma mu daɗa dogara gare shi. (Zab. 18:​17-19) Wani ɗan’uwa dattijo mai suna Joshua ya ce: “Nakan rubuta abubuwan da na roƙi Jehobah kuma ya amsa mini. Hakan yana tuna min lokacin da na roƙe Jehobah wani abu na musamman kuma ya ji addu’ata.” Yin tunanin yadda Jehobah ya taimaka mana a dā yana taimaka mana mu san yadda za mu riƙa shawo kan yawan damuwa.

3. Ka bi ƙa’idodin Jehobah. Kafin mu ɗau wani mataki, mu bincika Kalmar Allah don mu san ra’ayinsa. (Zab. 19:​7, 11) Mutane da yawa sun gano cewa idan suka bincika wata aya kafin su yanke shawara, suna iya fahimtar yadda ayar za ta taimake su. Wani dattijo mai suna Jarrod ya ce: “Yin bincike yana taimaka mini in daɗa fahimtar wani nassi kuma in fahimci abin da Jehobah yake so in sani. Hakan yana taimaka min in amince da abin da na karanta don in bi ja-gorancinsa.” Idan muka nemi ja-gorancin Jehobah a Littafi Mai Tsarki, kuma muka bi abin da muka karanta, za mu iya bi da damuwa yadda ya kamata.

JEHOBAH ZAI TAIMAKA MAKA KA JIMRE

Dauda ya fahimci cewa idan yana so ya shawo kan damuwa, yana bukatar taimakon Jehobah. Ya nuna godiya sosai don yadda Jehobah ya taimake shi, shi ya sa ya ce: “Da ikon Allahna zan iya tsallake kowace katanga. Allah shi ne mai ba ni ƙarfi.” (Zab. 18:​29, 32) Za mu iya ɗauka cewa matsalolinmu suna da yawa sosai da ba zai yiwu mu magance su ko jimre ba. Amma da taimakon Jehobah, za mu iya jimre kowace irin matsala! Hakika, idan muka nemi taimakon Jehobah, muka yi tunanin abubuwan da ya yi mana a dā, kuma muka bi ja-gorancinsa, za mu iya kasancewa da tabbacin cewa zai ba mu ƙarfi da hikimar da muke bukata don mu iya jimre matsalolinmu.

^ Mutumin da yake fama da ciwon damuwa yana bukatar ya tuntuɓi likita.