Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 37

“Zan Girgiza Dukan Kasashen Al’ummai”

“Zan Girgiza Dukan Kasashen Al’ummai”

“Zan girgiza dukan ƙasashen al’ummai, za su kuwa kawo arzikinsu a Gidana.”​—HAG. 2:7.

WAƘA TA 24 Ku Zo Tudun Jehobah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Wace girgiza ce annabi Haggai ya ce za ta faru a zamaninmu?

“A CIKIN ’yan mintoci, shaguna da tsofaffin gidaje suka soma rushewa.” “Kowa ya firgita . . . Mutane da yawa sun ce abin ya ɗauki minti biyu yana faruwa. Amma a ganina, ya ɗauki lokaci sosai yana faruwa.” Abin da wasu mutane suka faɗa ke nan bayan sun tsira daga girgizar ƙasa da aka yi a ƙasar Nepal a 2015. Idan ka fuskanci irin wannan mawuyacin yanayin, ba za ka taɓa mantawa da abin da ya faru ba.

2 Amma a yanzu, akwai wata irin girgiza dabam da take faruwa a dukan ƙasashe. Jehobah ne yake yin girgizar, kuma ya yi shekaru da yawa yana yin hakan. Annabi Haggai ya annabta cewa hakan zai faru. Ya ce: “Gama in ji Yahweh Mai Runduna, ‘Ba da jimawa ba, zan sake girgiza kome, sama da ƙasa, teku da busasshiyar ƙasa.’”​—Hag. 2:6.

3. Ta yaya girgizar da annabi Haggai ya yi magana a kai ya bambanta da girgizar ƙasa ta zahiri?

3 Annabi Haggai ba ya nufin girgizar ƙasa ta zahiri wadda hallaka kawai take yi. A maimakon haka, girgizar da Haggai ya yi magana a kai yana sa abubuwa masu kyau su faru. Jehobah da kansa ya gaya mana cewa: “Zan girgiza dukan ƙasashen al’ummai, za su kuwa kawo arzikinsu a gidana. Zan kuwa cika gidan nan da ɗaukaka.” (Hag. 2:7) Yaya wannan annabcin ya shafi mutane a zamanin Haggai? Kuma ta yaya annabcin ya shafe mu a yau? Za mu tattauna waɗannan tambayoyin, kuma za mu ga yadda mu ma za mu iya saka hannu a wannan aikin.

SAƘO MAI BAN ƘARFAFA A ZAMANIN HAGGAI

4. Me ya sa Jehobah ya aiki annabi Haggai ya ba da saƙo ga mutanensa?

4 Jehobah ya ba wa annabi Haggai aiki mai muhimmanci. Ka yi tunanin abin da ya faru kafin a ba shi aikin. Mai yiwuwa Haggai yana cikin Yahudawan da suka dawo Urushalima daga zaman bauta a Babila, a shekara ta 537 kafin haihuwar Yesu. Ba da daɗewa ba bayan sun isa Urushalima, Isra’ilawan sun kafa tushen haikalin Jehobah. (Ezra 3:8, 10) Amma jim kaɗan, wani abu marar daɗi ya faru. Sun daina gina haikalin domin al’ummai da ke kewaye da su, sun soma hamayya da su. (Ezra 4:4; Hag. 1:1, 2) Don haka, a shekara ta 520 kafin haihuwar Yesu, Jehobah ya gaya wa annabi Haggai ya ƙarfafa Yahudawan su sa ƙwazo don su gama gina haikalin. *​—Ezra 6:14, 15.

5. Me ya sa ya kamata saƙon Haggai ya ƙarfafa Yahudawan?

5 Dalilin da ya sa Jehobah ya ba wa Haggai saƙon shi ne ya taimaka wa Yahudawan su daɗa ba da gaskiya ga Jehobah. Da ƙarfin zuciya, annabin ya gaya wa Yahudawa da suka yi sanyin gwiwa cewa: “Ku yi ƙarfin zuciya, ya ku jama’ar ƙasar, in ji Yahweh. Ku yi aiki, gama Ni Yahweh Mai Runduna ina tare da ku.” (Hag. 2:4) Babu shakka, furucin nan “Yahweh Mai Runduna” ya ƙarfafa Isra’ilawan. Jehobah yana da mala’iku da yawa da za su iya yi masa yaƙi, don haka, Yahudawan suna bukatar su dogara gare shi idan suna so su yi nasara.

6. Me zai faru bayan girgizar da Haggai ya annabta?

6 Jehobah ya aiki annabi Haggai ya gaya wa Yahudawa cewa zai girgiza dukan al’ummai. Wannan saƙon ya ƙarfafa Yahudawan da suka yi sanyin gwiwa kuma suka daina gina haikalin. Ya nuna cewa Jehobah zai girgiza daular Fasiya, wadda take mulkin dukan duniya a lokacin. Mene zai faru bayan girgizar? Da farko, mutanen Allah za su kammala gina haikalin. Sa’an nan waɗanda ba Yahudawa ba ma za su zo su bauta ma Jehobah tare da su a cikin haikalin. Babu shakka, saƙon ya ƙarfafa mutanen Allah sosai!​—Zak. 8:9.

AIKIN DA YAKE GIRGIZA DUNIYA A YAU

Kana saka hannu a aikin girgiza al’ummai da ake yi a yau? (Ka duba sakin layi na 7-8) *

7. Wane aiki ne muke yi a yau da yake girgiza dukan duniya? Ka bayyana.

7 Ta yaya annabcin Haggai ya shafe mu a yau? A yau ma Jehobah yana girgiza dukan al’ummai, kuma a wannan karon muna yin hakan tare da shi. Ka yi la’akari da abin da ya faru a 1914, Jehobah ya naɗa Yesu a matsayin Sarkin Mulkinsa. (Zab. 2:6) Hakan bai yi ma shugabannin duniyar nan daɗi ba sam, domin ya nuna cewa “lokacinsu ya cika,” ko kuma lokacin da babu sarki mai wakiltar Allah ya ƙare. (Luk. 21:24) Don haka, musamman daga 1919, bayin Jehobah sun soma gaya wa mutane cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai magance duka matsalolin ’yan Adam. Yin wa’azin “labari mai daɗi na mulkin sama,” ya girgiza dukan duniya.​—Mat. 24:14.

8. Bisa ga Zabura 2:1-3, mene ne yawancin shugabannin duniya suka yi game da wa’azin Mulkin Allah?

8 Mene ne mutane suke yi game da saƙon nan? Yawancin mutane suna ƙin saƙon. (Karanta Zabura 2:1-3.) Al’ummai suna fushi. Sun ƙi su amince da Sarkin da Jehobah ya naɗa. Ba su yarda cewa wa’azin Mulkin da muke yi “labari mai daɗi” ne ba. Wasu gwamnatoci ma sun saka takunkumi a kan aikin wa’azin da muke yi! Da yawa daga cikin shugabannin duniya sun ce suna bauta wa Allah, amma ba sa so a karɓi ikon da suke da shi. Kamar yadda shugabanni a zamanin Yesu suka yi, shugabanni a yau ma sun ƙi amincewa da Wanda Jehobah Ya Naɗa ta yadda suke tsananta wa mabiyansa.​—A. M. 4:25-28.

9. Mene ne Jehobah ya yi don ya taimaka wa al’ummai?

9 Mene ne Jehobah ya yi domin al’ummai sun ƙi amincewa da wanda ya naɗa? Littafin Zabura 2:10-12 sun ba da amsar cewa: “Yanzu fa, ku yi hikima, ya ku sarakuna, ku yi hankali, ya ku masu mulkin duniya. Ku yi wa Yahweh hidima da tsoro kuna rawar jiki. Ku durƙusa a gabansa, kada fushinsa ya tashi ku mutu nan da nan, gama fushinsa mai saurin tashi ne. Masu albarka ne dukan masu neman wurin ɓuya a cikinsa.” Jehobah mai alheri ne, kuma ya ba su damar yanke shawarar da ta dace. Har ila za su iya canja ra’ayinsu kuma su amince da Mulkin Allah. Amma lokaci ya kusan ƙure musu domin muna rayuwa a “kwanaki na ƙarshe.” (2 Tim. 3:1; Isha. 61:2) Yanzu ne lokacin da ya dace mutane su yi hanzarin koya game da Jehobah kuma su bauta masa.

ABU MAI KYAU DA KE FARUWA SABODA GIRGIZAR

10. Ta yaya Haggai 2:7-9 suka nuna cewa wasu mutane za su amince da saƙon Mulkin?

10 Wasu mutane suna amincewa da saƙon Mulkin Allah. Annabi Haggai ya gaya mana cewa saboda girgizar, “dukan ƙasashen al’ummai, za su kuwa kawo arzikinsu [mutane masu zuciyar kirki] a Gidana,” wato za su zo su bauta wa Jehobah. * (Karanta Haggai 2:7-9.) Annabi Ishaya da Mika ma sun annabta cewa abu kamar haka zai faru a kwanakin ƙarshe.​—Isha. 2:2-4; Mik. 4:1, 2.

11. Mene ne wani ɗan’uwa ya yi a lokacin da ya fara jin saƙon Mulkin Allah?

11 Ka yi la’akari da yadda wannan saƙo mai girgiza al’ummai ya shafi ɗan’uwa Ken, wanda yake hidima a hedkwatarmu. Har yanzu yana tuna da abin da ya faru a lokacin da ya fara jin saƙon Mulkin Allah wajen shekaru 40 da suka wuce. Ken ya ce: “Na yi farin ciki sosai da aka nuna mini daga Littafi Mai Tsarki cewa muna kwanakin ƙarshe. Na fahimci cewa kafin in sami amincewar Allah da kuma rai na har abada, dole ne in fita sha’anin wannan duniyar, inda rayuwa ba ta da tabbas, kuma in fara bauta wa Jehobah. Na yi addu’a ga Jehobah kuma na ɗauki mataki nan da nan. Na fita sha’anin duniya kuma na soma goyon bayan Mulkin Allah da ba abin da zai iya girgiza shi.

12. Ta yaya haikalin Allah ya cika da ɗaukaka a wannan kwanakin ƙarshe?

12 A bayyane yake cewa Jehobah yana yi wa mutanensa albarka. A wannan kwanaki na ƙarshe, mun ga yadda mutane da yawa suka soma bauta wa Jehobah. A 1914, da kaɗan Shaidun Jehobah suka fi dubu 5. Amma a yanzu, akwai mutane sama da miliyan 8 da suke bauta ma Jehobah. Kuma kowace shekara miliyoyin mutane suna halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Don haka, arzikin ƙasashen al’ummai sun shigo farfajiyar da ke haikalin Allah. Wannan haikalin shi ne tsarin da Allah ya yi na bauta ta gaskiya. Canje-canje da mutanen nan suke yi ta wajen koyan sabon hali, yana ɗaukaka sunan Jehobah.​—Afis. 4:22-24.

Bayin Allah a faɗin duniya suna jin daɗin yin wa’azi ga mutane game da Mulkin Allah (Ka duba sakin layi na 13)

13. Yayin da bayin Jehobah suke ƙaruwa, wane annabci ne yake cika? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

13 Yadda mutane suke zuwa su bauta ma Jehobah ya cika annabcin da ke Littafin Ishaya sura 60. Aya 22 ta surar ta ce: “Mafi ƙanƙanta a cikinki kuma zai zama al’umma mai ƙarfi. Ni Yahweh ne, da sauri zan sa wannan ya cika a daidai lokaci.” Saboda mutane da yawa da suka soma bauta ma Jehobah, wani abu mai muhimmanci ya faru. Waɗannan mutanen suna da baiwa, sun ƙware a yin ayyuka dabam-dabam kuma suna son yin shelar “labari mai daɗi na mulkin sama.” A sakamakon haka, ƙungiyar Jehobah tana amfani da waɗannan baiwa da annabi Ishaya ya kira “nonon al’ummai.” (Isha. 60:5, 16, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Da taimakon waɗannan maza da mata, ana yin wa’azi a ƙasashe 240, kuma ana wallafa littattafai a yaruka fiye da 1,000.

LOKACIN YANKE SHAWARA

14. Wace shawara ce mutane suke bukatar su yanke?

14 A wannan kwanaki na ƙarshe, wa’azin Mulkin Allah yana girgiza mutane kuma yana sa su ɗauki mataki. Za su goyi bayan Mulkin Allah ne ko kuma za su dogara ga gwamnatocin wannan duniyar? Wannan shawara ce da kowa zai yanke da kansa. Ko da yake bayin Jehobah suna yin biyayya ga dokokin ƙasashen da suke zama, ba sa saka hannu a harkokin siyasa. (Rom. 13:1-7) Sun san cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai magance matsalolin ’yan Adam. Wannan Mulkin ba na duniya ba ne.​—Yoh. 18:36, 37.

15. Ta yaya littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ta nuna cewa za a gwada amincin bayin Allah?

15 Littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ya nuna cewa za a gwada amincin bayin Allah a kwanakin ƙarshe. Wannan gwajin zai sa a yi hamayya da mu, kuma a tsananta mana. Gwamnatocin duniya za su bukaci mu bauta musu, kuma za su tsananta ma duk wanda ya ƙi yin hakan. (R. Yar. 13:12, 15) Za su sa “a yi wa dukan mutane lamba a hannunsu na dama ko a goshinsu, manya da ƙanana, mai arziki da talaka, bawa da mai ’yanci.” (R. Yar. 13:16) Akan saka wa bayi lamba a zamanin dā don a iya gane maigidansu. A yau ma, mutane za su bukaci kowa ya nuna wanda yake goya wa baya. Furucinsu da ayyukansu, za su nuna cewa suna goyon bayan gwamnatocin wannan duniyar.

16. Me ya sa muke bukatar mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah yanzu?

16 Shin za mu karɓi wannan lambar kuma mu goyi bayan gwamnatocin wannan duniyar? Waɗanda suka ƙi karɓan lambar za su sha wahala kuma za su shiga mawuyacin hali. Littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ya ƙara da cewa babu wanda zai ‘saya ko ya sayar idan ba shi da lambar.’ (R. Yar. 13:17) Amma bayin Allah sun san abin da Allah zai yi ma waɗanda suka karɓi lambar da aka ambata a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 14:9, 10. Maimako su karɓi lambar, za su rubuta a hannunsu cewa su “Na Yahweh” ne. (Isha. 44:5) Yanzu ne ya kamata mu ƙarfafa amincinmu ga Jehobah. Idan muka yi hakan, Jehobah zai yi farin ciki cewa mu nasa ne!

GIRGIZA TA ƘARSHE

17. Me muke bukatar mu tuna game da haƙurin Jehobah?

17 Jehobah yana haƙuri sosai a wannan kwanaki na ƙarshe. Ba ya so kowa ya hallaka. (2 Bit. 3:9) Ya ba wa kowa damar tuba da kuma bauta masa. Amma haƙurinsa yana da iyaka. Waɗanda suka ƙi su goyi bayan Mulkin Allah za su fuskanci abin da ya faru da Fir’auna a zamanin Musa. Jehobah ya gaya wa Fir’auna cewa: “Gama da a ce tun tuni na miƙa hannuna na buge ka da mutanenka da bala’i, da an riga an kawar da kai daga fuskar duniya. Amma ni dai na bar ka ka rayu har war haka domin wannan dalili, wato domin in nuna maka ikona, in kuma sanar da Sunana a cikin duniya duka.” (Fit. 9:15, 16) A ƙarshe, dukan al’ummai za su sani cewa Jehobah ne Allah na gaskiya. (Ezek. 38:23) Ta yaya hakan zai faru?

18. (a) Wace irin girgiza ce kuma aka ambata a Haggai 2:​6, 20-22? (b) Ta yaya muka san cewa annabcin Haggai zai cika a nan gaba?

18 Karanta Haggai 2:6, 20-22. Shekaru da yawa bayan Haggai ya rasu, manzo Bulus ya rubuta wasiƙa ga Ibraniyawa, kuma ya nuna cewa annabcin da Haggai ya yi zai cika a nan gaba. Bulus ya ce: “Amma yanzu ya yi alkawari cewa, ‘Zan girgiza duniya sau ɗaya kuma, ba duniya kaɗai ba, amma har da sammai.’ Wannan magana, ‘sau ɗaya kuma,’ ta nuna za a kawar da abin da aka girgiza, wato, za a kawar da abubuwan da aka halitta, domin abubuwan da ba za a iya girgiza su ba su kasance.” (Ibran. 12:26, 27) Wannan girgizar ta bambanta da wadda aka ambata a Haggai 2:7. Wannan girgizar tana nufin cewa mutane da suka ƙi goyon bayan Mulkin Allah kamar Fir’auna, za su hallaka.

19. Mene ne ba za a girgiza ba, kuma ta yaya muka sani?

19 Mene ne ba za a girgiza ba? Bulus ya ci gaba da cewa: “Da yake muna karɓar mulkin da ba za a iya girgiza ba, bari mu yi godiya, mu kuma miƙa wa Allah sujada da ta dace a cikin tsoro da ban girma.” (Ibran. 12:28) Bayan an kammala wannan girgizar, Mulkin Allah ne kaɗai zai rage. Mulkin zai kasance yadda yake!​—Zab. 110:5, 6; Dan. 2:44.

20. Wane zaɓi ne mutane suke bukatar su yi, kuma ta yaya za mu taimaka musu?

20 Lokaci kaɗan ne ya rage! Mutane suna bukatar su zaɓa ko za su ci gaba da goyon bayan wannan duniyar da zai kai su ga hallaka, ko kuma za su soma bin ƙa’idodin Allah don su sami rai na har abada. (Ibran. 12:25) Ta wa’azin da muke yi, za mu iya taimaka wa mutane su yanke wannan shawara mai muhimmanci. Bari mu ci gaba da taimaka wa mutane da yawa su yanke shawarar bauta wa Jehobah. Kuma mu riƙa tunawa da abin da Ubangijinmu Yesu Kristi ya ce: “Za a ba da wannan labari mai daɗi na mulkin sama domin shaida ga dukan al’umma, sa’an nan ƙarshen ya zo.”​—Mat. 24:14.

WAƘA TA 40 Waye ne Allahnka?

^ sakin layi na 5 Abin da za a tattauna ƙarin haske ne ga yadda muka fahimci annabcin da ke Haggai 2:7. A wannan talifin, za mu ga yadda mu ma za mu saka hannu a aikin da ke girgiza dukan al’ummai. Ƙari ga haka, za mu kuma ga cewa wasu suna son aikin da muke yi, wasu kuma ba sa so.

^ sakin layi na 4 Mun san cewa Haggai ya yi abin da Jehobah ya ce masa ya yi domin an gama gina haikalin a shekara ta 515 kafin haihuwar Yesu.

^ sakin layi na 10 Bayanin nan ya canja yadda muka fahimci wannan ayar. A dā, mukan ce ba girgizar al’ummai ce take sa masu zuciyar kirki su soma bauta ma Jehobah ba. Ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” da ke Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuni, 2006.

^ sakin layi na 63 BAYANI A KAN HOTUNA: Haggai ya ƙarfafa bayin Allah su yi ƙwazo a gina haikalin, kuma bayin Allah a zamaninmu suna yin wa’azin Mulkin Allah da ƙwazo. Wasu ma’aurata suna wa’azi game da girgiza ta ƙarshe.