TARIHI
Yadda Na Koyi Gaskiya Duk da Yake Ba Ni da Hannaye
A yawancin lokaci idan mutane suna jin tsoro, suna riƙe wani abu. Amma ba na iya yin haka domin ba ni da hannaye. Sa’ad da nake ɗan shekara bakwai ne aka yanke hannuwana domin kada in mutu.
Mahaifiyata tana da shekara 17 sa’ad da ta haife ni a shekara ta 1960. Mahaifina ya rabu da mahaifiyata kafin a haife ni. Ni da mahaifiyata mun zauna tare da kakana a wani ƙaramin gari da ake kira Burg a Gabashin ƙasar Jamus. Mutane da yawa a garin har da iyalinmu ba su yarda da wanzuwar Allah ba. Babu ruwanmu da Allah.
Yayin da nake girma, ina jin daɗin kasancewa tare da kakana. Yana sa ni ayyuka iri-iri, har ma yana cewa in hau bishiya don in yanke reshe. Ina jin daɗin ayyukan sosai. Ina farin ciki kuma ba na jin tsoro.
HATSARI YA CANJA RAYUWATA
Wani abin taƙaici ya faru da ni sa’ad da nake ɗan shekara bakwai. A lokacin ban daɗe da shigan aji biyu ba. Yayin da nake dawowa gida, sai na hau falwaya. Da na hau na kai kafa 25, sai wutan lantarki ya ja ni kuma na sume. Sa’ad da na farfaɗo, sai na lura cewa hannuwana sun mutu. Lantarkin ya ƙona hannuwana sosai har aka yanke su don kada gubar ta ɓata jinina. Hakan ya rikitar da iyayena sosai. Amma da yake ni yaro ne a lokacin, ban fahimci yadda rashin hannu zai shafi rayuwata ba.
Na koma makaranta bayan da aka sallame ni daga asibiti. Yara suna yawan tsokana na, suna ture ni da jifa na domin sun san cewa ba zan iya kāre kaina ba. Hakan yana sa ni baƙin ciki sosai. Daga baya, sai aka tura ni makarantar kwana ta naƙasassu a garin Birkenwerder. Da yake makarantar tana da nisa da gidanmu, mahaifiyata da kakannina ba sa iya kawo mini ziyara. A lokacin hutu kawai nake ganinsu. Na yi shekara goma a wurin ba tare da renon mahaifiyata da kakannina ba.
YIN GIRMA BA TARE DA HANNAYE BA
Na koya wa kaina yin wasu ayyuka ta wajen yin amfani da ƙafafuna. Ka taɓa yin tunanin yadda yake da wuya mutum ya riƙe cokali da yatsun kafa yana cin abinci? Abin da na koya wa kaina ke nan. Na kuma koya riƙe buroshin goge haƙora da matajen kai da yatsun ƙafafuna. Na ma soma yin motsi da ƙafafuna sa’ad da nake magana da mutane. Ƙafafuna sun zama hannuwana.
Sa’ad da na zama matashi, ina jin daɗin karanta littattafan kimiyya. A wasu lokuta, ina tunanin samun hannun na’ura da zan iya yin kome da shi. Na soma shan taɓa sigari sa’ad da nake ɗan shekara 14. Na ga kamar yana sa in ji daɗin jikina kuma in kasance kamar sauran mutane. Kamar dai ina ce wa kaina: ‘E, ba a bar ni a baya ba. Masu shaye-shaye manya ne ko suna da hannu ko ba su da shi.’
Na shagala da ayyuka iri-iri. Sai na shiga rukunin matasa da ake kiran Free German Youth, ni ne sakatare a ƙungiyar kuma wannan babban matsayi ne. Na kuma shiga rukunin mawaƙa, na rubuta waƙoƙi kuma na soma wasanni na naƙasassu. Bayan na gama koyan wani sana’a, sai na soma aiki a wani kamfani a garinmu. Yayin da nake girma, ina saka hannun robana sosai domin ba na so a gan ni kamar naƙasasse.
KOYAN GASKIYAR LITTAFI MAI TSARKI
Wata rana da nake jiran jirgin ƙasa da zan shiga zuwa wurin aiki, sai wani mutum ya zo wurina. Ya tambaye ni ko zan so wata rana Allah ya maido mini da hannayena. Hakan ya sa ni mamaki. Ko da yake ina son hannuwana, amma a ganina hakan ba zai yiwu ba! Ban ma yarda cewa Allah ya wanzu ba. Daga ranar, sai na soma ɓoye wa mutumin.
Bayan wani lokaci, wata abokiyar aikina ta gayyace ni zuwa gidansu. Sa’ad da muke shan shayi, sai iyayenta suka soma tattaunawa da ni game da Allah Jehobah. Wannan ne lokaci na farko da na ji cewa Allah yana da suna. (Zabura 83:18) Amma na ce a zuciyata: ‘Babu Allah, ko da mene ne sunansa. Sai na nuna wa mutanen nan cewa ƙarya suke yi.’ Da yake na riƙe imanina gam-gam, sai na yarda mu tattauna Littafi Mai Tsarki tare. Amma na kasa tabbatar musu da cewa Allah ba ya wanzuwa.
Yayin da muke tattauna annabcin Littafi Mai Tsarki, sai na soma canja ra’ayina. Annabci da yawa da Allah ya yi sun cika, ko da yake an rubuta su ɗarurruwan shekaru kafin su auku. A wani lokaci da muke tattauna Littafi Mai Tsarki, mun gwada abubuwan da ke faruwa a duniya yau da annabcin da ke Matta sura 24 da Luka sura 21 da kuma 2 Timotawus sura 3. Kamar yadda alamu dabam-dabam a jikin mutum za su iya taimaka wa likita ya san ciwon da ke damunsa, hakan ma abubuwan da aka ambata a annabcin sun taimaka mini in san cewa muna rayuwa a “kwanaki na ƙarshe.” * Hakan ya ba ni mamaki sosai domin ina ganin yadda annabcin suke cika.
Na yi imani cewa abin da nake koya gaskiya ne. Na soma addu’a ga Jehobah kuma na daina shan taba sigari ko da yake na kwashi shekaru da yawa ina shan sigari. Na ci gaba da yin nazarin Littafi
Mai Tsarki har wajen shekara ɗaya. A ranar 27 ga Afrilu, 1986, na yi baftisma a wani baho a asirce domin a lokacin, an saka wa aikinmu takunkumi a Gabashin Jamus.TAIMAKA WA WASU
Muna yin taro a ƙananan rukunoni a gidajen ‘yan’uwa kuma ban san ‘yan’uwa da yawa ba. Amma abin mamaki, hukuma ta yarda in yi tafiya zuwa Yammacin Jamus inda ba a saka wa aikinmu takunkumi ba. Wannan ne lokaci na farko a rayuwata da na halarci taron yanki kuma na ga dubban ‘yan’uwa maza da mata. Hakan ya sa ni farin ciki sosai.
An cire takunkumin da aka saka wa Shaidun Jehobah sa’ad da aka rushe Ganuwar Berlin. Mun sami ‘yancin bauta wa Jehobah a fili. Na so in faɗaɗa hidimata. Amma, ina kunyar haɗuwa da baƙi. Yanayina da kuma gidan naƙasassu da na zauna suna sa in ji kamar ba zan iya yin kome ba. Amma a shekara ta 1992, na gwada yin wa’azi na sa’o’i 60 a wata ɗaya. Na cim ma maƙasudina kuma na yi farin ciki sosai. Sai na ci gaba har wajen shekara uku.
Ina yawan tunawa da kalmomin nan a cikin Littafi Mai Tsarki: “Wanene rarrauna, ni ban zama rarrauna” ba? (2 Korintiyawa 11:29) Me ya sa? Domin ko da yake na naƙasa, amma ina da ƙwaƙwalwa da kuma baƙi. Saboda haka, na yi ƙoƙarin taimaka wa wasu duk da yanayina. Ina tausaya wa mutanen da suka naƙasa domin ni ma na naƙasa. Na san yadda mutum yake ji idan yana so ya yi wani abu amma ya kasa. Ina ƙarfafa mutanen da suke jin haka. Taimaka wa mutane yana sa ni farin ciki.
JEHOBAH YANA TAIMAKA MINI KULLUM
A gaskiya, ina baƙin ciki a wasu lokuta. Ba na so in zama mai naƙasa. Ina iya yin ayyuka na yau da kullum da kaina, amma yana ɗaukan lokaci sosai kuma yana mini wuya. Abin da nake cewa kullum shi ne: ‘Zan iya yin abu duka ta wurin Kristi da yake ƙarfafani.’ (Filibiyawa 4:13) Jehobah yana ba ni ƙarfin yin ayyuka na yau da kullum. Na lura yadda Jehobah yake taimaka mini, shi ya sa ba na so in daina bauta masa.
Jehobah ya albarkace ni da abin da ba ni da shi sa’ad da nake ƙarami, wato iyali. Matata Elke tana ƙaunar mutane da kuma tausaya musu sosai. Ƙari ga hakan, miliyoyin Shaidun Jehobah sun zama iyalina.
Alkawarin da Allah ya yi mana cewa zai “sabonta dukan abu,” har da hannuwana yana ƙarfafa ni. (Ru’ya ta Yohanna 21:5) Yin bimbini a kan abubuwan da Yesu ya yi sa’ad da yake duniya suna sa in daɗa fahimtar wannan alkawarin sosai. Alal misali, ya warkar da gurgu kuma ya manne kunnen wani mutum da aka yanke. (Matta 12:13; Luka 22:50, 51) Alkawuran Jehobah da kuma mu’ujizai da Yesu ya yi sun tabbatar mini da cewa nan ba da daɗewa ba, zan sake samun hannuwana biyu.
Amma albarka mafi girma da na samu ita ce sanin Jehobah Allah. Ya zama ubana da aminina da mai ta’azantar da ni da kuma mai ƙarfafa ni. Ra’ayina ya zo ɗaya da na Sarki Dauda sa’ad da ya ce: “Ubangiji ƙarfina ne . . . na sami taimako: domin wannan zuciyata tana murna ƙwarai.” (Zabura 28:7) Ina so in riƙe wannan gaskiyar hannu bibbiyu muddar raina. Na same ta duk da yake ba ni da hannuwa.
^ sakin layi na 17 Don samun cikakken bayani a kan abubuwan da za su faru a kwanaki na ƙarshe, ka duba babi na 9, “Shin Ƙarshen Duniya Ya Kusa?” a littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi kuma za ka iya samunsa a dandalin www.jw.org/ha.