Me Yake Shafan Yadda Rayuwarmu Za Ta Kasance?
Mutane da yawa sun gaskata cewa akwai wasu abubuwa da suke sa su yi sa’a ko rashin sa’a a rayuwa. Saboda haka, suna yin abubuwa dabam-dabam da suke ganin za su sa su riƙa yin sa’a don rayuwarsu ta yi kyau.
ABIN DA WASU SUKA GASKATA
YIN DUBA DA TAURARI: Mutane da yawa sun gaskata cewa yadda taurari suka jeru a lokacin da aka haife su zai shafi yadda rayuwarsu za ta kasance. Suna zuwa wurin masanan taurari ko masu sihiri don su ji abin da zai faru da su a nan gaba ko kuma su san matakin da za su ɗauka.
BOKAYE: Wasu mutane sun gaskata cewa bokaye za su iya yin duba kuma su gaya musu abin da ya sa wasu abubuwa suke faruwa da su, da abin da ya kamata su yi. Suna ganin da zarar sun san sanadiyyar matsalolinsu, za su kauce musu ko su nemi mafita don su yi nasara a rayuwa.
BAUTA WA KAKANNI: Har ila wasu sun gaskata cewa dole ne su faranta ran kakanninsu da suka mutu, in har suna son su sami kāriya da kuma albarka. Wata mata mai suna Van * daga ƙasar Vietnam ta ce: “Na gaskata cewa idan na daraja kakannina da suka mutu, ni da yarana za mu ji daɗin rayuwa yanzu da kuma nan gaba.”
SAKE HAIFAN MUTUM: Wasu mutane sun gaskata cewa idan mutum ya mutu, akan sake haifan sa kuma hakan yana faruwa sau da sau. Sun gaskata cewa abubuwa masu kyau ko marar kyau da suke samin su a yanzu, sakamakon abubuwan da suka yi a rayuwarsu ta dā ne kafin a sake haifan su.
Akwai mutane da yawa da suke ganin cewa wannan ra’ayin ba gaskiya ba ne. Duk da haka, suna yin duba da tafin hannu, da taurari, da allo, da katuna, da dai sauransu. Suna ganin yin hakan zai sa su san yadda rayuwarsu za ta kasance a nan gaba.
WANE SAKAMAKO AKA SAMU?
Abubuwan da mutanen nan suke yi yana sa rayuwarsu ta yi kyau kuwa?
Ga labarin wani mai suna Hào daga Vietnam. Ya nemi taimako daga masu duba da taurari, ya bauta wa kakanninsa kuma ya bi wani tsari da ake kira feng shui don ya riƙa yin sa’a a rayuwa. Shin abin nema ya samu? Hào ya ce: “Na yi hasarar kuɗaɗe da yawa, na shiga bashi, iyalina babu zaman lafiya kuma na shiga baƙin ciki.”
Wani mai suna Qiuming daga ƙasar Taiwan shi ma ya yi imani da masu duba da taurari, da sake haihuwa, da feng shui da kuma bautar kakanni. Amma da ya bincika da kyau, sai ya ce: “Na gano cewa waɗannan ra’ayoyin da al’adun ba su jitu da juna ba kuma suna rikitar da mutum. Na kuma fahimci cewa yawancin abubuwan da masu duba da taurari suke faɗa, ba sa faruwa.” Batun sake haihuwa kuma fa? Qiuming ya ce: “Idan ba za ka iya tuna irin rayuwar da ka yi a dā ba, ta yaya za ka canja kuma ka yi rayuwa mai kyau a nan gaba?”
“Na gano cewa waɗannan ra’ayoyin da al’adun ba su jitu da juna ba kuma suna rikitar da mutum.”—QIUMING, DAGA ƘASAR TAIWAN
Kamar yadda labarin Hào da Qiuming da kuma wasu da yawa suka nuna, taurari, da bautar kakanni, da sake haihuwa, da makamantansu ba sa shafan yadda rayuwarmu za ta kasance. Shin, ba abin da za mu iya yi don rayuwarmu ta yi kyau a nan gaba ke nan?
Mutane da yawa suna ganin cewa idan suka je jami’a ko suka yi kuɗi, za su ji daɗin rayuwa a nan gaba. Shin waɗanda suka yi hakan sun sami abin da suke so?
^ sakin layi na 6 An canja sunayen wasu mutane a nan da kuma talifofi na gaba.
^ sakin layi na 16 Furucin nan yana cikin Nassosi Masu Tsarki a Galatiyawa 6:7. A yau ma, mutane da yawa sukan ce idan ka shuka abu mai kyau, za ka girbi abu mai kyau; idan kuma marar kyau ka shuka, shi za ka girba.