An Halicce Mu Ne don Mu Rayu Har Abada
WAYE ne a cikinmu ba ya so ya daɗe yana rayuwa a cikin kwanciyar hankali? Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance a ce mutane suna rayuwa har abada cikin farin ciki da ƙoshin lafiya! Za mu daɗe muna zama tare da waɗanda muke ƙauna, mu yi tafiye-tafiye zuwa duk inda muke so a duniya, kuma mu koyi yin wasu abubuwan da muke jin daɗin yin su.
Me ya sa mutane suke so su yi rayuwa har abada? Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Allah ne ya saka wannan muraɗin a zuciyarmu. (Mai-Wa’azi 3:11, New World Translation) Ya kuma ce, “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Da yake Allah yana ƙaunar mu, kana ganin zai saka muraɗin kasancewa har abada a zuciyarmu, da a ce ba za mu iya rayuwa har abada ba?
Ba wanda yake so ya mutu. Littafi Mai Tsarki ya ce mutuwa “abokiyar gaba” ce. (1 Korintiyawa 15:26) Wasu suna mutuwa tun suna ƙanana, wasu kuma bayan sun tsufa, amma a kwana a tashi, kowa zai mutu. Mutane da yawa ba sa so su tuna cewa wata rana za su mutu. Shin, akwai lokacin da mutuwa ba za ta ƙara kasancewa ba? Hakan zai yiwu kuwa?
YADDA MUKA SAN CEWA ALLAH YANA SO MU RAYU HAR ABADA
Idan ka ji cewa Allah bai taɓa nufan mutane da mutuwa ba, haka zai ba ka mamaki? A cikin Littafi Mai Tsarki, littafin Farawa ya tabbatar mana cewa nufin Allah shi ne, mutane su yi rayuwa har abada a duniya. Jehobah ya halicci duniyar nan cike da abubuwan da mutane suke bukata don su yi rayuwa mai inganci. Sai ya halicci mutum na farko wato, Adamu, kuma ya saka shi a cikin aljanna, wato, a lambun Adnin. Bayan haka, “Allah kuwa ya dubi dukan abin da ya yi, ya ga yana da kyau sosai.”—Farawa 1:26, 31.
Allah ya halicci Adamu ba tare da wani aibi ba. (Maimaitawar Shari’a 32:4) Matar Adamu wato, Hauwa’u ma an halicce ta ba tare da wani aibi ba. Jehobah ya gaya musu cewa: “Ku yi ta haifuwa . . . ku yalwata, ku ciccika duniya ku kuma sha ƙarfinta. Ku yi mulkin kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da kowane abu mai rai mai kai da kawowa cikin duniya.”—Farawa 1:28.
Ba shakka, zai ɗauki Adamu da Hauwa’u shekaru da yawa kafin su haifi ’ya’yan da za su cika duniyar nan. Hauwa’u za ta haifi ’ya’ya, ’ya’yan da ta haifa za su haifi nasu ’ya’yan har sai duniya ta cika da mutane kamar yadda Allah yake so. (Ishaya 45:18) Shin, Jehobah zai ba Adamu da Hauwa’u irin wannan aikin da a ce ya shirya cewa za su yi rayuwa na tsawon shekarun da za su ga ’ya’yansu da jikokinsu ne kawai, ba tare da sun ƙarasa aikin da Jehobah ya ba su ba?
Ka yi tunanin irin aikin da Allah ya ba wa Adamu na yin mulki bisa dabbobi. An ce ya ba kowace dabba suna, kuma hakan zai ɗauki lokaci sosai. (Farawa 2:19) Kafin ya zama da iko bisa dabbobi, sai ya koyi abubuwa game da dabbobin kuma ya fahimci yadda zai riƙa kula da su. Wannan ba abu ne da mutum zai iya yi a cikin ƙanƙanin lokaci ba.
Umurnin da Allah ya ba Adamu da Hauwa’u na cika duniya da kuma zama da iko bisa dabbobi ya nuna cewa Allah ya so su daɗe sosai suna rayuwa. Kuma Adamu ya yi rayuwa mai tsawo.
ALLAH YANA SO MUTANE SU RAYU HAR ABADA A CIKIN ALJANNA A DUNIYA
SUN YI SHEKARU DA YAWA
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a dā, mutane sun yi rayuwa mai tsawo fiye da mu a yau. Ya ce: ‘Dukan kwanakin Adamu shekara 930 ne.’ Bayan haka, ya ambata mutane shida da suka yi sama da shekara 900 a duniya! Mutanen su ne, Set, da Enosh, da Kenan, da Yared, da Metusela, da Nuhu. Dukansu sun yi rayuwa kafin Babban ambaliyar da aka yi a zamanin Nuhu, kuma Nuhu ya yi shekara 600 kafin ambaliyar ta auku. (Farawa 5:5-27; 7:6; 9:29) Ya aka yi suka rayu shekaru da yawa haka?
Duka mutanen nan sun rayu ne jim kaɗan bayan da Adamu da Hauwa’u suka zama ajizai. Wataƙila abin da ya sa suka daɗe suna rayuwa ke nan. Amma me mahaɗin yin rayuwa mai tsawo da ajizanci? Ta yaya za a kawar da mutuwa? Don samun amsoshin tambayoyin nan, muna bukatar mu san dalilin da ya sa muke tsufa da kuma mutuwa.