Za Ka Iya Yin Rayuwa Har Abada a Duniya
WANNAN ALKAWARIN ABIN SHA’AWA NE! Mahaliccinmu ya yi alkawari cewa zai sa mu yi rayuwa har abada a nan duniya. Amma mutane da yawa ba su yarda da hakan ba. Sun ce, ‘Dole ne kowa ya mutu domin haka rayuwa take.’ Wasu kuma sun gaskata cewa za a iya yin rayuwa har abada, amma ba a nan duniya ba. Sun ce kafin mutum ya yi rayuwa har abada, sai ya mutu kuma ya je sama. Mene ne ra’ayinka game da hakan?
Kafin ka faɗi naka ra’ayin, ka ɗan yi la’akari da yadda Littafi Mai Tsarki ya amsa waɗannan tambayoyin: Ta yaya yadda aka halicci ’yan Adam ya nuna irin tsawon rayuwar da aka nufe su da ita? Mene ne ainihin abin Allah ya nufa ga ’yan Adam da kuma duniya? Me ya sa mutane suke mutuwa?
’YAN ADAM DABAM SUKE
A cikin dukan abubuwa masu rai da Allah ya halitta, ’yan Adam sun bambanta da sauran. Ta yaya? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mutane ne kawai aka halicce su da “kamannin” Allah da ‘siffarsa.’ (Farawa 1:26, 27) Me hakan yake nufi? Hakan yana nufin cewa an halicci ’yan Adam da halayen da suka yi dai-dai da na Allah, kamar ƙauna da son adalci.
An kuma halicci ’yan Adam a hanyar da za su iya yin tunani da kyau kuma su iya bambanta tsakanin abu mai kyau da marar kyau. Ƙari ga haka, suna da marmarin koya game da Allah kuma su zama aminansa. Shi ya sa muna jin daɗin ganin halittun sama da ƙasa masu ban mamaki kuma muna jin daɗin zane-zane da kiɗi da kuma waƙa. Fiye da kome, ’yan Adam suna da gatan bauta wa Mahaliccin kome. Waɗannan halayen sun nuna irin bambancin da ke tsakanin ’yan Adam da sauran halittu masu rai.
Saboda haka, kana ganin Allah zai ba wa ’yan Adam irin halayen nan masu kyau kamar ƙauna da hikima da sauransu kuma ya ba su ikon ƙara inganta halayen idan yana son su yi rayuwa na ɗan lokaci kawai? Gaskiyar ita ce, Allah ya ba mu waɗannan halaye masu kyau don yana so mu ji daɗin rayuwa a nan duniya har abada.
AINIHIN ABIN DA ALLAH YA NUFA GA DUNIYA
Wasu sun ce Allah bai yi ’yan Adam don su yi rayuwa a nan duniya har abada ba. Sun ce Allah ya yi duniya ne don ya gwada ya ga mutanen da za su cancanci yin rayuwa a sama har abada da shi. Idan Kubawar Shari’a 32:4.
hakan gaskiya ne, shin hakan ba zai ɗora ma Allah alhakin mugunta da ta zama ruwan dare a yau ba? Da hakan zai yi dabam da halin Allah. Domin ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da shi: “Aikinsa cikakke ne, kuma dukan hanyoyinsa gaskiya ne. Allah mai aminci ne, ba ya ruɗu.”—Littafi Mai Tsarki ya bayyana abin da Allah ya nufa ga ’yan Adam, ya ce: “Saman sammai na Yahweh ne, amma duniya ya ba ’yan Adam.” (Zabura 115:16) Hakika, Allah ya halicci duniya da kyau don ta zama wurin zaman ’yan Adam har abada kuma ya saka abubuwa da yawa da za su sa mu ji daɗin rayuwa.—Farawa 2:8, 9.
“Saman sammai na Yahweh ne, amma duniya ya ba ’yan Adam.”—Zabura 115:16
Littafi Mai Tsarki ya sake bayyana abin da Allah ya nufa ga ’yan Adam. Ya ce wa iyayenmu na farko “ku yi ta haihuwa sosai ku yalwata, ku ciccika duniya ku kuma sha ƙarfinta. Ku yi mulkin . . . kowane abu mai rai mai kai da kawowa cikin duniya.” (Farawa 1:28) Hakan gata ce babba a gare su su kula da lambun kuma su faɗaɗa shi har iyakar duniya! Hakika, Adamu da Hawa’u ba su sa rai cewa wata rana za su koma yin rayuwa a sama ba, a maimako, sun yi begen yin rayuwa har abada a duniya.
ME YA SA MUKE MUTUWA?
Me ya sa muke mutuwa? Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa wani mala’ika wanda daga baya aka san shi da suna Shaiɗan Iblis, ya yi ƙoƙarin ya lalata abin da Allah ya shirya a lambun Adnin. Ta yaya?
Shaiɗan ya sa iyayenmu na farko wato Adamu da Hauwa’u su yi wa Jehobah tawaye. Da Shaiɗan ya yi musu ƙarya cewa Allah yana hana su ’yancin zaɓa ma kansu abu mai kyau ko mara kyau, sun yarda da shi kuma suka juya ma Allah baya. Me ya zama sakamakon hakan? Sun mutu a ƙarshe kamar yadda Allah ya gaya musu. Hakan ya sa ba su rayu har abada a duniya ba.—Farawa 2:17; 3:1-6; 5:5.
Rashin biyayya da Adamu da Hauwa’u suka yi ya sa ’yan Adam cikin damuwa har zuwa zamaninmu. Kalmar Allah ta ce: “To, kamar yadda zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, zunubin nan kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta bi ta shiga dukan ’yan Adam.” (Romawa 5:12) Saboda haka, ba gaskiya ba ne cewa muna mutuwa don Allah ya kadara hakan ba. Amma, zunubin da muka gāda daga wurin Adamu da Hauwa’u ne ya jawo hakan.
ZA KA IYA YIN RAYUWA HAR ABADA A DUNIYA
Rashin biyayyar da iyayenmu suka yi a lambun Adnin bai canja nufin Allah ga wannan duniyar da kuma mutane ba. Da yake Allah yana ƙaunar mu sosai kuma shi mai adalci ne, ya yi tanadi don mu sami ’yanci daga zunubi da mutuwa da muka gāda. Manzo Bulus ya ce: “Gama sakamakon zunubi shi ne mutuwa, amma kyautar Allah ita ce rai na har abada ta wurin Almasihu Yesu Ubangijinmu.” (Romawa 6:23) Ƙauna ce ta sa Allah “ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin dukan wanda ya ba da gaskiya gare shi kada ya halaka, amma ya sami rai na har abada.” (Yohanna 3:16) Yadda Yesu ya amince ya ba da ransa fansa ne ya ceto mu daga bala’in da Adamu ya saka mu a ciki. a
Nan ba da daɗewa ba, alkawarin Allah game da Aljanna a nan duniya zai cika. Za ka iya zama cikin waɗanda za su ji daɗin zama a Aljannar idan ka bi shawarar nan: “Ku shiga ta ƙaramar ƙofa, gama ƙofar zuwa halaka tana da fāɗi. Kuma hanyarta tana da sauƙin bi, masu shiga cikinta kuma suna da yawa. Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce. Hanyarta kuma da wuyar bi. Masu binta kuma ba su da yawa.” (Matiyu 7:13, 14) Babu shakka, kai ne za ka zaɓi yadda rayuwarka za ta kasance a nan gaba. To, wane zaɓi za ka yi?
a Don ƙarin bayani a kan yadda za ka amfana daga fansar, ka duba darasi na 27 na littafin nan Ka Ji Ɗadin Rayuwa Har Abada! Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi. Za ka iya saukar da shi kyauta a www.jw.org/ha