Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Matsalar Ƙwaƙwalwa a Faɗin Duniya

Matsalar Ƙwaƙwalwa a Faɗin Duniya

“Ina yawan damuwa ko da ni kaɗai ne nake zaune a ɗaki.”

“Idan na ji jikina kalau nakan soma damuwa, domin na san cewa idan ina farin ciki sosai baƙin ciki ne zai biyo baya.”

“Nakan yi ƙoƙari in mai da hankali ga abubuwan da ke faruwa kowace rana, amma a wasu lokuta nakan soma damuwa game da abubuwa da yawa.”

Mutanen da suke fama da matsalar ƙwaƙwalwa ne suka faɗi abubuwan nan. Shin, hakan ya taɓa faruwa da kai ko wanda ka sani?

A gaskiya ba kai kaɗai ba ne kake fama da wannan matsalar. Matsalar ƙwaƙwalwa takan shafi mutane da yawa ko kuma waɗanda suke ƙauna.

Babu shakka, muna rayuwa a lokacin da ake shan “wahala sosai” kuma hakan yana jawo damuwa iri-iri. (2 Timoti 3:1) A wani nazari da aka yi, an gano cewa a faɗin duniya, mutum ɗaya cikin takwas ne yake fama da matsalar ƙwaƙwalwa. A 2020, a lokacin annobar korona an sami ƙarin mutane wajen miliyan 78 da suke fama da ciwon damuwa da kuma matsalar ƙwaƙwalwa.

Ko da yake yana da muhimmanci ka san yawan mutanen da suke fama da matsalar nan, ya fi muhimmanci ka san yadda kai da waɗanda kake ƙauna za ku kasance da ƙoshin lafiya.

Mene ne ake nufi da lafiyar ƙwaƙwalwa?

Idan mutum bai da matsalar ƙwaƙwalwa yana iya yin abubuwa daidai yadda ya kamata. Mutumin ya san yadda zai bi da duk yanayin da ya shiga, yana yin aiki da kyau kuma hankalinsa a kwance yake.

Matsalar ƙwaƙwalwa . . .

  • BA sakamakon kasawar mutum ba ne.

  • MATSALA CE da ke jefa mutum cikin damuwa, kuma takan rikitar da tunanin mutum da yadda yake yin abubuwa.

  • Takan sa ya zama da wuya mutum ya ƙulla abota da kuma gudanar da abubuwa na yau da kullum.

  • Tana iya shafan kowa ko da manya ne ko yara ko da yaya alꞌadarsu take ko launin fatarsu ko ƙabilarsu ko addininsu ko iliminsu ko kuma wadatarsu.

Yadda mai fama da matsalar ƙwaƙwalwa zai sami taimako

Idan mutum ya soma gani wasu canje-canje a halayensa ko yadda yake barci ko cin abinci ko yana yawan damuwa ko baƙin ciki, zai dace ya nemi taimakon likita don a gano abin da ya jawo hakan kuma a san yadda za a magance shi. Amma a ina ne za ka sami taimako?

Mutum mafi hikima da ya taɓa rayuwa wato, Yesu Almasihu ya ce: “Masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya.” (Matiyu 9:12) Waɗanda suke rashin lafiya kuma suka je asibiti aka ba su magani, za su iya samun sauƙi kuma su yi farin ciki. Ba zai dace irin mutanen nan su yi jinkirin neman taimako ba, musamman idan alamun sun yi tsanani ko kuma sun daɗe. a

Ko da yake Littafi Mai Tsarki ba littafin kiwon lafiya ba ne, abubuwan da ke ciki za su iya taimakawa a batun lafiyar ƙwaƙwalwa. Za mu so ka karanta talifofi na gaba da za su tattauna yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana idan muna fama da matsalar ƙwaƙwalwa.

a Hasumiyar Tsaro ba ta ba da shawara a kan irin jinyar da mutum zai zaɓa. Kowane mutum ne zai yi tunani sosai a kan irin jinyar da zai zaɓa kafin ya yanke shawara.