TALIFIN NAZARI NA 24
‘Ka Ba Ni Zuciya Daya, Don In Girmama Sunanka’
Ka “ba ni zuciya ɗaya, domin in girmama Sunanka. Ya Ubangiji Allahna, zan yabe ka da dukan zuciyata.”—ZAB. 86:11, 12.
WAƘA TA 7 Jehobah Ne Ƙarfinmu
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1. Mene ne tsoron Allah yake nufi, kuma me ya sa yake da muhimmanci ga waɗanda suke ƙaunar Jehobah?
KIRISTOCI suna ƙaunar Allah kuma suna tsoron shi. Wasu suna ganin cewa yin waɗannan abubuwa biyu a lokaci ɗaya ba zai yiwu ba. Amma ba irin tsoron da ke sa mutane fargaba muke magana a kai ba. Za mu tattauna wani tsoro na musamman. Mutanen da ke jin irin wannan tsoron suna daraja Allah sosai. Ba sa so su ɓata wa Allah rai domin ba sa so su ɓata dangantakarsu da shi.—Zab. 111:10; K. Mag. 8:13.
2. Waɗanne abubuwa biyu ne za mu tattauna daga abubuwan da Sarki Dauda ya faɗa a Zabura 86:11?
2 Karanta Zabura 86:11. Yayin da kake yin tunani a kan waɗannan kalmomi, za ka ga cewa Sarki Dauda ya san muhimmancin jin tsoron Allah. Bari mu tattauna yadda za mu iya yin amfani da abubuwan da Dauda ya faɗa a addu’arsa. Na ɗaya, za mu tattauna dalilin da ya sa muke bukatar mu riƙa daraja sunan Allah. Na biyu, za mu tattauna yadda za mu nuna cewa muna jin tsoron Allah a rayuwarmu.
DALILINMU NA DARAJA SUNAN ALLAH
3. Mene ne ya taimaka wa Musa ya daraja sunan Allah?
3 Ka yi tunanin yadda Musa ya ji a lokacin da yake kan dutse kuma ya ga ɗaukakar Jehobah. Littafin nan Insight on the Scriptures ya ce: “Babu shakka wannan ne abu mafi ban-mamaki da ɗan Adam ya taɓa gani kafin Yesu ya zo duniya.” Musa ya ji furucin nan: “Ni ne Ubangiji, Ubangiji Allah mai jinƙai, mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna, mai gaskiya. Ni ne mai nuna ƙauna ga dubbai, mai gafarta mugunta, da laifi, da zunubi.” (Fit. 33:17-23; 34:5-7, Littafi Mai Tsarki) A lokacin da Musa ya kira sunan Jehobah, wataƙila yakan tuna abin da ya faru a lokacin. Hakan ya sa ya gargaɗi Isra’ilawa cewa: “Ku ji tsoron Sunan nan mai ɗaukaka mai ban tsoro.”—M. Sha. 28:58.
4. Mene ne zai taimaka mana mu riƙa daraja Jehobah sosai?
4 A duk lokacin da muka yi tunani game da sunan nan Jehobah, ya kamata mu yi tunani a kan mai sunan. Muna bukatar mu yi tunani a kan ikonsa da hikimarsa da adalcinsa da kuma ƙaunarsa. Idan muka yi tunani a kan waɗannan halaye da kuma wasu, hakan zai taimaka mana mu riƙa daraja Jehobah sosai.—Zab. 77:11-15.
5-6. (a) Mene ne ma’anar sunan Allah? (b) Kamar yadda Fitowa 3:13, 14 da kuma Ishaya 64:8 suka nuna, a waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake sa abubuwa su faru?
5 Mene ne ma’anar sunan Allah? Masana da yawa sun yarda cewa sunan nan Jehobah yana nufin “Yana Sa Ya Kasance.” Ma’anar sunan nan ta nuna mana cewa babu abin da zai iya hana Jehobah cika nufinsa, kuma duk abin da yake so ya faru zai faru. Ta yaya?
6 Jehobah yana cika nufinsa ta wajen zama duk abin da ake bukata don hakan ya faru. (Karanta Fitowa 3:13, 14.) A littattafanmu, ana yawan ƙarfafa mu mu riƙa yin tunanin wannan halin Jehobah mai ban-mamaki. Ƙari ga haka, Jehobah yana iya sa bayinsa ajizai su zama duk abin da ake bukata don su bauta masa kuma su cika nufinsa. (Karanta Ishaya 64:8.) A waɗannan hanyoyin ne Jehobah yake sa a cika nufinsa. Babu abin da zai iya hana shi cika nufinsa.—Isha. 46:10, 11.
7. Ta yaya za mu ci gaba da nuna cewa muna daraja Jehobah?
7 Muna iya nuna godiya ga Jehobah ta yin bimbini a kan abubuwan da ya yi mana da kuma waɗanda yake sa mu yi. Alal misali, abubuwan da Jehobah ya halitta suna burge mu sosai sa’ad da muka Zab. 8:3, 4) Idan muka yi bimbini a kan abin da Jehobah ya sa mu zama domin mu cika nufinsa, hakan zai sa mu daɗa daraja shi. Hakika, sunan nan Jehobah yana sa mu ji tsoron sa! Wannan sunan ya ƙunshi dukan halayen Jehobah da abubuwan da ya yi da kuma abubuwan da zai yi.—Zab. 89:7, 8.
yi tunani a kansu. (“GAMA ZAN YI SHELAR SUNAN YAHWEH”
8. Kamar yadda Maimaitawar Shari’a 32:2, 3 suka nuna, yaya Jehobah yake ɗaukan sunansa?
8 Jim kaɗan kafin Isra’ilawa su shiga Ƙasar Alkawari, Jehobah ya koya wa Musa wata waƙa. (M. Sha. 31:19) Musa kuma ya koya wa Isra’ilawa waƙar. (Karanta Maimaitawar Shari’a 32:2, 3.) Yayin da muka yi tunani a kan aya ta 2 da 3, za mu ga cewa Jehobah ba ya so a ɓoye sunansa, wato a riƙa ganin cewa sunan yana da tsarki sosai, don haka bai kamata a riƙa amfani da shi ba. Jehobah yana so kowa ya san sunansa! Isra’ilawa sun yi farin ciki sosai sa’ad da Musa ya koya musu game da Jehobah da kuma Sunansa mai ban ɗaukaka! Kamar yadda ruwa yake taimaka wa shuke-shuke, abin da Musa ya koya musu ya sa su kasance da bangaskiya sosai kuma ya ƙarfafa su. Ta yaya za mu tabbatar cewa haka koyarwarmu take?
9. Ta yaya za mu taimaka wa mutane su tsarkake sunan Allah?
9 Sa’ad da muke wa’azi, muna iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki don mu nuna wa mutane sunan nan Jehobah. Muna iya ba su littattafai ko bidiyoyi ko kuma abubuwan da aka wallafa a dandalinmu da ke ɗaukaka sunan Allah. Sa’ad da muke wurin aiki ko makaranta ko kuma sa’ad da muke tafiya, muna iya samun zarafin yi wa mutane wa’azi game da Allah da kuma halayensa. Muna iya gaya wa mutanen da muka haɗu da su nufin Jehobah ga ’yan Adam da kuma duniya. Sa’ad da suka ji waɗannan abubuwan, za su ga cewa Jehobah yana ƙaunar su sosai. Yayin da muke gaya wa mutane gaskiya game da Jehobah, muna tsarkake sunansa. Muna taimaka wa mutane su fahimci cewa an koya musu ƙaryace-ƙaryace game da Jehobah. Abubuwan da muke koya wa mutane daga Littafi Mai Tsarki zai ƙarfafa su.—Isha. 65:13, 14.
10. Me ya sa ba koya wa mutane game da ƙa’idodin Jehobah kaɗai muke bukatar yi ba?
10 Sa’ad da muke nazarin Littafi Mai Tsarki da ɗalibanmu, ya kamata mu taimaka musu su san sunan Jehobah kuma su riƙa amfani da sunan. Ƙari ga haka, muna so mu taimaka musu so san Jehobah sosai. Ba za mu cim ma hakan ba idan muka koya musu umurni da dokokin da ke Littafi Mai Tsarki kaɗai. Ɗalibi yana iya koyon dokokin Allah kuma ya soma son dokokin. Amma ɗalibin zai yi wa Jehobah biyayya domin yana ƙaunar sa ne? Ka tuna cewa Hauwa’u ta san dokar Allah, amma ita da Adamu ba su ƙaunaci wanda ya ba da dokar ba. (Far. 3:1-6) Don haka, ba koya wa mutane game da ƙa’idodin Jehobah kaɗai muke bukatar mu yi ba.
11. Sa’ad da muke koya wa ɗalibanmu dokoki da ƙa’idodin Allah, ta yaya za mu taimaka musu su soma ƙaunar Jehobah?
11 Dokoki da ƙa’idodin Jehobah suna amfanar mu. (Zab. 119:97, 111, 112) Amma wataƙila ɗalibanmu ba za su fahimci hakan ba idan ba su san cewa Jehobah ya ba da waɗannan dokokin ne domin yana ƙaunar mu ba. Don haka, muna iya tambayar ɗalibinmu: “Me ya sa kake gani cewa Allah ya gaya wa bayinsa su yi wannan ko kuma kada su yi wannan? Mene ne hakan yake koya maka game da Jehobah?” Za mu ratsa zuciyar ɗalibanmu idan muka taimaka musu su riƙa tunani game da Jehobah kuma su ƙaunaci sunansa. Ɗalibanmu za su so bin dokokinsa kuma su riƙa ƙaunar Jehobah wanda ya ba da dokokin. (Zab. 119:68) Hakan zai taimaka musu su kasance da bangaskiya kuma su iya jimre matsalolin da za su fuskanta.—1 Kor. 3:12-15.
“ZA MU BI YAHWEH ALLAHNMU HAR ABADA ABADIN”
12. Ta yaya zuciyar Dauda ta rabu biyu, kuma wane sakamako ne hakan ya jawo?
12 Furucin nan “ba ni zuciya ɗaya” da Sarki Dauda ya rubuta a littafin Zabura 86:11 yana da muhimmanci sosai. Sarki Dauda ya fahimci cewa yana da sauƙi zuciyar mutum ta rabu biyu. Akwai wata rana da yake saman gidansa kuma ya hango matar wani tana wanka. A lokacin, zuciyar Dauda ta rabu biyu. Ya san dokar Jehobah cewa: “Ba za ka yi ƙwaɗayin matar maƙwabcinka” ba. (Fit. 20:17) Amma Dauda ya ci gaba da kallon ta don zuciyarsa ta rabu biyu. Yana sha’awar Bath-sheba, duk da haka, yana so ya faranta ran Jehobah. Ko da yake Dauda ya yi shekaru da yawa yana ƙaunar Jehobah da kuma jin tsoronsa, ya nuna son kai ta wajen barin sha’awar jikinsa ta sha ƙarfinsa. Saboda haka, Dauda ya yi abin da bai dace ba. Ya ɓata sunan Allah. Ƙari ga haka, Dauda ya jawo wa mutanen da ba su yi wani laifi ba matsaloli, har da iyalinsa.—2 Sam. 11:1-5, 14-17; 12:7-12.
13. Ta yaya muka san cewa daga baya Dauda ya kasance da zuciya ɗaya?
13 Jehobah ya yi masa horo, kuma Dauda ya sake ƙulla dangantaka mai kyau da shi. (2 Sam. 12:13; Zab. 51:2-4, 17) Dauda ya tuna matsaloli da ƙunci da ya fuskanta sa’ad da zuciyarsa ta rabu biyu. Jehobah ya taimaka wa Dauda ya kasance da zuciya ɗaya ne? E, domin daga baya Kalmar Allah ta ce Dauda ya “miƙa zuciyarsa gaba ɗaya ga Yahweh Allahnsa.”—1 Sar. 11:4; 15:3.
14. Me muke bukatar mu tambayi kanmu, kuma me ya sa?
14 Misalin Dauda yana da ban-ƙarfafa kuma gargaɗi ne a gare mu. Ya kamata bayin Allah su koyi darasi daga abin da ya faru da Dauda. Ko da bai daɗe muka soma bauta wa Jehobah ba ko kuma mun yi shekaru muna bauta masa, muna bukatar mu tambayi kanmu, ‘Ina
guje wa ƙoƙarin da Shaiɗan yake yi don ya raba zuciyata?’15. Ta yaya tsoron Allah zai kāre mu sa’ad da muka ga hoton lalata?
15 Alal misali, mene ne za ka yi idan an nuna abu a telibijin ko kuma a Intane da zai sa ka soma sha’awar yin lalata? Yana da sauƙi mu yi tunani cewa hoton ko kuma bidiyon ba na batsa ba ne. Amma wataƙila abin da Shaiɗan yake so ya yi amfani da shi ke nan don ya raba zuciyarka. (2 Kor. 2:11) Muna iya kwatanta wannan hoto da bakin gatarin da mutum yake faskare da shi. Da farko, bakin gatarin da ke da kaifi ne zai ɗan sare itacen. Sa’ad da mutumin ya ci gaba da yin faskaren sai itacen ya rabu biyu. Hotunan lalata suna kama da bakin gatarin. Kallon irin waɗannan hotunan zai iya zama kamar ba shi da illa, amma da shigewar lokaci, yana iya sa mu yi zunubi ga Jehobah. Don haka, kada ka bari abin da bai dace ba ya shiga zuciyarka. Ka kasance da zuciya ɗaya don ka nuna cewa kana tsoron Jehobah!
16. Sa’ad da muke fuskantar jarrabawa, waɗanne tambayoyi za mu yi wa kanmu?
16 Ban da amfani da hotunan lalata, Shaiɗan yana yin amfani da wasu abubuwa don ya sa mu yi zunubi. Mene ne za mu yi? Yana da sauƙi mu soma tunani cewa waɗannan abubuwan ba zunubi ba ne. Alal misali, muna iya tunani cewa: ‘Ba za a mini yankan zumunci don na yi wannan abin ba, don hakan, yin sa ba laifi ba ne.’ Irin wannan tunanin bai dace ba. Zai fi dacewa mu tambayi kanmu: ‘Shaiɗan yana so ya yi amfani da wannan abin don ya raba zuciyata ne? Zan ɓata sunan Jehobah ne idan na bi sha’awar banza? Yin Yaƙ. 1:5) Yin hakan zai sa ka sami kāriya sosai. Zai taimaka maka ka guji jarrabawa, kamar yadda Yesu ya yi sa’ad da ya ce: “Tafi daga nan kai Shaiɗan!”—Mat. 4:10.
wannan abin zai sa in kusaci Jehobah ne ko kuma in nisanta kaina da shi?’ Ka yi bimbini a kan irin waɗannan tambayoyin. Ka yi addu’a don ka sami amsar waɗannan tambayoyin ba tare da ka ruɗi kanka ba. (17. Me ya sa bai dace zuciyarmu ta rabu biyu ba? Ka ba da misali.
17 Za mu cutar da kanmu idan zuciyarmu ta rabu biyu. A ce a rukunin ’yan wasa akwai wasu da ba sa ba da haɗin kai. Wasu suna son yin suna, wasu ba sa bin ƙa’idodin wasan, wasu kuma sun raina kocin. Irin rukunin nan ba za su yi nasara a wasan ba. Amma rukunin da suke da haɗin kai suna iya yin nasara a wasan. Zuciyarka tana iya zama kamar rukunin da suke da haɗin kai idan tunaninka da sha’awoyinka da kuma abubuwan da kake so suna ɗaukaka Jehobah. Ka tuna cewa Shaiɗan yana so ya raba zuciyarka. Ba ya son tunaninka da sha’awoyinka da kuma abubuwan da kake so su jitu da ra’ayin Jehobah. Amma kana bukatar ka kasance da zuciya ɗaya domin ka bauta wa Jehobah. (Mat. 22:36-38) Kada ka bari Shaiɗan ya raba zuciyarka!
18. Kamar yadda littafin Mika 4:5 ya faɗa, mene ne ka ƙuduri niyyar yi?
18 Ka yi addu’a ga Jehobah kamar yadda Dauda ya yi. Ya ce: “Ba ni zuciya ɗaya, domin in girmama sunanka.” Ka yi iya ƙoƙarinka don ka yi amfani da wannan addu’ar a rayuwarka. A kowace rana, ka ƙuduri niyyar nuna cewa duk shawarwarinka suna daraja sunan Allah. Idan ka yi hakan, za ka ɗaukaka sunan Allah a matsayin ka na Mashaidin Jehobah. (K. Mag. 27:11) Kuma za mu iya yin furucin nan da annabi Mika ya yi. Ya ce: “Za mu bi Yahweh Allahnmu har abada abadin.”—Mik. 4:5.
WAƘA TA 41 Allah Ka Ji Roƙona
^ sakin layi na 5 A wannan talifin, za mu tattauna addu’ar da Sarki Dauda ya yi da ke littafin Zabura 86:11, 12. Mene ne jin tsoron sunan nan Jehobah yake nufi? Me ya sa muke bukatar mu daraja wannan sunan? Ta yaya jin tsoron Allah zai taimaka mana mu guji yin abin da bai dace ba sa’ad da aka jarraba mu?
^ sakin layi na 53 BAYANI A KAN HOTUNA: Musa ya koya wa Isra’ilawa waƙar da ke ɗaukaka Jehobah.
^ sakin layi na 57 BAYANI A KAN HOTUNA: Hauwa’u ba ta guji sha’awar banza ba. Amma muna ƙin hotuna da saƙonni da ke ta da sha’awoyin banza da za su iya ɓata sunan Allah.