Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Goyi Bayan Sarautar Jehobah!

Ka Goyi Bayan Sarautar Jehobah!

“Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu.”​—R.YOH. 4:11.

WAƘOƘI: 112, 133

1, 2. Wane tabbaci ne ya kamata kowannenmu ya kasance da shi? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

KAMAR yadda aka ambata a talifin da ya gabata, Iblis ya yi da’awa cewa Jehobah bai cancanci ya yi wa ’yan Adam sarauta ba, don ba zai yi hakan yadda ya dace ba. Ƙari ga haka, Shaiɗan ya ce mutane za su fi jin daɗi idan suka yi sarauta da kansu. Hakan gaskiya ne? Da a ce mutane da gaske za su iya sarauta da kansu kuma su yi rayuwa har abada, shin za su fi yin farin ciki idan ba Allah ba ne sarkinsu? Shin za ka fi yin farin ciki idan za ka yi rayuwa har abada ba tare da ja-gorancin Allah ba?

2 Mu da kanmu ne za mu iya ba da amsoshin waɗannan tambayoyin. Ya kamata kowannenmu ya yi tunani a kansu sosai. Idan muka yi hakan, za mu ga cewa sarautar Jehobah ne ta fi dacewa kuma muna bukatar mu goyi bayansa da dukan zuciyarmu. Littafi Mai Tsarki ya ba mu ƙwaƙƙwarar dalilin da ya sa za mu yi hakan. Alal misali, ka yi la’akari da abin da ya bayyana mana da ya nuna cewa sarautar Jehobah ce ta fi dacewa.

JEHOBAH NE YA CANCANCI YIN SARAUTA

3. Me ya sa Jehobah ne kaɗai ya dace ya yi sarauta?

3 Jehobah ne ya cancanci ya yi sarauta domin shi ne maɗaukaki da kuma Mahalicci. (1 Laba. 29:11; A. M. 4:24) A wahayin da aka ambata a littafin Ru’ya ta Yohanna 4:​11, an ga abokan sarautar Kristi guda 144,000 suna cewa: “Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.” Hakika, da yake Jehobah ne ya halicci dukan abubuwa, ya dace ya yi wa mutane da kuma halittun da ke sama sarauta.

4. Me ya sa kasancewa da ’yanci bai ba mu damar yin tawaye ga Allah ba?

4 Shaiɗan bai halicci kome ba, saboda haka ba zai dace ya yi sarautar sama da kuma duniya ba. Shi da kuma iyayenmu na farko sun nuna girman kai sa’ad da suka yi tawaye ga sarautar Jehobah. (Irm. 10:23) Hakika, da yake su halittu ne da suke da ’yancin yin abin da suke so, suna iya zaɓa su yi zaman kansu. Amma shin hakan ya ba su damar ƙin sarautar Jehobah? A’a. ’Yanci yana ba wa mutum damar zaɓan abin da ya dace a kowace rana. Duk da haka, bai kamata hakan ya sa su yi tawaye ga Mahaliccinsu ba. Hakika, yin tawaye ga Jehobah ya nuna cewa ba ma amfani da ’yancinmu a hanyar da ta dace. A matsayinmu na ’yan Adam, muna bukatar sarautar Jehobah da ja-gorancinsa.

5. Me ya sa muka tabbata cewa duk wata shawarar da Allah ya tsai da ya dace?

5 Wani dalili kuma da ya sa Jehobah ne ya dace ya yi sarauta shi ne yana nuna ikonsa a hanyar da ta dace. Ya ce: “Ni ne Ubangiji mai-aikin rahama, da shari’a, da adalci, a cikin duniya: gama cikin waɗannan abu ni ke murna, in ji Ubangiji.” (Irm. 9:24) Jehobah ba ya bukatar dokokin ’yan Adam don ya san abin da ya dace. Maimakon haka, yana kafa wa mutane dokoki bisa abin da ya dace. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Adalci da shari’a su ne tushen kursiyinsa,’ saboda haka, muna da tabbaci cewa dukan dokokinsa da ƙa’idodinsa da kuma shawarwarinsa sun dace. (Zab. 89:14; 119:128) Shaiɗan ba zai iya sa duniya ta yi zaman lafiya ba ko da yake ya ce bai dace Jehobah ya yi sarauta ba.

6. Wane ne yake da ilimin yin sarautar wannan duniya? Ka yi bayani.

6 Ƙari ga haka, ya dace Jehobah ya yi sarauta don yana da ilimi da hikimar da ake bukata don a kula da sama da kuma duniya. Alal misali, Allah ya ba Ɗansa ikon warkar da cututtuka da ba likitan da zai iya warkarwa. (Mat. 4:​23, 24; Mar. 5:​25-29) A gaban Jehobah, wannan ba mu’ujiza ba ne don ya san yadda jiki yake aiki kuma zai iya warkar da kowace irin matsala da jikin ya samu. Ban da haka ma, zai iya ta da matattu kuma ya hana bala’i faruwa.

7. Ta yaya hikimar Jehobah ta fi na duniya da Shaiɗan ke sarautarsa?

7 Duniyar da Shaiɗan yake sarautarta ba za ta iya sa mutane zaman lafiya ba. Jehobah ne kaɗai zai iya sa mutane su yi zaman lafiya. (Isha. 2:​3, 4; 54:13) Yayin da muke koya game da ilimi da hikimar Jehobah, za mu ji yadda manzo Bulus ya ji, kuma ya ce: “Oh! zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa! ina misalin wuyan binciken shari’unsa, al’amuransa kuma sun fi gaban a bincika su duka.”​—Rom. 11:33.

SARAUTAR JEHOBAH CE TA FI KYAU

8. Yaya kake ji game da yadda Jehobah yake sarauta?

8 Kamar yadda muka gani, Littafi Mai Tsarki ya nuna sarai cewa Jehobah ne ya dace ya yi sarauta. Ya nuna mana dalilin da ya sa shi ne sarki mafi kyau. Wani dalili shi ne cewa yana ƙaunar waɗanda yake sarauta a kansu. Hakika, muna kusantarsa don yadda yake sarauta. Yana “da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai da gaskiya.” (Fit. 34:6) Allah yana mutunta da kuma daraja bayinsa. Yana kula da mu da kyau fiye da yadda muke kula da kanmu. Iblis ya yi ƙarya sa’ad da ya ce Jehobah ba ya son abin da zai amfane bayinsa masu aminci. Me ya sa muka ce hakan? Domin Allah ya ba da Ɗansa da yake ƙauna don mu samu begen yin rayuwa har abada!​—Karanta Zabura 84:11; Romawa 8:32.

9. Ta yaya muka san cewa Jehobah ya damu da kowannenmu?

9 Jehobah yana ƙaunar dukan mutanensa. Amma yana damuwa da kowannenmu. Alal misali, ka yi la’akari da abin da ya faru a cikin shekaru ɗari uku da Jehobah ya yi amfani da alƙalai don ya ceci al’ummar Isra’ila daga masu zaluntarsu. Yayin da hakan yake faruwa, Jehobah ya lura da Ruth wadda ba ’yar Isra’ila ba ce amma ta soma bauta masa. Jehobah ya sa Ruth ta samu miji kuma ya albarkace ta da ɗa. Ƙari ga haka, sa’ad da aka ta da Ruth daga mutuwa, za ta ji cewa Almasihu ya fito daga zuriyarta. Kuma za ta yi farin ciki sosai idan ta ji cewa an rubuta labarinta a wani littafi mai ɗauke da sunanta a Littafi Mai Tsarki!​—Ruth 4:13; Mat. 1:​5, 16.

10. Me ya sa sarautar Jehobah ba ta sa mutane su sha wahala?

10 Yadda Jehobah yake sarauta ba ya sa mutane su sha wahala. Maimakon haka, tana sa mutane su yi farin ciki. (2 Kor. 3:17) Dauda ya ce: “Daraja da ɗaukaka suna gabansa [Allah]; ƙarfi da farinciki suna cikin wurinsa.” (1 Laba. 16:​7, 27) Wani marubucin zabura mai suna Ethan ya ce: “Mai-albarka ne wannan dangi da ya san muryan nan ta murna: Suna tafiya, ya Ubangiji, a cikin hasken fuskarka. Cikin sunanka suna murna dukan yini: Cikin adalcinka kuma sun ɗaukaka.”​—Zab. 89:​15, 16.

11. Ta yaya za mu ƙara kasancewa da tabbaci cewa sarautar Jehobah ce ta fi kyau?

11 Idan muna bimbini a kai a kai game da nagartan Jehobah, hakan zai sa mu ƙara kasancewa da tabbaci cewa sarautarsa ce ta fi kyau. Za mu ji kamar wani marubucin zabura da ya ce: “Yini ɗaya cikin gidajenka ya fi dubu.” (Zab. 84:10) Hakan gaskiya ne, da yake Jehobah ne ya halicce mu, ya san abin da muke bukata don mu yi farin ciki, kuma yana biyan bukatunmu. Duk wani abu da Jehobah yake son mu yi don amfaninmu ne. Ko da muna bukatar yin wasu sadaukarwa, za mu yi farin ciki idan muka yi biyayya ga Jehobah.​—Karanta Ishaya 48:17.

12. Mene ne ainihin dalilin da ya sa muke goyon bayan sarautar Jehobah?

12 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa bayan Sarautar Yesu na Shekara Dubu, wasu mutane za su yi wa Jehobah tawaye. (R. Yoh. 20:​7, 8) Mene ne zai sa su yi hakan? A wannan lokacin bayan an saki Iblis daga kurkuku, zai sa mutane su zama masu son kai kamar yadda yake yaudararsu kafin a ɗaure shi. Zai yi ƙoƙari ya tabbatar wa mutane cewa za su yi rayuwa har abada ko da ba sa yi wa Jehobah biyayya. Amma hakan ba gaskiya ba ne. Don haka, ya kamata mu tambayi kanmu: Shin zan gaskata da wannan ƙaryar? Ba za mu saurari wannan ƙaryar ba idan muna ƙaunar Jehobah kuma muna bauta masa saboda nagartarsa kuma don shi ne ya dace ya yi sarauta. Ƙari ga haka, muna so mu yi rayuwa kawai sa’ad da Jehobah yake sarauta don yana ƙaunar mutanen da yake sarauta a kansu.

KA GOYI BAYAN SARAUTAR JEHOBAH DA AMINCI

13. Ta yaya yin koyi da Allah ya nuna cewa muna goyon bayansa?

13 Hakika, ya dace mu goyi bayan sarautar Jehobah da dukan zuciyarmu. Kamar yadda muka gani, ya dace Jehobah ya yi sarauta, kuma sarautarsa ce ta fi kyau. Za mu goyi bayan sarautar Jehobah ta wajen kasancewa da aminci ga Allah da kuma yin koyi da shi. A wace hanya ce kuma za mu goyi bayan sarautar Jehobah? Za mu yi hakan ta wajen yin abubuwan da yake so. Ƙari ga haka, idan muna iya ƙoƙarinmu don mu riƙa abubuwa yadda Jehobah yake yi, muna nuna cewa muna son yadda yake sarauta kuma muna goyon bayansa.​—Karanta Afisawa 5:​1, 2.

14. Ta yaya dattawa da magidanta za su yi koyi da Jehobah?

14 Sa’ad da muke nazarin Littafi Mai Tsarki, mun koya cewa Jehobah yana nuna ikonsa a hanyar da ta dace. Saboda haka, magidanta da dattawa da suke goyon bayan sarautar Jehobah ba za su riƙa matsa wa mutane ba. Maimakon haka, za su yi koyi da Jehobah kamar yadda Bulus ya yi koyi da shi da kuma Ɗansa. (1 Kor. 11:⁠1) Bulus bai kunyantar da wasu ba ko kuma matsa musu su yi abin da ya dace. Maimakon haka, ya roƙe su su yi hakan. (Rom. 12:1; Afis. 4:1; Fil. 8-10) Ta yin hakan, Bulus ya yi koyi da Jehobah. Idan muka bi da mutane yadda ya dace, muna goyon bayan sarautar Jehobah.

15. Ta yaya muke goyon bayan sarautar Jehobah ta wajen daraja waɗanda suke yi mana ja-goranci?

15 Ta yaya za mu nuna muna miƙa kai ga waɗanda suke ja-goranci? Muna goyon bayan sarautar Jehobah ta wajen ba su haɗin kai. Ko da ba mu fahimci ko kuma amince da wata shawara da aka tsai da ba, har ila zai dace mu goyi bayan sarautar Jehobah. Mutanen duniya ba sa yin haka, amma za mu yi hakan idan mun amince da sarautar Jehobah. (Afis. 5:​22, 23; 6:​1-3; Ibran. 13:17) Ƙari ga haka, domin Allah yana son abin da zai amfane mu, za mu amfana idan muka goyi bayan sarautarsa.

16. Ta yaya waɗanda suke goyon bayan sarautar Allah suke tsai da shawarwari?

16 Muna goyon bayan sarautar Allah ta wajen shawarwarin da muke yankewa. Jehobah ba ya ba mu takamammun umurni a kan kowane yanayi a rayuwa ba. Maimakon haka, yana gaya mana ra’ayinsa. Alal misali, Jehobah bai tsara wa Kiristoci kayan da za su riƙa sakawa da wanda bai kamata su saka ba. Amma, ya bayyana cewa ya kamata mu zaɓi kaya kuma mu yi adon da ya dace da Kiristoci. (1 Tim. 2:​9, 10) Yana son mu yi tunani a kan yadda shawarwarinmu zai shafi wasu. (1 Kor. 10:​31-33) Idan muka tsai da shawarwari da suka jitu da yadda Jehobah yake tunani, muna nuna cewa muna so kuma muna goyon bayan sarautarsa.

Ku goyi bayan sarautar Allah sa’ad da kuke yanke shawara da kuma a iyalinku (Ka duba sakin layi na 16-18)

17, 18. A waɗanne hanyoyi ne ma’aurata za su nuna cewa suna goyon bayan sarautar Jehobah?

17 Ku yi la’akari da wata hanya da ma’aurata za su goyi bayan sarautar Jehobah. Wataƙila, aurensu bai kasance yadda suka yi zato zai zama ba. Mai yiwuwa suna samun matsaloli sosai. Idan haka ne, za su amfana idan suka yi tunani game da yadda Jehobah ya bi da al’ummar Isra’ila ta dā. Jehobah ya kwatanta kansa a matsayin miji ga mutanensa. (Isha. 54:5; 62:4) Wannan dangantaka tana kama da “aure” da ke cike da matsaloli. Amma Jehobah bai yi saurin daina sha’ani da al’ummar ba. Ya nuna musu jin ƙai a kai a kai kuma ya cika alkawarin da ya yi musu. (Karanta Zabura 106:​43-45.) Hakika, irin wannan ƙaunar za ta sa dangantakarmu da Jehobah ta yi danƙo!

18 Ma’aurata da suke ƙaunar Jehobah suna ƙoƙari su yi koyi da shi. Ko da a ce suna fuskantar matsaloli a aurensu, ba sa kashe aurensu sai idan wani a cikinsu ya yi zina. Sun san cewa Jehobah yana ɗaukan wa’adin aure da muhimmanci sosai kuma yana so mata da miji su “manne” wa juna. (Mat. 19:​5, 6, 9) Kiristoci suna goyon bayan sarautar Jehobah idan suka yi iya ƙoƙarinsu don su yi nasara a aurensu.

19. Mene ne ya kamata mu yi idan muka yi kuskure?

19 Da yake dukanmu ajizai ne, a wasu lokatai mukan yi abubuwa da ke ɓata wa Jehobah rai. Ya san da hakan, shi ya sa ya yi tanadin fansa da Kristi ya ba da. Saboda haka, idan muka yi kuskure, ya kamata mu roƙi Jehobah ya gafarta mana. (1 Yoh. 2:​1, 2) Ya kamata mu koyi darasi daga kuskuren maimakon mu riƙa yin baƙin ciki game da shi. Ban da haka ma, zai dace mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah don shi ne zai gafarta mana kuma ya taimaka mana mu magance wannan yanayin da kyau idan hakan ya faru a nan gaba.​—Zab. 103:3.

20. Me ya sa za mu goyi bayan sarautar Jehobah yanzu?

20 A sabuwar duniya, Jehobah ne zai yi sarauta kuma za mu koyi adalcinsa. (Isha. 11:9) Amma ko a yau ma, za mu iya koyan ra’ayinsa da yadda yake so mu bi da abubuwa. Nan ba da daɗewa ba, babu wanda zai tuhumi yadda Jehobah yake sarauta. Saboda haka, bari dukanmu mu yi iya ƙoƙarinmu don mu goyi bayan sarautar Jehobah ta wurin yi masa biyayya da bauta masa da aminci kuma mu yi ƙoƙari mu yi koyi da shi.