“Ku Yi Kuka Tare da Masu-Kuka”
“Sai ku ƙarfafa wa juna zuciya, kuna riƙa inganta juna.”—1 TAS. 5:11, Littafi Mai Tsarki.
WAƘOƘI: 121, 75
1, 2. Me ya sa muke bukatar mu bincika yadda za a yi wa masu makoki ta’aziyya? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)
WATA ’yar’uwa mai suna Susi ta ce: “Ɗanmu ya rasu kusan shekara ɗaya yanzu, mun yi baƙin ciki sosai a lokacin.” Wani Ɗan’uwa kuma ya ce, “ba zan iya kwatanta irin baƙin cikin da na ji ba” sa’ad da matata ta rasu.” Abin baƙin ciki shi ne, mutane da yawa suna samun kansu a irin wannan yanayin. Kuma ’yan’uwa da yawa ba su taɓa tsammanin ’yan’uwansu ko abokansu za su rasu kafin Armageddon ba. Idan ɗan’uwanka ko abokinka ya rasu ko kuma ka san wani da yake makoki, za ka iya tambayar kanka, ‘Ta yaya za a iya taimaka wa masu makoki su jimre da baƙin cikin da suke yi?’
2 Wataƙila ka taɓa jin mutane suna cewa, da shigewar lokaci mutum zai daina baƙin ciki. Amma hakan gaskiya ne? Wata gwauruwa ta ce, “Abin da mutum yake yi da lokacinsa ne zai sa baƙin cikin ya riƙa raguwa.” Idan mutum ya ji rauni kuma ya kula da shi sosai, a hankali zai warke. Hakazalika idan aka yi mana rasuwa, da sannu-sannu baƙin cikin zai
ragu. Amma mene ne zai taimaka wa masu makoki su rage baƙin cikin da suke yi?JEHOBAH SHI NE “ALLAH NA DUKAN TA’AZIYYA”
3, 4. Me ya sa za mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana fahimtar yanayin masu makoki?
3 Babu shakka, wanda zai iya yi mana ta’aziyya da kyau shi ne Ubanmu mai tausayi, Jehobah. (Karanta 2 Korintiyawa 1:3, 4.) Da yake shi mai tausayi ne sosai, ya tabbatar wa bayinsa cewa: “Ni dai, ni ne mai-yi maku ta’aziyya.”—Isha. 51:12; Zab. 119:50, 52, 76.
4 Jehobah ma da kansa ya yi baƙin ciki sa’ad da bayinsa suka rasu. Kamar su waye ke nan? Ibrahim da Ishaku da Yakubu da Musa da kuma Sarki Dauda. (Lit. Lis. 12:6-8; Mat. 22:31, 32; A. M. 13:22) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Jehobah yana ɗokin ganin lokacin da zai ta da su. (Ayu. 14:14, 15) Za su yi farin ciki kuma su zama da koshin lafiya. Ƙari ga haka, Ɗan da Allah yake ƙauna sosai wato “abin daularsa” ma ya yi mutuwar wulaƙanci. (Mis. 8:22, 30) Ba za a iya kwatanta irin baƙin cikin da Jehobah ya ji ba.—Yoh. 5:20; 10:17.
5, 6. Ta yaya Jehobah yake mana ta’aziyya?
5 Muna da tabbaci cewa Jehobah zai iya taimaka mana. Don haka, ya kamata mu yi addu’a ga Jehobah kuma mu gaya masa irin baƙin cikin da muke yi. Sanin cewa Jehobah ya san irin baƙin cikin da muke yi kuma zai yi mana ta’aziyya yana ƙarfafa mu sosai, ko ba haka ba? Amma ta yaya Jehobah yake yi mana ta’aziyya?
6 Hanya ɗaya da Allah yake amfani da ita don ya ƙarfafa mu ita ce ta wurin “ta’aziyyar Ruhu Mai-tsarki.” (A. M. 9:31) Ruhun Allah yana mana ta’aziyya sosai. Yesu ya yi mana alkawari cewa Allah yana “ba da Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda suke roƙonsa.” (Luk. 11:13) Susi da aka ambata ɗazun ta ce: “Akwai lokatan da muke durƙusawa mu roƙi Jehobah ya yi mana ta’aziyya. Kuma a duk lokacin da muka yi hakan, muna samun salama da kwanciyar hankali.”—Karanta Filibiyawa 4:6, 7.
YESU BABBAN FIRIST NE MAI TAUSAYI SOSAI
7, 8. Me ya sa muke da tabbaci cewa Yesu zai yi mana ta’aziyya?
7 A lokacin da Ɗan Allah, Yesu yake duniya, furucinsa da ayyukansa sun nuna cewa Ubansa mai tausayi ne sosai. (Yoh. 5:19) Jehobah ya aiko Yesu don ya yi wa masu baƙin ciki da “makoki” ta’aziyya. (Isha. 61:1, 2; Luk. 4:17-21) Mutane sun san cewa Yesu ya fahimci irin wahalar da suke sha kuma ya taimaka musu.—Ibran. 2:17.
8 Yesu ma ya yi baƙin ciki don ’yan’uwansa da abokansa sun rasu a lokacin da yake ƙarami. Wataƙila Yusufu wanda ya yi rainon Yesu, ya mutu a lokacin da Yesu yake yaro. * Hakika, zai yi wa Yesu a lokacin wuya sosai ya jimre da rashin. Ban da haka ma, zai yi baƙin ciki sosai sa’ad da ya ga mahaifiyarsa da ’yan’uwansa suna makoki.
9. Ta yaya Yesu ya nuna cewa shi mai tausayi ne sa’ad da Li’azaru ya mutu?
9 Yadda Yesu ya yi hidimarsa a duniya ya nuna cewa ya fahimci yanayin mutane kuma ya ji tausayinsu. Alal misali, Yoh. 11:33-36.
Yesu ya yi baƙin ciki sosai kamar yadda Martha da Maryamu suka yi a lokacin da abokinsa Li’azaru ya mutu. Irin baƙin cikin da Yesu ya yi ne ya sa ya zub da hawaye ko da yake ya san cewa zai je ya ta da Li’azaru daga mutuwa.—10. Me ya sa muke da tabbaci cewa Yesu ya san irin baƙin cikin da mutane suke yi?
10 Ta yaya furucin Yesu na yi wa mutane ta’aziyya zai iya ƙarfafa mu a yau? Littafi Mai Tsarki ya ba mu tabbaci cewa “Yesu Kristi ɗaya ne, da jiya, da yau, i, har abada.” (Ibran. 13:8) Da yake “Sarkin rai” ya san yadda mutane suke ji sa’ad da suke baƙin ciki, “yana da iko ya taimaki waɗanda ake jarabtarsu.” (A. M. 3:15; Ibran. 2:10, 18) Saboda haka, muna da tabbaci cewa sa’ad da Yesu ya ga mutane suna baƙin ciki, yana tausaya musu. Ƙari ga haka, ya fahimci yanayinsu kuma zai yi musu ta’aziyya a “lotun bukata,” wato a lokacin da ya dace.—Karanta Ibraniyawa 4:15, 16.
YADDA NASSOSI SUKE YI MANA TA’AZIYYA
11. Waɗanne nassosi ne musamman kake gani suke ƙarfafa ka?
11 Labarin baƙin cikin da Yesu ya yi sa’ad da Li’azaru ya mutu yana ɗaya daga cikin labaran nassosi da yawa da za su iya ƙarfafa masu makoki. Babu shakka, “iyakar abin da aka rubuta a dā aka rubuta su domin koyarwarmu, domin ta wurin haƙuri da ta’aziyyar littattafai mu zama da bege.” (Rom. 15:4) Idan kana baƙin ciki ko makoki, za ka iya yin amfani da waɗannan nassosin don ka sami ƙarfafa:
-
“Ubangiji yana kusa da masu-karyayyar zuciya, yana ceton irin waɗanda suke da ruhu mai-tuba.”—Zab. 34:18, 19.
-
“Sa’ad da nake alhini, ina cikin damuwa, [Jehobah] Ka ta’azantar da ni, ka sa in yi murna.”—Zab. 94:19, LMT.
-
“Ubangijinmu Yesu Kristi da kansa, da Allah Ubanmu wanda ya ƙaunace mu, ya ba mu ta’aziya madawwamiya kuma da nagarin bege ta wurin alheri, shi ta’azantar da zukatanku.”—2 Tas. 2:16, 17. *
YADDA ’YAN’UWA A CIKIN IKILISIYA SUKE MANA TA’AZIYYA
12. A wace hanya mai muhimmanci ce za mu iya yi wa masu makoki ta’aziyya?
12 Waɗanda suke makoki suna iya samun ƙarfafa a ikilisiyar Kirista. (Karanta 1 Tasalonikawa 5:11.) Ta yaya za ka iya ƙarfafa waɗanda suke baƙin ciki da kuma yi musu ta’aziyya? (Mis. 17:22) Ka tuna cewa da akwai “lokacin shiru da lokacin magana.” (M. Wa. 3:7) Wata gwauruwa mai suna Dalene ta ce: “Waɗanda suke makoki suna bukatar su faɗi yadda suke ji da kuma ra’ayinsu. Saboda haka, abu mafi muhimmanci da za ka yi ma wanda yake makoki shi ne ka saurare shi ba tare da ka katse masa magana ba.” Junia, wadda yayanta ya kashe kansa ta ce: “Ko da yake ba za ka iya fahimtar irin baƙin cikin da suke yi ba, abin da ya fi muhimmanci shi ne ka saurare su kuma ka nuna ka damu da su.”
13. Me ya kamata mu riƙa tunawa game da yin makoki?
13 Ya kamata mu riƙa tunawa cewa yadda mutane suke makoki ya bambanta. A wani lokaci ba za mu iya bayyana irin baƙin cikin da muke yi ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zuciya ta san azabar Mis. 14:10) Ko da mutum yana ƙoƙarin ya bayyana mana yadda yake ji, yakan mana wuya mu fahimci ainihin abin da yake son ya faɗa.
kanta: Kuma baƙo ba za ya yi shishige cikin murnarta ba.” (14. Ta yaya za mu ƙarfafa masu makoki?
14 Yana iya yi wa mutum wuya ya san irin furucin da zai yi amfani da shi don ya ƙarfafa masu makoki. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ce “harshen mai-hikima lafiya ne.” (Mis. 12:18) Mutane da yawa sun sami abin da za su iya ƙarfafa wasu da shi a ƙasidar nan Yayinda Wani Wanda Ka Ke Ƙauna ya Mutu. * Amma abu mai muhimmanci da za ka iya yi shi ne ka “yi kuka tare da masu-kuka.” (Rom. 12:15) Wata mai suna Gaby da mijinta ya rasu ta ce: “Ina kuka a kowane lokaci kuma idan wasu suka yi kuka tare ni, ina samun ƙarfafa. A lokacin da na ga hakan, sai in ji kamar ba ni kaɗai ba ne nake makoki.”
15. Ta yaya za mu iya ƙarfafa masu makoki idan ba mu san abin da za mu faɗa ba? (Ka duba akwatin nan “Furuci Masu Daɗi da Za Su Iya Ƙarfafa Masu Makoki.”)
15 Idan ba ka san abin da za ka faɗa don ka ƙarfafa masu makoki ba, za ka iya tura masa kati ko wasiƙa ko saƙon imel ko kuma tes ta waya. Za ka iya rubuta wata ayar Littafi Mai Tsarki ko ka ambaci wani hali mai kyau na mutumin da ya rasu ko kuma ka faɗi wani abin farin ciki da kuka yi tare da shi da zai ƙarfafa mai makokin. Junia ta ce: “Idan na karɓi saƙo ko wasu ’yan’uwa suka gayyace ni, ina samun ƙarfafa sosai. Hakan yana sa in ji cewa mutane suna ƙauna ta kuma sun damu da ni sosai.”
16. A wace hanya kuma za mu iya ƙarfafa masu makoki?
16 Za mu iya yin addu’a a madadin ’yan’uwanmu masu makoki don su sami ƙarfafa. Ban da haka ma, za mu iya yin addu’a tare da su. Ko da yake bai da sauƙi mu yi hakan don za mu iya ji kamar mu yi kuka, amma idan muka ƙoƙarta muka yi hakan za mu ƙarfafa mai makokin sosai. Dalene ta ce: “A wasu lokuta idan ’yan’uwa mata sun zo su ƙarfafa ni, ina gaya musu mu yi addu’a tare. Kuma sau da yawa idan suka soma addu’ar sukan rasa abin da za su faɗa, amma idan suka ci gaba sai su san abin da za su faɗa. Ƙaunar da suke nunawa da bangaskiyarsu da yadda suke nuna cewa sun damu da ni yana ƙarfafa ni sosai.”
KA CI GABA DA YI WA MUTANE TA’AZIYYA
17-19. Me ya sa muke bukata mu ci gaba da ƙarfafa masu makoki?
17 Yadda mutane suke makoki ya bambanta sosai da juna. Don haka, sa’ad da wani abokinmu ko ɗan’uwanmu ya rasu, dangi da abokai da yawa za su riƙa zuwa don su yi mana ta’aziyya. Amma idan suka tafi, masu makokin za su bukaci ta’aziyya. Shi ya sa yake da kyau mu ci gaba da ƙarfafa su bayan hakan. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Aboki kullayaumi ƙauna yake yi, kuma an haifi ɗan’uwa domin kwanakin shan wuya.” (Mis. 17:17) ’Yan’uwa za su ci gaba da yi wa masu makoki ta’aziyya ko da sun daɗe suna makoki.—Karanta 1 Tasalonikawa 3:7.
18 Abubuwa kamar su bikin tuna da ranar aure da wata waƙa ko hotuna da wasu ayyuka da ƙamshin turare ko ƙara ko kuma wata rana ko wata a shekara zai iya tuna musu game da ’yan’uwansu da suka rasu kuma ya sa su baƙin ciki sosai. Bayan rasuwar abokin aure, duk wani abin da ɗayan zai yi da farko shi kaɗai kamar halartan babban taro da taron Tuna da Mutuwar Yesu zai sa shi baƙin ciki sosai. Wani ɗan’uwa ya ce: “Sa’ad da matata ta rasu, na san cewa idan ranar tuna aurenmu ta zagayo, zan yi baƙin ciki sosai. Amma ’yan’uwa sun shirya wani bikin shaƙatawa tare da abokai na kud da kud don kada in yi baƙin ciki sosai.”
19 Ya kamata mu tuna cewa masu makoki suna bukatar ta’aziyya a kowane lokaci. Junia ta ce: “Idan ana ƙarfafa ka a kowane lokaci, ba kawai a lokacin tuna da bikin aurenku ba, hakan yana taimaka wa sosai. Irin wannan taimakon yana ƙarfafa ni sosai.” A gaskiya mun sa cewa ba za mu iya kawar da baƙin cikin da suke yi ko kuma kaɗaicin ba, amma za mu iya ƙarfafa masu makoki idan muka taimaka musu da wasu ayyuka. (1 Yoh. 3:18) Gaby ta ce: “Ina godiya ga Jehobah don dattawa masu ƙauna da ya tanadar a ikilisiya da suka taimaka min sosai sa’ad da nake baƙin ciki. Sun sa na ji cewa Jehobah yana kula da ni sosai.”
20. Me ya sa alkawarin da Jehobah ya yi mana yake ƙarfafa mu sosai?
20 Da yake mun san cewa Jehobah, Allah na dukan ta’aziyya zai kawar da baƙin ciki kuma ya sa ‘dukan waɗanda suke cikin kabarbaru su ji muryarsa [Kristi] su fito,’ hakan yana ƙarfafa mu sosai! (Yoh. 5:28, 29) Allah ya yi alkawari cewa zai “haɗiye mutuwa har abada: Ubangiji Yahweh za ya shafe hawaye daga dukan fuskoki.” (Isha. 25:8) Mutane a faɗin duniya za su yi farin ciki tare da masu farin ciki maimakon su yi “kuka tare da masu-kuka.”—Rom. 12:15.
^ sakin layi na 8 A lokaci na ƙarshe da aka ba da labarin Yusufu a Littafi Mai Tsarki Yesu yana ɗan shekara 12. A lokacin da Yesu ya yi mu’ujizarsa ta farko na juya ruwa zuwa giya, ba a sake ambata Yusufu ba. A lokacin da Yesu yake kan gungumen azaba, ya ce manzo Yohanna ya kula da mahaifiyarsa Maryamu. Da a ce Yesu bai ambaci mahaifiyarsa kaɗai ba, da za mu ce Yusufu yana da rai a lokacin.—Yoh. 19:26, 27.
^ sakin layi na 11 Nassosin da mutane da yawa suka ce ya ƙarfafa su, su ne Zabura 20:1, 2; 31:7; 38:8, 9, 15; 55:22; 121:1, 2; Ishaya 57:15; 66:13; Filibiyawa 4:13; da kuma 1 Bitrus 5:7.
^ sakin layi na 14 Don ƙarin bayani, ka duba talifin nan “Comfort the Bereaved, as Jesus Did” da ke Hasumiyar Tsaro na 1 ga Nuwamba, 2010 a Turanci.