TALIFIN NAZARI NA 42
Ka Kasance da Tabbaci Cewa Ka Sami Gaskiya
“Sai dai ku gwada kome, ku riƙe abin da yake da kyau.”—1 TAS. 5:21.
WAƘA TA 142 Mu Jimre, Aljanna Ta Kusa
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1. Me ya sa mutane da yawa suka rikice?
AKWAI ɗarikun Kiristoci da yawa a yau da suke da’awar cewa suna bauta wa Allah a hanyar da yake so. Shi ya sa mutane da yawa suka rikice kuma suke tambaya, “Shin, akwai addini ɗaya na gaskiya ko kuma dukan addinai ne suke faranta wa Allah rai?” Mun tabbata da dukan zuciyarmu cewa abubuwan da muke koyarwa gaskiya ne kuma Jehobah ya amince da tsarin bauta da muke bi? Zai yiwu mu kasance da wannan tabbacin? Bari mu tattauna abubuwan da suka tabbatar mana da hakan.
2. Me ya sa Bulus ya kasance da tabbaci cewa yana bin gaskiya? (1 Tasalonikawa 1:5)
2 Manzo Bulus ya kasance da tabbaci cewa abin da ya yi imani da shi gaskiya ne. (Karanta 1 Tasalonikawa 1:5.) Ya yi hakan ne domin ya yi nazarin Kalmar Allah sosai, ba don son zuciyarsa kawai ba. Ya gaskata cewa “duk Rubutacciyar Maganar Allah hurarre ce daga wurinsa.” (2 Tim. 3:16) Mene ne Bulus ya koya daga nazarin da ya yi? A cikin Nassosi, Bulus ya ga tabbaci cewa Yesu shi ne Almasihun da aka yi alkawari zai zo. Amma limaman addinin Yahudawa sun ƙi amincewa da wannan tabbacin. Sun ce suna koya wa mutane gaskiya game da Allah amma suna yin abubuwan da Allah ya tsana. (Tit. 1:16) Bulus ya bambanta da waɗannan mutanen. Bai gaskata da wasu abubuwa a cikin Kalmar Allah sa’an nan ya ƙi gaskatawa da sauran ba. Bulus ya kasance a shirye ya koyar kuma ya bi “dukan shawarar Allah.”—A. M. 20:27, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.
3. Muna bukatar mu sami amsoshin dukan tambayoyinmu kafin mu tabbata cewa abubuwan da muka yi imani da su gaskiya ne? (Ka duba akwatin nan “ Yawan Ayyukan Jehobah da Shirye-Shiryensa ‘Sun Fi Gaban Ƙirge.’”)
3 Wasu suna ganin ya kamata addini na gaskiya ya iya ba 1 Tas. 5:21) Ya ce: “Iliminmu ba cikakke ba ne,” kuma ya daɗa da cewa, ‘muna ganin kamanni ne a madubi duhu-duhu.’ (1 Kor. 13:9, 12) Bulus bai fahimci kome da kome ba, kuma mu ma ba mu fahimci kome da kome ba. Amma ya fahimci gaskiya game da nufin Jehobah kuma ya koyi abubuwan da suka tabbatar masa da cewa abubuwan da ya yi imani da su gaskiya ne.
da amsa ga kowace tambaya, har da tambayoyi da ba a tattauna a Littafi Mai Tsarki ba. Shin, hakan zai yiwu? Ka yi la’akari da misalin Bulus. Ya ƙarfafa ’yan’uwansa Kiristoci cewa ‘su gwada kome,’ amma ya amince cewa akwai abubuwa da yawa da bai fahimta ba. (4. Ta yaya za mu tabbata cewa abubuwan da muka yi imani da su gaskiya ne, kuma mene ne za mu tattauna game da Kiristoci na gaskiya?
4 Hanya ɗaya da za mu iya tabbata cewa abubuwan da muka yi imani da su gaskiya ne ita ce ta wajen gwada tsarin ibada da Yesu ya kafa da wanda Shaidun Jehobah suke bi a yau. A wannan talifin, za mu ga cewa Kiristoci na gaskiya (1) suna guje wa bautar gumaka, (2) suna daraja sunan Allah, (3) suna son gaskiya kuma (4) suna ƙaunar juna sosai.
MUNA GUJE WA BAUTAR GUMAKA
5. Mene ne muka koya daga Yesu game da hanyar da ta dace mu bauta wa Allah, kuma ta yaya za mu bi abin da ya koya mana?
5 Yesu ya bauta wa Jehobah shi kaɗai domin yana ƙaunar sa, kuma ya yi hakan sa’ad da yake sama da kuma duniya. (Luk. 4:8) Ya koya wa mabiyansa ma su bauta wa Jehobah kaɗai. Yesu da mabiyansa masu aminci ba su yi amfani da wata siffa a ibadarsu ko sau ɗaya ba. Tun da yake ba ma iya ganin Allah, babu mutumin da zai iya yin wata siffa da za ta yi kama da Allah! (Isha. 46:5) Shin ya dace a yi siffar mutanen da ake ganin suna da tsarki kuma a riƙa yin addu’a a gare su? Doka ta biyu a cikin dokoki goma da Jehobah ya ba Isra’ilawa ta ce: ‘Ba za ka sassaƙa wa kanka wani gunki, ko mai kama da wata halittar wani abu a can sama ko a nan duniya . . . ba. Ba za ka rusuna musu ba.’ (Fit. 20:4, 5) Waɗanda suke so su faranta wa Allah rai sun san cewa ba ya so su bauta wa gumaka.
6. Wane irin tsarin ibada ne Shaidun Jehobah suke bi a yau?
6 Masanan tarihi sun ce a ƙarni na farko, Allah ne kaɗai Kiristoci suka bauta wa. Alal misali, littafin nan History of the Christian Church ya ce da Kiristocin ƙarni na farko ne suke a zamaninmu, “da ba za su yarda” su yi amfani da siffofi a wuraren ibada ba. A yau, Shaidun Jehobah suna bin tsarin da Kiristoci a ƙarni na farko suka kafa. Ba ma addu’a ga mutanen da ake ganin suna da tsarki ko kuma mala’iku, ba ma yin addu’a ga Yesu. Ba ma sara wa tuta kuma ba ma yin abin da zai ɗaukaka gwamnatin ’yan Adam. Ko da me zai faru, muna shirye mu bi umurnin Yesu cewa: “Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta masa.”—Mat. 4:10.
7. Wane bambanci ne ke tsakanin Shaidun Jehobah da sauran addinai?
7 A yau, mutane da yawa suna son saurarar limaman addinai da suka shahara. Suna ɗaukaka limaman nan har kusan su bauta musu. Mutane da yawa suna zuwa cocinsu, suna sayan littattafansu, kuma suna ba da gudummawa sosai ga waɗannan limamai ko ƙungiyoyi don su nuna goyon bayansu. Wasu suna amincewa da dukan abin da limaman suka faɗa. Mutanen suna yi ma limaman ganin Yesu da kansa. Amma waɗanda suke bauta wa Allah a hanyar da ta dace ba sa bin ’yan Adam. Ko da yake muna daraja waɗanda suke ja-goranci a tsakaninmu, mun amince da abin da Yesu ya koyar cewa: “Dukanku kuwa ’yan’uwa ne.” (Mat. 23:8-10) Ba ma bauta wa ’yan Adam, ko da su limamai ne ko ’yan siyasa. Ba ma goyon bayan abubuwan da suke yi, kuma ba ma saka baki a sha’anin duniya. A waɗannan hanyoyin ne muka bambanta da mutanen da suke kiran kansu Kiristoci.—Yoh. 18:36.
MUNA DARAJA SUNAN ALLAH
8. Ta yaya muka san cewa Jehobah yana so a girmama sunansa kuma kowa ya san sunan?
8 Akwai lokacin da Yesu ya yi addu’a ya ce: “Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Jehobah da kansa ya amsa da babbar murya daga sama ya ce zai ɗaukaka sunansa. (Yoh. 12:28) Ta wajen wa’azin da ya yi, Yesu ya ɗaukaka sunan Ubansa. (Yoh. 17:26) Saboda haka, Kiristoci suna alfahari da yin amfani da sunan Allah kuma suna koya wa mutane game da sunan.
9. Ta yaya Kiristoci a ƙarni na farko suka nuna cewa suna daraja sunan Allah?
9 A ƙarni na farko, ba da daɗewa ba bayan an kafa ikilisiyar Kirista, Jehobah ya “keɓe wata jama’a” daga cikin waɗanda ba Yahudawa ba don su zama jama’arsa. (A. M. 15:14) Kiristoci a ƙarni na farko sun yi alfahari da yin amfani da sunan Allah da kuma koya wa mutane. Sun yi amfani da sunan Allah sosai sa’ad da suke wa’azi da kuma a nassosin da suka rubuta. * Ta yin hakan, sun nuna cewa su ne kaɗai mutanen da suke sanar da sunan.—A. M. 2:14, 21.
10. Mene ne ya tabbatar mana cewa Shaidun Jehobah suna girmama sunan Allah?
10 Shaidun Jehobah suna girmama sunan Allah kuwa? Bari mu bincika abubuwan da suka tabbatar da hakan. A yau, limamai da yawa suna yin iya ƙoƙarinsu don su ɓoye sunan Allah. Sun ciccire sunan Allah a fassarar Littafi Mai Tsarki da suka yi, har ma wasu sun hana yin amfani da sunan a ibadarsu. * Hakika Shaidun Jehobah ne kaɗai suke girmama da kuma daraja sunansa. Mu ne muke sanar da sunan Allah a faɗin duniya fiye da kowane addini! Hakan yana nufin cewa muna yin iya ƙoƙarinmu mu yi abin da sunan nan, Shaidun Jehobah, yake nufi. (Isha. 43:10-12) Mun wallafa juyin New World Translation of the Holy Scriptures fiye da kofi miliyan 240, kuma mun mayar da sunan Allah a wuraren da waɗansu mafassaran Littafi Mai Tsarki suka ciccire. Ƙari ga haka, muna wallafa littattafan da suke bayyana Littafi Mai Tsarki da suke ɗaukaka sunan Allah a yaruka fiye da 1000!
MUNA SON GASKIYA
11. Ta yaya Kiristoci a ƙarni na farko suka nuna cewa suna son gaskiya?
11 Yesu yana son gaskiya game da Allah da kuma nufinsa. Yadda Yesu ya yi rayuwa Yoh. 18:37) Mabiyan Yesu na gaskiya ma suna son gaskiya sosai. (Yoh. 4:23, 24) Manzo Bitrus ma ya ce bangaskiyar Kirista “hanyar gaskiya” ce. (2 Bit. 2:2) Domin suna son gaskiya sosai, Kiristoci na farko sun ƙi amincewa da wasu koyarwar addini, da al’adu da kuma ra’ayoyin mutane da ba su jitu da gaskiya ba. (Kol. 2:8) Haka ma a yau, Kiristoci na gaskiya suna yin iya ƙoƙarinsu su riƙa “bin gaskiya” ta wajen tabbata cewa abubuwan da suka yi imani da su da kuma salon rayuwarsu sun jitu da Kalmar Allah.—3 Yoh. 3, 4.
ya nuna cewa ya san gaskiya, kuma ya koya wa mutane gaskiyar. (12. Mene ne Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu take yi a duk lokacin da ta gano cewa muna bukatar gyara yadda muka fahimci wani batu a Littafi Mai Tsarki, kuma me ya sa suke yin hakan?
12 Shaidun Jehobah ba sa cewa sun san kome da kome a Littafi Mai Tsarki. A wasu lokuta, sukan yi kuskure a yadda suka bayyana wata koyarwar Littafi Mai Tsarki ko kuma yadda aka tsara ikilisiya. Bai kamata hakan ya ba mu mamaki ba. Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa a hankali a hankali ne mutanen Allah za su daɗa fahimtar gaskiya. (Kol. 1:9, 10) A hankali a hankali ne Jehobah yake sa mu san gaskiya. Saboda haka, dole ne mu yi haƙuri har sai mun daɗa fahimtar gaskiya da kyau. (K. Mag. 4:18) A duk lokacin da Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta gano cewa ya kamata a canja yadda muka fahimci wani batu ko yadda muke yin wasu abubuwa, tana yin hakan nan da nan. Coci-coci suna yin canje-canje domin su faranta wa mabiyansu rai kuma su daɗa bin halin mutanen duniya. Amma ƙungiyar Jehobah tana yin canje-canje ne domin mu daɗa kusantar Allah kuma mu bauta masa kamar yadda Yesu ya yi. (Yak. 4:4) Ba don ra’ayin mutanen duniya ya canja ne shi ya sa muke yin canje-canje ba, amma domin mun daɗa fahimtar Littafi Mai Tsarki ne. Hakika, muna son gaskiya!—1 Tas. 2:3, 4.
MUNA ƘAUNAR JUNA SOSAI
13. Wane hali mafi kyau ne Kiristoci na gaskiya suka nuna, kuma ta yaya Shaidun Jehobah suke nuna wannan halin a yau?
13 Kiristoci na farko sun nuna halaye da yawa masu kyau. Amma halin da suka fi nunawa shi ne ƙauna. Yesu ya ce: “Ta haka kowa zai sani ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.” (Yoh. 13:34, 35) A yau, Shaidun Jehobah a faɗin duniya suna ƙaunar juna kuma suna da haɗin kai. Mun bambanta da sauran addinai. Duk da cewa mun fito daga ƙasashe dabam-dabam da kuma al’adu dabam-dabam, dukanmu iyali ɗaya ne. Muna ganin yadda ’yan’uwa suke nuna wannan ƙaunar a duk lokacin da muka halarci taron ikilisiya ko taron da’ira ko kuma taron yanki. Hakan ya tabbatar mana cewa Jehobah ya amince da ibadarmu.
14. Kamar yadda Kolosiyawa 3:12-14 suka nuna, a wace hanya mai muhimmanci ce za mu nuna cewa muna ƙaunar juna?
14 Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu “ƙaunaci juna da ƙauna ta ainihi.” (1 Bit. 4:8) Wata hanya da za mu nuna cewa muna ƙaunar ’yan’uwanmu ita ce ta gafarta musu da kuma yin haƙuri da su a duk lokacin da suka yi mana laifi. Ƙari ga haka, muna ƙoƙari mu zama masu bayarwa hannu sake ga kowa a ikilisiya, har da ’yan’uwan da suka yi mana laifi. (Karanta Kolosiyawa 3:12-14.) Idan muna nuna irin wannan ƙaunar, kowa zai san cewa mu ne Kiristoci na gaskiya.
“BANGASKIYA ƊAYA”
15. A waɗanne hanyoyi ne muke bin tsarin da Kiristoci a ƙarni na farko suka kafa?
15 Akwai wasu hanyoyi kuma da muke bin tsarin ibada da Kiristoci a ƙarni na farko suka kafa. Yadda aka tsara ƙungiyar Jehobah a yau daidai ne da yadda Kiristoci a ƙarni na farko suka tsara kansu. Kamar yadda suka yi, muna da masu kula masu ziyara, da dattawa da kuma bayi masu hidima. (Filib. 1:1; Tit. 1:5) Muna bin dokokin da Jehobah ya bayar game da jima’i da aure da kuma yin amfani da jini. Ƙari ga haka, muna yanke zumunci da masu zunubi da suka ƙi tuba domin mu kāre ’yan’uwa a ikilisiya.—A. M. 15:28, 29; 1 Kor. 5:11-13; 6:9, 10; Ibran. 13:4.
16. Mene ne muka koya daga abin da ke Afisawa 4:4-6?
16 Yesu ya ce mutane da yawa za su ce su mabiyansa ne. Amma ba dukansu ba ne za su bi shi da gaske. (Mat. 7:21-23) Littafi Mai Tsarki ya ce a kwanaki na ƙarshe, mutane da yawa za su “nuna su masu addini ne.” Amma hakan ruɗu ne. (2 Tim. 3:1, 5) Littafi Mai Tsarki ya bayyana sarai cewa “bangaskiya ɗaya” ko addini ɗaya ne kawai Allah ya amince da shi.—Karanta Afisawa 4:4-6.
17. Su waye ne suke bin Yesu kuma suke da addini na gaskiya?
17 Su waye ne suke da addini na gaskiya a yau? Mun riga mun tattauna abubuwa da yawa da suka nuna mana amsar. Mun tattauna tsarin ibada da Yesu ya kafa da kuma yadda Kiristoci a ƙarni na farko suka bi tsarin. Duka abubuwa da muka tattauna sun tabbatar mana cewa Shaidun Jehobah ne suke da addini na gaskiya. Gata ne babba mu kasance cikin mutanen Jehobah da kuma sanin gaskiya game da Jehobah da kuma nufinsa. Don haka, bari mu yi iya ƙoƙarinmu don mu riƙe bangaskiyarmu da ƙarfi.
WAƘA TA 3 Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu
^ sakin layi na 5 A wannan talifin, za mu tattauna tsarin bauta ta gaskiya da Yesu ya kafa da kuma yadda mabiyansa a ƙarni na farko suka bi tsarin. Ƙari ga haka, talifin zai ba da tabbaci da ya nuna cewa Shaidun Jehobah suna bin wannan tsari na bauta ta gaskiya a yau.
^ sakin layi na 9 Ka duba akwatin nan, “Did the First Christians Use God’s Name?” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuli, 2010, shafi na 6, a Turanci.
^ sakin layi na 10 Alal misali, a 2008, Paparoma Benedict na 16 ya ba da umurni cewa “kada a yi amfani da sunan Allah” a ibadarsu ta Katolika, ko a waƙoƙinsu ko addu’o’insu.
^ sakin layi na 63 BAYANI A KAN HOTO: Shaidun Jehobah sun buga juyin New World Translation a yaruka fiye da 200 don mutane su karanta Kalmar Allah a yarensu, kuma littafin ya yi amfani da sunan Allah.