Ka Sani?
Me ya taimaka wa Istifanus ya natsu sa’ad da ake tsananta masa?
ISTIFANUS yana gaban mutane masu adawa da shi. Yana gaban Majalisa, wato kotu mafi girma a Isra’ila kuma alƙalai 71 mafi iko a al’ummar ne suke shari’ar. Babban Firist Kayafa ne ya tara su, kuma shi ne ya ja-goranci shari’a da aka yi wa Yesu ’yan watanni da suka shige kuma aka yanke wa Yesu hukuncin mutuwa. (Mat. 26:57, 59; A. M. 6:8-12) Mutane masu shaidar ƙarya suna zuwa ɗaya bayan ɗaya suna ba da shaida. Amma mutane da suke majalisar sun lura da wani abin ban-mamaki game da Istifanus. Sun ga cewa “fuskarsa ta zama kamar ta mala’ika.”—A. M. 6:13-15.
Me ya taimaka wa Istifanus ya natsu a irin wannan yanayin? Kafin a kai Istifanus gaban Majalisa yana hidimarsa da ƙwazo kuma ruhu mai tsarki ne yake taimaka masa. (A. M. 6:3-7) Sa’ad da yake fuskantar wannan gwajin, ruhu mai tsarki yana tare da shi kuma ya taimaka masa. (Yoh. 14:16) Istifanus ya furta abin da ke rubuce a Ayyukan Manzanni sura 7 da gaba gaɗi sa’ad da yake kāre kansa. Kuma ruhu mai tsarki ya sa ya tuna abin da ke cikin ayoyi 20 ko kuma fiye da hakan a cikin Nassosin Ibrananci. (Yoh. 14:26) Ƙari ga haka, Istifanus ya sami ƙarfafa sosai sa’ad da ya ga wahayi game da Yesu yana tsaye a hannun dama na Allah.—A. M. 7:54-56, 59, 60.
Wata rana wataƙila mu ma za a yi mana barazana kuma a tsananta mana. (Yoh. 15:20) Amma ruhun Jehobah zai taimaka mana idan muna karanta Kalmar Allah a kai a kai kuma muna ƙwazo a hidima. Hakan zai sa mu sami ƙarfin jimre tsanantawa kuma mu natsu.—1 Bit. 4:12-14