HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Oktoba 2018
Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 3-30 ga Disamba, 2018.
1918—Shekara Dari da ta Shige
Duk da cewa ana kan tabka Yakin Duniya na Daya a Turai, abubuwan da suka faru a somawar shekarar, sun ba da alama cewa Daliban Littafi Mai Tsarki da kuma duniya gabaki daya za su cim ma abubuwa da yawa.
Ka Rika Fadin Gaskiya
Me ya sa mutane suke karya, kuma wane sakamako ne hakan yake kawo wa? Ta yaya za mu rika fada wa juna gaskiya?
Ka Rika Koyar da Gaskiya
Da yake karshe ya kusa sosai, muna bukatar mu mai da hankali ga soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma koya wa mutane gaskiya game da Jehobah. Ta yaya za mu yi amfani da Kayan Aiki don Koyarwa a wa’azi?
TARIHI
Jehobah Ya Albarkace Ni Sosai Don Zabin da Na Yi
Sa’ad da yake matashi, Charles Molohan ya zabi ya fadada hidimarsa ta wurin yin hidima a Bethel. Jehobah ya albarkace shi sosai don wannan zabin da ya yi.
Ku Dogara ga Kristi, Mai Mana Ja-goranci
Yayin da kungiyar Allah take samun ci gaba, me ya sa ya kamata mu bi ja-gorancin Kristi?
Ku Kasance da Kwanciyar Rai Idan Yanayinku Ya Canja
Muna fuskantar canje-canje a rayuwarmu da ba mu yi zato ba, kuma hakan na iya tayar mana da hankali. Ta yaya salama da Allah yake sa mu kasance da ita ke taimaka mana?
Ka Sani?
Istifanus ya zama mabiyin Yesu da aka fara kashewa don imaninsa. Me ya taimaka masa don kada ya firgita sa’ad da ake tsananta masa?