Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Hoton da ke dakalin magana da kuma naɗaɗɗen hoton da ke saman shi

1922​—Shekaru Dari da Suka Shige

1922​—Shekaru Dari da Suka Shige

“ALLAH . . . ya ba mu nasara ta wurin . . . Yesu Almasihu!” (1 Kor. 15:57) Waɗannan kalamai da aka zaɓa su zama jigon shekara ta 1922 sun tabbatar wa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki cewa za a albarkaci bangaskiyarsu. A shekarar, Jehobah ya albarkace waɗannan ’yan’uwa da suka yi wa’azi da ƙwazo. Ya daɗa albarkace su sa’ad da suka soma buga littattafansu da kansu da kuma yaɗa wa’azin Mulkin Allah ta rediyo. Daga baya, a cikin shekarar, Jehobah ya sake nuna cewa yana yi wa mutanensa albarka. Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun sami damar halartar gagarumin taro a Cedar Point, Ohio, a ƙasar Amirka. Abin da ya faru a taron ya shafi aikin da ƙungiyar Jehobah take yi daga lokacin har wa yau.

“SHAWARA MAI MUHIMMANCI”

Da aka soma samun ƙarin masu shela, an bukaci ƙarin littattafai. ’Yan’uwan da ke Bethel a Brooklyn suna buga mujallu, amma wasu kamfanoni ne suke buga musu shafin farko na littattafansu. Sa’ad da aka yi ƙarancin takardu na ’yan watanni, hakan ya shafi wa’azi a lokacin. Don haka, Ɗan’uwa Rutherford ya tambayi Robert Martin, wanda shi ne mai kula da ɓangaren buga mujallu, ko a ganinsa za su iya buga littattafan da kansu?

Wurin buga littattafanmu da ke Concord Street a Brooklyn na jihar New York

Ɗan’uwa Martin ya ce: “Wannan shawara ce mai kyau, domin hakan ya sa mun iya buɗe wurin buga littattafai.” Sai ’yan’uwan suka yi hayar wani wuri a 18 Concord Street da ke Brooklyn kuma suka sayi kayan aikin da suke bukata.

Ba kowa ba ne ya yi farin ciki cewa ’yan’uwan za su iya buga littattafai da kansu ba. Shugaban wani kamfani da suka saba buga mana littattafanmu ya ziyarci inda muke buga littattafai kuma ya ce: “Ga shi kuna da kayan buga littattafai masu kyau, amma babu wanda zai iya amfani da su. A cikin wata shida za ku lalata duka kayan aikin.”

Ɗan’uwa Martin ya ce: “Hakan yana iya zama gaskiya, amma mun san cewa Jehobah zai taimaka mana kuma ya yi hakan.” Ɗan’uwa Martin ya faɗi gaskiya. Ba da daɗewa ba, an soma buga littattafai 2,000 a sabon wurin buga littattafan kowace rana.

Waɗanda suke buga littattafai a tsaye kusa da injin buga littattafai wanda ake kira linotype

YADDA AKA KOYAR DA DUBBAN MUTANE TA REDIYO

Ban da buga nasu littattafai, bayin Jehobah sun soma amfani da rediyo wajen yaɗa bisharar Mulki. A ranar Lahadi, 26 ga Fabrairu, 1922, Ɗan’uwa Rutherford ya yi jawabi a gidan rediyo a karo na farko. Jigon jawabin da ya bayar shi ne, “Miliyoyin Mutane da Suke Rayuwa Yanzu Ba Za Su Taɓa Mutuwa Ba!” a tashar rediyo na KOG a Los Angeles, na jihar California, a ƙasar Amirka.

Aƙalla mutane 25,000 suka saurari shirin. Wasunsu sun rubuta wasiƙu zuwa ga Ɗan’uwa Rutherford, kuma sun gode masa domin jawabin. Ɗaya daga cikinsu shi ne wanda Willard Ashford da ke zama a Santa Ana, a jihar California ya rubuta. Ya gode wa Ɗan’uwa Rutherford don yadda ya yi jawabi “mai ƙayatarwa da kuma daɗi.” Ya kuma ce: “A gidana, akwai marasa lafiya guda uku da ba za su iya fita su saurari jawabin ba ko da a ce ka ba da shi a kusa da gidanmu ne.”

Daga baya, an ba da wasu jawabai a makonnin da ke biye. A ƙarshen shekarar, Hasumiyar Tsaro ta bayyana cewa, “aƙalla mutane 300,000 ne suka saurari jawaban ta rediyo.”

Wasiƙu da kuma kalaman da mutane suke yi, ya sa Ɗaliban Littafi Mai Tsarkin su kafa tashar rediyo a Staten Island, kusa da Bethel da ke Brooklyn. A shekarun da suka biyo baya, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi amfani da tashar WBBR, don su yaɗa bisharar Mulkin ga mutane a wurare da yawa.

“ADV”

A ranar 15 ga Yuni, 1922, an sanar a Hasumiyar Tsaro cewa za a yi babban taro a Cedar Point, Ohio, daga ranar 5 zuwa 13 ga Satumba, 1922. Ɗaliban Littafi Mai Tsarkin sun yi farin ciki sosai da suka isa Cedar Point.

A jawabinsa na farko Ɗan’uwa Rutherford ya gaya wa masu sauraro cewa: “Ina da tabbaci cewa Jehobah zai . . . albarkaci wannan taron kuma zai sa a yi wa’azi fiye da yadda aka saba yi.” Waɗanda suka ba da jawabai a taron sun yi ta ƙarfafa ’yan’uwa su yi wa’azi.

Jama’a da suka halarci taron da aka yi a Cedar Point, Ohio, a 1922

A ranar Jumma’a 8 ga Satumba, mutane wajen 8,000 ne suka halarci taron, kuma sun yi marmarin su saurari jawabin da Ɗan’uwa Rutherford zai bayar. Sun sa rai cewa zai bayyana ma’anan haruffan nan, “ADV,” da aka rubuta a kan takardar gayyatar da aka ba su. Bayan da suka zauna, da yawa daga cikinsu sun lura da wani katon naɗaɗɗen abin da ake zane a kai (wato canvas) a saman dakalin magana. Arthur Claus, wanda ya zo taron daga Tulsa, a jihar Oklahoma, a ƙasar Amirka, ya sami wurin zama a inda zai saurari jawabin da kyau, domin a lokacin babu na’urori kamar makarufo ko lasifika kuma hakan yana yi wa mutane wuya su ji jawabi da kyau.

“Mun saurare shi da kyau”

Don a tabbatar cewa babu wanda zai ɗauke hankalin mutane daga jawabin, mai kujerar ya yi sanarwa cewa ba za a yarda wanda ya zo latti ya shiga ɗakin taron a lokacin da Ɗan’uwa Rutherford yake ba da jawabinsa ba. Da ƙarfe 9:30 na safe, Ɗan’uwa Rutherford ya soma jawabinsa ta wajen ƙaulin kalaman Yesu da ke Matiyu 4:​17, da ta ce: “Mulkin sama ya kusa.” (Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Da yake tattauna a kan yadda mutane za su saurari saƙon Mulkin, ya ce: “Yesu da kansa ya ce a lokacin bayyanuwarsa, zai tattara mutanensa kuma a lokacin zai tara masu aminci a gare shi.”

Ɗan’uwa Claus, wanda yake zaune a ɗakin taron ya tuna da abin da ya faru kuma ya ce: “A lokacin, mun saurare shi da kyau.” Amma jim kaɗan, sai Ɗan’uwa Claus ya soma rashin lafiya kuma ya zama dole ya bar ɗakin taron. Arthur ya bar ɗakin taron ko da yake bai so ya yi hakan ba domin ba za a yarda masa ya sake dawo ɗakin taron a lokacin da Ɗan’uwa Rutherford yake ba da jawabinsa ba.

Bayan ’yan mintoci, ya soma samun sauƙi. Ya faɗi cewa sa’ad da yake koma ɗakin taron, ya ji mutane suna tafi sosai. Hakan ya sa shi farin ciki sosai! Ya ƙudiri niyyar cewa ko da zai hau saman rufin ne don ya saurari raguwar jawabin mai daɗi zai yi hakan. A lokacin, Ɗan’uwa Claus matashi ne mai shekara 23, don haka, ya iya ya hau rufin ginin. Ya ce wundodin suna nan a buɗe. Don haka, da ya yi kusa da wundon sai ya soma jin jawabin da kyau.”

Amma ba Arthur ne kawai ya hau saman rufin ba. Wasu abokansa ma suna saman rufin. Ɗaya daga cikinsu mai suna Frank Johnson ya zo ya tambaye shi, “Kana da guntun wuka?”

Sai Arthur ya ce: “E, ina da shi.”

Frank ya ce, “muna ta addu’a don mu sami wanda yake da wuka. Ka ga wannan naɗaɗɗen hoton? Ga igiyoyin da suka riƙe shi. Ka saurari Alƙalin da kyau. a Idan ka ji ya ce, ‘ku yi shela, ku yi shela,’ sai ka yanka igiyoyin nan guda huɗu.”

Arthur yana riƙe da wuka a hannu tare da abokansa suna jiran lokacin da Ɗan’uwa Rutherford zai ambaci kalmar da za ta nuna musu cewa lokaci ya yi na yanka igiyar. Jim kaɗan, sai Ɗan’uwa Rutherford ya kai sashe mafi muhimmanci na jawabinsa. Tare da farin ciki da kuzari, da alama Ɗan’uwa Rutherford ya yi ihu cewa: “Ku zama shaidu masu aminci ga Ubangiji. Ku ci gaba da yin wa’azi har sai an hallaka addinan ƙarya. Ku yi wa’azin a ko’ina. Dole ne duniya ta san cewa Jehobah ne Allah na gaskiya kuma Yesu Kristi ne Sarkin Sarakuna da Ubangijin iyayengiji. Wannan ita ce rana mafi muhimmanci a tarihi. Ga shi, Sarkin yana sarauta! Hakkinku ne ku gaya wa mutane game da hakan. Don haka, ku yi shela, ku yi shela, ku yi shelar Sarkin da kuma Mulkinsa!”

Arthur ya faɗi cewa shi da sauran ’yan’uwan sun yanka igiyoyin kuma hoton ya sauka a hankali. An taƙaita kalmar nan a Turanci “Advertise” da haruffan nan “ADV,” wanda yake nufi ku yi shela.

AIKI MAI MUHIMMANCI

Taron da aka yi a Cedar Point ya taimaka ma ’yan’uwan su mai da hankali ga yin aiki mafi muhimmanci, wato wa’azin Mulkin, kuma waɗanda suka ba da kansu sun saka hannu a yin wa’azin. Wani majagaba daga Oklahoma, a Amirka ya rubuta cewa: “A yankin da muke wa’azi, mutane suna haƙa kwal, kuma talakawa ne sosai.” Ya ce a yawancin lokaci, sa’ad da mutane suka ji saƙon da ke mujallar Golden Age, “sukan fashe da kuka.” Ya kammala da cewa, “Mun yi farin ciki sosai don mun iya ƙarfafa su.”

Ɗaliban Littafi Mai Tsarkin sun san muhimmancin kalmomin Yesu da ke Luka 10:2 da ta ce: “Girbin yana da yawa, amma masu aikin kaɗan ne.” Da shekarar ta ƙare, sun ci gaba da yin ƙwazo a yin shelar saƙon Mulkin a duk faɗin duniya.

a A wasu lokuta ana kiran Ɗan’uwa Rutherford “Alƙali” domin a dā shi alƙali ne a Missouri, a Amirka.