Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 21

Kana Nuna Godiya Don Alherin Allah Kuwa?

Kana Nuna Godiya Don Alherin Allah Kuwa?

“Ya Yahweh Allahna, ayyukanka na ban mamaki suna da yawa! Shirye-shiryenka gare mu sun fi gaban ƙirge!”​—ZAB. 40:5.

WAƘA TA 5 Ayyukan Allah Suna da Ban Al’ajabi

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Kamar yadda Zabura 40:5 ta nuna, mene ne Jehobah ya ba mu, kuma me ya sa za mu tattauna su?

JEHOBAH Allah ne mai karimci. Ka yi la’akari da wasu cikin kyaututtuka da ya ba mu. Ya ba mu duniyar nan mai kyau da ƙwaƙwalwarmu mai ban-mamaki da kuma Kalmarsa mai daraja. Jehobah ya yi amfani da waɗannan kyaututtuka wajen tanadar mana da wurin zama da damar yin tunani da tattaunawa da kuma samun amsoshin tambayoyi mafi muhimmanci a rayuwa.​—Karanta Zabura 40:5.

2 Za mu tattauna kyaututtukan nan a wannan talifin. Idan mun yi tunani game da kyaututtukan, za mu zama masu godiya kuma za mu so faranta ran Mahaliccinmu, Jehobah. (R. Yar. 4:11) Za mu kuma kasance a shirye mu taimaka wa mutanen da aka ruɗe su da koyarwar ƙarya na juyin halitta.

AN HALICCI DUNIYA DA KYAU

3. Me ya sa duniya take da ban-mamaki?

3 Yadda Allah ya yi duniya ya nuna cewa shi mai hikima ne sosai. (Rom. 1:20; Ibran. 3:4) Ba duniyar nan kaɗai ba ce take zagaya rana ba, amma duniya tana da ban-mamaki domin a cikinta ne kaɗai abu mai rai zai iya wanzuwa.

4. Me ya sa muka ce duniya ta fi jirgin ruwa?

4 Duniyar nan tana kamar gida mai nisa sosai da ke a rufe. Amma akwai bambanci sosai tsakanin gidan da ke cike da mutane da kuma duniyar nan. Idan mutanen da ke cikin gidan ne suke tanada wa kansu iska da abinci da ruwa, kuma suna zubar da shara a cikin gidan, za su iya rayuwa na dogon lokaci kuwa? Babu shakka, za su yi saurin mutuwa. Akasin haka, biliyoyin mutane da dabbobi suna rayuwa a duniya. Muna samun isasshen iska da abinci da kuma ruwa, kuma ba a taɓa yin ƙarancin su. A duniyar nan ne muke zubar da dukan shara, amma duk da haka, tana da kyau kuma muna iya zama a cikinta. Ta yaya hakan ya yiwu? Sharar da ke duniya tana canjawa zuwa abin da zai amfani mazaunan duniya. Za mu tattauna yadda za mu ga hikimar Jehobah a yadda iskar Oxygen da kuma ruwa suke zagayawa.

5. Ta yaya iska take zagayawa, kuma mene ne hakan ya nuna?

5 Dabbobi da ʼyan Adam suna bukatar iskar Oxygen don su rayu. An kimanta cewa a kowace shekara, iskar da muke shaƙa tana da yawa sosai. ʼYan Adam da dabbobi suna fitar da iskar da ake kira carbon dioxide. Duk da haka, ʼyan Adam da dabbobi ba za su taɓa iya shaƙar dukan iskar da ke duniya ba kuma iskar da suke fitarwa ba za ta iya gurɓata duniya ba. Me ya sa? Domin Jehobah ya halicci itatuwa manya da ƙanana da ke shaƙar iskar carbon dioxide kuma suna fitar da iskar oxygen. Yadda iskar oxygen ke zagayawa ta tabbatar da abin da ke Ayyukan Manzanni 17:​24, 25. Ayoyin sun ce “Allah . . . ne yake ba dukan mutane rai, da numfashi.”

6. Ta yaya ruwa yake zagayawa, kuma mene ne hakan ya nuna? (Ka duba akwatin nan “ Ruwa Kyauta Ne Daga Jehobah.”)

6 Nisar duniya daga rana ta sa ruwan da ke cikinta ba ta zama ƙanƙara ba. Da a ce duniya ta ɗan ƙara kusa da rana, da duk ruwan da ke cikinta ya bushe kuma dukan halittu za su mutu. Kuma da a ce duniya ta ɗan yi nesa da rana, da duk ruwan da ke cikinta ya zama ƙanƙara kuma kome ya daskare. Amma yadda Jehobah ya kafa duniya a wurin da ya dace ya sa ana ci gaba da samun ruwa kuma halittun da ke cikinta ba su mutu ba. Zafin rana na jan ruwan da ke tekuna da doron ƙasa, kuma ruwan yana zama gajimare. A kowace shekara, ruwan da rana yake ja zuwa gajimare zai cika tankin da faɗinsa da kuma tsayinsa ya kai nisan kilomita 80. Gajimare yana riƙe ruwan nan har wajen kwana goma kafin ya sauko duniya kamar ruwan sama ko dusan ƙanƙara. Wannan tsarin ya nuna cewa Jehobah yana da hikima da kuma iko.​—Ayu. 36:​27, 28; M. Wa. 1:7.

7. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna godiya don kyautar da aka bayyana a Zabura 115:16?

7 Mene ne zai taimaka mana mu nuna godiya sosai don wannan duniyar da Allah ya ba mu kyauta? (Karanta Zabura 115:16.) Hanya ɗaya ita ce ta wajen yin tunani a kan abubuwan da Jehobah ya yi. Hakan zai motsa mu mu gode wa Jehobah kullum don alherinsa. Kuma za mu nuna cewa muna daraja duniya ta wajen tsabtace mahallinmu sosai.

ƘWAƘWALWARMU MAI BAN MAMAKI

8. Me ya sa muka ce an yi ƙwaƙwalwarmu a hanya mai ban-mamaki?

8 An halicci ƙwaƙwalwarmu a hanya mai ban-mamaki sosai. Sa’ad da muke cikin mahaifiyarmu, ƙwaƙwalwarmu ta yi girma bisa yadda aka tsara ta. Kuma a kowane minti, dubban sababbin kwayoyin halitta na ƙwaƙwalwa na tasowa! Masu bincike sun faɗi cewa ƙwaƙwalwar mutumin da ya manyanta yana ɗauke da ƙananan ƙwayoyin halitta kusan biliyan 100. An tattara waɗannan ƙwayoyi cikin wani ƙunshi da ke da nauyin wajen kilo 1 da digo 5. Ka yi la’akari da wasu abubuwa da ƙwaƙwalwarmu za ta iya yi.

9. Me ya nuna cewa yin magana baiwa ce daga Allah?

9 Yadda muke yin magana mu’ujiza ce. Ka yi tunani a kan abin da ke faruwa sa’ad da muke magana. Sa’ad da ka furta kalma guda, ƙwaƙwalwarka tana sarrafa jijiyoyi 100 da ke harshenka da maƙogwaronka da leɓenka da muƙamuƙinka da kuma ƙirjinka. Dukan jijiyoyin suna bukatar su bi tsari domin a fahimci abin da kake faɗa. Wani bincike da aka yi a shekara ta 2019 game da yin yare dabam-dabam ya nuna cewa jarirai suna fahimtar kowace kalmar da aka furta. Hakan ya jitu da abin da masu bincike da yawa suka faɗa cewa muna da baiwar koyan harsuna dabam-dabam. Baba shakka, yin magana baiwa ce daga Allah.​—Fit. 4:11.

10. Ta yaya za mu nuna cewa mun daraja baiwar yin magana da Allah ya ba mu?

10 Hanya ɗaya da za mu nuna cewa muna godiya don wannan baiwar ita ce ta wajen tabbatar wa mutanen da suka amince da juyin halitta cewa Allah ne ya halicci kome. (Zab. 9:1; 1 Bit. 3:15) Mutanen da ke da wannan ra’ayin sun ce ba a halicci duniya da abubuwan da ke cikinta ba. Za mu iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki da kuma abubuwan da muka tattauna a wannan talifin don mu koyar da gaskiya game da Mahaliccinmu. Kuma za mu iya bayyana wa mutanen da ke son saƙonmu dalilin da ya sa muka yi imani cewa Jehobah ne Mahaliccin sama da duniya.​—Zab. 102:25; Isha. 40:​25, 26.

11. Me ya sa ƙwaƙwalwarmu take da ban-mamaki?

11 Yadda muke tuna abubuwa yana da ban-mamaki. A dā, wani marubuci ya ce ƙwaƙwalwar ʼyan Adam tana iya tuna bayanan da za su cika manya-manyan littattafai guda miliyan 20. Amma a yau, an gano cewa abubuwan da muke iya tunawa da su sun fi hakan yawa. Wace baiwa ta musamman ce muke da ita don yadda muke iya tunawa da abu?

12. Ta yaya yadda muke koyan darussa ya bambanta mu da dabbobi?

12 A cikin dukan halittun da ke duniya, ʼyan Adam ne kaɗai suke iya koyan darussa ta wajen tunawa da abubuwa da suka taɓa faruwa da kuma yin la’akari da su. A sakamakon haka, muna iya koyan ƙa’idodi masu kyau, mu canja tunaninmu da salon rayuwarmu. (1 Kor. 6:​9-11; Kol. 3:​9, 10) Muna iya horar da zuciyarmu don ta san abu mai kyau da marar kyau. (Ibran. 5:14) Za mu iya koyan nuna ƙauna da tausayi da kuma jinƙai. Kuma za mu iya koyan nuna adalci.

13. Ta yaya ya kamata mu yi amfani da baiwar tunawa da abu, kamar yadda Zabura 77:​11, 12 suka nuna?

13 Hanya ɗaya da za mu nuna godiya don wannan baiwar tunawa da abu ita ce ta wajen tuna cewa Jehobah ya taimaka da kuma ƙarfafa mu a dā. Hakan zai tabbatar mana da cewa zai taimaka mana a nan gaba. (Karanta Zabura 77:​11, 12; 78:​4, 7) Wata hanya kuma ita ce ta wajen tunawa da alherin da mutane suka yi mana da kuma nuna godiya. Binciken da aka yi ya nuna cewa mutanen da ke nuna godiya sun fi farin ciki. Ya kamata kuma mu yi koyi da Jehobah a yadda yake mantawa da wasu abubuwa. Alal misali, Jehobah ba ya mantuwa, amma idan muka yi zunubi kuma muka tuba, yana gafarta mana kuma ya mance da kurakuren da muka yi. (Zab. 25:7; 130:​3, 4) Ya kamata mu yi koyi da shi ta wajen gafarta wa mutanen da suka yi mana laifi.​—Mat. 6:14; Luk. 17:​3, 4.

Muna nuna godiya don ƙwaƙwalwar da Jehobah ya ba mu ta wajen girmama shi da ita (Ka duba sakin layi na 14) *

14. Ta yaya za mu nuna godiya don ƙwaƙwalwar da Jehobah ya ba mu?

14 Za mu iya nuna godiya ga Jehobah idan mun yi amfani da ƙwaƙwalwar da ya ba mu don mu daraja shi. Wasu suna yin amfani da ƙwaƙwalwarsu don su kafa wa kansu ƙa’ida a kan abin da ya dace da wanda bai dace ba, kuma hakan bai dace ba. Amma da yake Jehobah ne ya halicce mu, ƙa’idodinsa sun fi namu daraja. (Rom. 12:​1, 2) Bin ƙa’idodinsa zai sa mu ji daɗin rayuwa. (Isha. 48:​17, 18) Kuma za mu san abin da Jehobah yake so mu yi da rayuwarmu, wato mu daraja shi da kuma faranta masa rai.​—K. Mag. 27:11.

LITTAFI MAI TSARKI KYAUTA NE MAI DARAJA

15. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah yana ƙaunar mutane?

15 Jehobah ya tanadar mana da Littafi Mai Tsarki domin yana ƙaunar mu. Ubanmu na sama ya sa a rubuta shi domin yana ƙaunar ʼya’yansa da ke duniya sosai. Jehobah yana yin amfani da Littafi Mai Tsarki don ya amsa tambayoyi mafi muhimmanci da muke yi a rayuwa. Alal misali: Daga ina muka fito? Mene ne manufar rayuwa? Kuma mene ne zai faru a nan gaba? Jehobah yana so ʼya’yansa su san amsoshin waɗannan tambayoyi, shi ya sa ya motsa mutane su fassara Littafi Mai Tsarki cikin harsuna da yawa. A yau, akwai cikakken Littafi Mai Tsarki ko rabinsa a sama da harsuna 3,000! Littafi Mai Tsarki ne littafin da aka fi fassarawa da kuma rarrabawa. Ko da wane yare ne mutum yake yi ko kuma a ina ne yake da zama, yawanci suna da zarafin karanta Littafi Mai Tsarki a yarensu.​—Ka duba akwatin nan “ An Tanadar da Littafi Mai Tsarki a Harsunan Afirka.”

16. Kamar yadda Matiyu 28:​19, 20 suka nuna, ta yaya za mu nuna godiya don Littafi Mai Tsarki da aka tanada mana?

16 Za mu iya nuna godiya don Littafi Mai Tsarki da Allah ya tanada mana ta wajen karanta shi kowace rana da yin tunani a kan darussan da ke cikinsa da kuma yin abin da muka karanta. Ƙari ga haka, za mu nuna godiya ta wajen koya wa mutane da yawa gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki.​—Zab. 1:​1-3; Mat. 24:14; karanta Matiyu 28:​19, 20.

17. Waɗanne irin kyaututtuka ne muka tattauna a wannan talifin, kuma me za mu tattauna a talifi na gaba?

17 A wannan talifin, mun tattauna kyaututtuka da Allah ya ba mu. Wato duniyar nan da ƙwaƙwalwarmu mai ban-mamaki da kuma hurariyar Kalmarsa. Amma akwai wasu abubuwa da Jehobah ya tanada mana da ba ma iya gani da ido. Za mu tattauna su a talifi na gaba.

WAƘA TA 12 Jehobah, Allah Mafi Iko

^ sakin layi na 5 Wannan talifin zai taimaka mana mu nuna godiya ga Jehobah don kyaututtuka uku da ya ba mu. Zai kuma sa mu taimaka wa mutanen da ke shakkar wanzuwar Allah.

^ sakin layi na 64 BAYANI A KAN HOTUNA: Wata ’yar’uwa tana koyan wani yare don ta koya wa baƙi gaskiyar da ke Kalmar Allah.