Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Su waye ne ’yan sandan haikalin Yahudawa? Mene ne aikinsu?
A dā, wasu daga cikin Lawiyawa da ba firistoci ba suna aikin ’yan sanda a haikali. Shugaban masu gadin haikalin ne yake ja-goranci a wannan aikin. Wani marubuci Bayahude mai suna Philo ya bayyana aikin da ’yan sandan suke yi, ya ce: “Wasu daga cikin waɗannan [Lawiyawa] suna zama a ƙofofin haikalin don yin gadi. Wasu kuma suna zama a [cikin haikalin] a gaban mazauni don su hana mutane shiga wurin da bai kamata ba. Suna yawo a cikin haikalin don yin gadi, wasu suna aiki daddare wasu kuma sa’ad da gari ya waye.”
Ƙari ga haka, waɗannan ’yan sanda suna taimakawa a Majalisa. ’Yan sandan ne kaɗai Romawa suka amince da su.
Wani masani mai suna Joachim Jeremias ya ce: “Abin da Yesu ya ce sa’ad da ’yan sanda suka kama shi cewa kowace rana ina zama a Haikali ina yin koyarwa ba ku kama ni ba (Mat. 26:55), ya nuna cewa ’yan sandan haikali ne suka kama shi.” Marubucin ya gaskata cewa mutanen da suka so su kama Yesu kafin wannan lokacin ma ’yan sandan haikali ne. (Yoh. 7:32, 45, 46) Bayan haka, an tura ’yan sanda da shugabansu su kawo Yesu gaban Majalisa. Daga baya, ’yan Majalisa sun tura ’yan sandan su kamo manzannin Yesu, kuma wataƙila su ne suka fitar da Bulus daga haikali.—A. M. 4:1-3; 5:17-27; 21:27-30.