Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 13

Ku Rika Kaunar Juna da Zuciya Daya

Ku Rika Kaunar Juna da Zuciya Daya

Ku riƙa “ƙaunar juna da zuciya ɗaya.”​—1 BIT. 1:22.

WAƘA TA 109 Mu Kasance da Ƙauna ta Gaske

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

A dare na ƙarshe da Yesu ya kasance da almajiransa, ya yi magana sosai a kan nuna ƙauna (Ka duba sakin layi na 1-2)

1. Wane umurni ne Yesu ya ba almajiransa? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

A DAREN da Yesu ya rasu, ya ba almajiransa wani umurni. Ya ce: “Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma ku ƙaunaci juna.” Sai ya ƙara cewa: “Ta haka kowa zai sani ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.”​—Yoh. 13:​34, 35.

2. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa ƙaunar juna?

2 Yesu ya ce kowa zai san mabiyansa idan suna ƙaunar juna yadda ya ƙaunace su. Wannan furucin gaskiya ne a ƙarni na farko, kuma hakan yake a yau. Shi ya sa yake da muhimmanci sosai mu riƙa ƙaunar juna har a lokacin da yin hakan yake da wuya!

3. Mene ne za mu koya a wannan talifin?

3 Dukanmu ajizai ne, shi ya sa yake da wuya mu riƙa ƙaunar juna sosai. Amma, wajibi ne mu yi ƙoƙari mu yi koyi da Kristi. A wannan talifin, za mu koyi yadda ƙauna za ta taimaka mana mu riƙa zaman lafiya da mutane. Ban da haka, za mu koyi yadda za mu guji son kai kuma mu zama masu karɓan baƙi. Yayin da kake nazarin wannan talifin, ka tambayi kanka: ‘Me zan iya koya daga ’yan’uwa da suka ci gaba da ƙaunar juna duk da matsalolin da suke fuskanta?’

KU RIƘA ZAMAN LAFIYA DA MUTANE

4. Kamar yadda aka nuna a Matiyu 5:​23, 24, me ya sa ya kamata mu sasanta da ɗan’uwan da muka samu saɓani da shi?

4 Yesu ya koya mana muhimmancin sasantawa da ɗan’uwa da ya ɓata mana rai. (Karanta Matiyu 5:​23, 24.) Ya nanata cewa muna bukatar mu yi zaman lafiya da mutane idan muna so mu faranta wa Allah rai. Jehobah yana farin ciki idan mun yi iya ƙoƙarinmu mu yi zaman lafiya da ’yan’uwanmu. Jehobah ba zai amince da bautarmu ba idan mun ci gaba da riƙe wani a zuciya ko kuma muka ƙi sasantawa da mutumin.​—1 Yoh. 4:20.

5. Me ya sa ya kasance da wuya wasu ʼyan’uwa su sasanta?

5 Yana iya yi mana wuya mu sulhunta da mutane. Me ya sa? Ka yi la’akari da abin da ya faru da Mark. * Ya yi baƙin ciki sa’ad da wani ɗan’uwa ya zarge shi kuma ya yi baƙar magana game da shi ga wasu a ikilisiya. Mene ne Mark ya yi? Ya ce: “Na yi fushi sosai kuma na yi wa ɗan’uwan magana da fushi.” Daga baya, Mark ya yi da-na-sani kuma ya ce wa ɗan’uwan ya gafarce shi. Amma ɗan’uwan ya ƙi sasantawa da Mark. Da farko, Mark ya yi tunani, ‘Me ya sa zan ci gaba da ƙoƙari idan ba ya so mu sasanta?’ Amma, mai kula da da’ira ya ƙarfafa Mark cewa kada ya daina neman sasantawa da ɗan’uwan. Me Mark ya yi?

6. (a) Ta yaya Mark ya yi ƙoƙari ya sasanta da wani? (b) Ta yaya Mark ya bi shawarar da ke Kolosiyawa 3:​13, 14?

6 Mark ya bincika kansa kuma ya lura cewa a wasu lokuta yana ganin ya fi wasu mutunci. Ya ga cewa yana bukatar ya canja halinsa. (Kol. 3:​8, 9, 12) Sai ya koma wajen ɗan’uwan don ya sake neman gafara. Ƙari ga haka, Mark ya rubuta wa ɗan’uwan wasiƙu yana neman su sake zama abokai. Har ya ba ɗan’uwan kyauta da yake ganin ɗan’uwan zai so. Abin baƙin ciki, ɗan’uwan ya ci gaba da riƙe Mark a zuciya. Duk da haka, Mark ya ci gaba da bin umurnin Yesu cewa ya ƙaunaci ɗan’uwansa kuma ya riƙa gafartawa. (Karanta Kolosiyawa 3:​13, 14.) Ko da wasu ba sa son su sasanta da mu, ƙauna za ta taimaka mana mu ci gaba da gafarta musu. Ban da haka, za mu riƙa addu’a don mu sake zaman lafiya da su.​—Mat. 18:​21, 22; Gal. 6:9.

Idan wani yana fushi da mu, muna bukatar mu nemi hanyoyi dabam-dabam da za mu sasanta da mutumin (Ka duba sakin layi na 7-8) *

7. (a) Mene ne Yesu ya ƙarfafa mu mu yi? (b) A wane irin yanayi mai wuya ne wata ’yar’uwa ta sami kanta?

7 Yesu ya ce mu riƙa yi wa mutane abin da muke so a yi mana. Ya kuma ce ba mutanen da suke ƙaunar mu ne kaɗai za mu riƙa ƙauna ba. (Luk. 6:​31-33) Ko da yake hakan ba ya yawan faruwa, mene ne za ka yi idan wani a ikilisiya ya ƙi ya gaishe ka? Abin da ya faru da Lara ke nan. Ta ce: “Wata ’yar’uwa ta daina yi mini magana, ban san abin da na yi mata ba. Hakan ya sa ni baƙin ciki kuma ba na jin daɗin zuwa taro.” Da farko Lara ta yi tunani: ‘Ban yi mata kome ba. Ballantana ma, wasu a ikilisiya suna ganin cewa wannan ’yar’uwan tana da wani irin hali.’

8. Mene ne Lara ta yi don ta sulhunta da wata, me muka koya daga labarinta?

8 Lara ta ɗauki mataki don su sasanta. Ta yi addu’a kuma ta tsai da shawarar yi wa ’yar’uwar magana. Sai suka tattauna batun, suka rungumi juna kuma suka sasanta. Lara ta ce: “Amma daga baya, ’yar’uwar ta soma nuna halinta na dā. Hakan ya sa ni baƙin ciki sosai.” Da farko, Lara tana ganin cewa za ta yi farin ciki idan ’yar’uwar ta canja halinta. Amma Lara ta fahimci cewa abin da ya dace ta yi shi ne ta ci gaba da ƙaunar ’yar’uwar kuma ta riƙa “yafe” mata. (Afis. 4:32–5:2) Lara ta tuna cewa ƙauna “ba ta riƙe laifi a zuciya. Ƙauna takan sa haƙuri cikin kowane hali, da bangaskiya cikin kowane hali, da sa zuciya cikin kowane hali, da kuma jimiri cikin kowane hali.” (1 Kor. 13:​5, 7) Lara ba ta sake damun kanta don matsalar ba. Da shigewar lokaci, ’yar’uwar ta soma yi mata fara’a. Idan kuna zaman lafiya da ’yan’uwanku kuma kuka ci gaba da nuna musu ƙauna, ku kasance da tabbaci cewa “Allah mai ƙauna da salama zai kasance tare da ku.”​—2 Kor. 13:11.

KADA MU ZAMA MASU SON KAI

9. Kamar yadda Ayyukan Manzanni 10:​34, 35 suka nuna, me ya sa bai dace mu riƙa nuna bambanci ba?

9 Jehobah ba ya nuna bambanci. (Karanta Ayyukan Manzanni 10:​34, 35.) Muna nuna cewa mu ’ya’yan Jehobah ne idan ba ma nuna bambanci. Ƙari ga haka, muna bin umurnin da aka ba mu cewa mu ƙaunaci maƙwabcinmu kamar kanmu. Kuma muna zaman lafiya da ’yan’uwanmu.​—Rom. 12:​9, 10; Yaƙ. 2:​8, 9.

10-11. Ta yaya wata ’yar’uwa ta daina fushi da mutanen wata ƙasa?

10 Me ya sa yake da wuya wasu su daina nuna son kai? Alal misali, ka yi la’akari da abin da ya faru da wata ’yar’uwa mai suna Ruth. Sa’ad da Ruth take matashiya, wata mata daga wata ƙasa ta yi wa iyalinta wani mugun abu. Ta yaya hakan ya shafe ta? Ruth ta ce: “Na tsani kome game da wannan ƙasar. Ina ganin cewa haka halin duk ʼyan ƙasar yake, har ma da ’yan’uwa.” Mene ne ya taimaka wa Ruth ta daina jin hakan?

11 Ruth ta fahimci cewa ya kamata ta yi ƙoƙari ta daina irin wannan tunani. Ta karanta labarai da rahotanni daga littafin nan Yearbook of Jehovah’s Witnesses game da ƙasar. Ta ce: “Na yi ƙoƙari in riƙa tunani mai kyau game da mutanen ƙasar. Na soma lura cewa ’yan’uwan suna da ƙwazo a bautar Jehobah. Na fahimci cewa suna cikin ’yan’uwanmu da ke faɗin duniya.” A hankali, Ruth ta fahimci cewa tana bukatar ta nuna wa matar ƙauna. Ta ce: “A duk lokacin da na haɗu da ’yan’uwa daga ƙasar, ina ƙoƙartawa in nuna musu fara’a. Nakan yi musu magana kuma in yi musu tambayoyi don in san su da kyau.” Mene ne sakamakon yin hakan? Ruth ta ce: “Da shigewar lokaci, sai na daina fushi da mutanen ƙasar.”

Idan muna ƙaunar dukan “’yan’uwa” za mu guji nuna son kai (Ka duba sakin layi na 12-13) *

12. Wace matsala ce wata ’yar’uwa mai suna Sarah take da ita?

12 Wasu suna iya nuna bambanci ba tare da saninsu ba. Alal misali, Sarah tana ganin ba ta nuna bambanci don ba ta bi da mutane bisa ƙasarsu ko don suna da arziki ko kuma don matsayinsu a ƙungiyar Jehobah. Amma ta ce: “Sai na fahimci ina nuna bambanci.” Ta yaya? Sarah ta fito daga iyalin da suka je makarantar jami’a kuma ta fi son yin cuɗanya da mutane da suka yi makaranta. Akwai lokacin da ta taɓa gaya wa wani abokinta cewa: “Ina cuɗanya kawai da waɗanda suka karantu sosai. Nakan guji ’yan’uwa da ba su je makaranta ba.” Hakika, Sarah tana bukatar ta canja halinta. Ta yaya?

13. Mene ne za mu koya daga yadda Sarah ta canja halinta?

13 Wani mai kula da da’ira ya taimaka wa Sarah ta bincika kanta. Ta ce: “Ya yaba mini don kasancewa da aminci da yin kalami mai ƙarfafawa da kuma sanin Nassosi da kyau. Sai ya ce, yayin da muke ƙara sanin Jehobah, muna bukatar mu koyi kasancewa da halaye masu kyau kamar tawali’u da kuma juyayi.” Sarah ta bi shawarar mai kula da da’irar. Ta ce: “Na fahimci cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne nuna alheri da kuma ƙauna.” Saboda haka, ta soma bi da ’yan’uwa yadda ya dace. Ta ce: “Na yi ƙoƙari in fahimci halayensu masu kyau da ya sa Jehobah yake daraja su.” Mu kuma fa? Kada mu ɗauka cewa mun fi wasu domin mun yi makaranta! Idan muna ƙaunar dukan “’yan’uwa,” za mu guji nuna bambanci.​—1 Bit. 2:17.

KU RIƘA ƘARBAN BAƘI

14. Kamar yadda Ibraniyawa 13:16 ta nuna, yaya Jehobah yake ji sa’ad da muke karɓan baƙi?

14 Jehobah yana farin ciki sosai idan muna karɓan baƙi. (Karanta Ibraniyawa 13:16.) Yana ganin taimaka wa mabukata wata hanya ce da muke bauta masa. (Yaƙ. 1:27; 2:​14-17) Saboda haka, Nassosi sun ƙarfafa mu mu “dinga karɓar baƙi hannu biyu-biyu.” (Rom. 12:13) Idan muna karɓan baƙi, muna nuna wa mutane cewa mun damu da su, muna ƙaunar su kuma muna so su zama abokanmu. Jehobah yana farin ciki sa’ad da muka ba mabukata abinci ko abin sha ko kuma muka keɓe lokaci don mu yi cuɗanya da su. (1 Bit. 4:​8-10) Amma wasu abubuwa suna iya sa ya yi mana wuya mu riƙa karɓan baƙi.

“A dā, ba na son karɓan baƙi, amma na canja kuma ina farin ciki matuƙa” (Ka duba sakin layi na 16) *

15-16. (a) Me ya sa wasu suke jinkirin karɓan baƙi? (b) Mene ne ya taimaka wa Edit ta soma karɓan baƙi?

15 Muna iya jinkirin karɓan baƙi don dalilai da yawa. Ka yi la’akari da misalin wata gwauruwa mai suna Edit. Kafin ta zama Mashaidiya, ba ta son yin cuɗanya da mutane. Edit tana ganin cewa wasu sun fi ta iya kula da baƙi.

16 Edit ta canja ra’ayinta bayan ta zama Mashaidiya. Ta ɗauki matakai don ta riƙa karɓan baƙi. Ta ce: “Sa’ad da ake gina Majami’ar Mulki a yankinmu, sai wani dattijo ya gaya mini ko zan so wasu ma’aurata da za su zo yin aikin su zauna a gidanmu na sati biyu. Sai na tuna yadda Jehobah ya albarkaci wata gwauruwa a Zarefat.” (1 Sar. 17:​12-16) Edit ta yarda. Ta sami albarka kuwa? Ta ce: “Na yi farin ciki sosai domin sun zauna a gidanmu wata biyu maimakon sati biyu. A wannan lokaci, mun ƙulla abokantaka na kud da kud.” Ƙari ga haka, Edit ta sami abokai sosai a ikilisiya. Yanzu tana hidimar majagaba kuma tana gayyatar waɗanda suka fita wa’azi tare su zo gidanta su shaƙata. Ta ce: “Bayarwa tana sa ni farin ciki! Kuma gaskiyar ita ce, ina samun albarka sosai.”​—Ibran. 13:​1, 2.

17. Mene ne Luke da matarsa suka lura?

17 Wataƙila muna karɓan baƙi, amma yaya za mu kyautata yin hakan? Alal misali, Luke da matarsa suna nuna karimci sosai. Suna gayyatar iyayensu da danginsu da abokansu da kuma mai kula da da’ira da matarsa zuwa gidansu. Amma, Luke ya ce, “Mun lura cewa muna gayyatar abokanmu kaɗai.” Ta yaya suka inganta yadda suke nuna karimci?

18. Ta yaya Luke da matarsa suka inganta yadda suke karɓan baƙi?

18 Luke da matarsa sun koyi abin da karɓan baƙi yake nufi sa’ad da suka yi tunani a kan kalmomin Yesu: “Idan waɗanda suke ƙaunarku kawai kuke ƙauna, wane lada za ku samu?” (Mat. 5:​45-47) Sun ga cewa suna bukatar su yi koyi da Jehobah, Wanda yake nuna karimci ga kowa. Saboda haka, suka tsai da shawarar gayyatar ’yan’uwa da ba su taɓa gayyata ba. Luke ya ce: “Yanzu, muna jin daɗin yin cuɗanya da juna. Hakan na sa mu kusaci juna da kuma Jehobah.”

19. Ta yaya muke nuna cewa mu almajiran Yesu ne, mene ne ka ƙuduri niyyar yi?

19 Mun tattauna yadda ƙaunar juna za ta taimaka mana mu riƙa zaman lafiya da mutane. Mun koyi yadda za mu guji nuna son kai kuma mu zama masu karɓan baƙi. Wajibi ne mu guji riƙe ’yan’uwanmu a zuciya amma mu ƙaunace su da zuciya ɗaya. Idan muka yi hakan, za mu yi farin ciki kuma za mu nuna cewa mu almajiran Yesu ne.​—Yoh. 13:​17, 35.

WAƘA TA 88 Ka Koya Mini Hanyoyinka

^ sakin layi na 5 Yesu ya ce mutane za su gane Kiristoci na gaskiya ta yadda suke nuna ƙauna. Ƙaunar ’yan’uwanmu za ta taimaka mana mu riƙa zaman lafiya da su, ba za mu riƙa son kai ba kuma za mu zama masu karɓan baƙi. Hakan ba shi da sauƙi. A wannan talifin, za mu koyi yadda za mu riƙa ƙaunar juna da zuciya ɗaya.

^ sakin layi na 5 An canja wasu sunaye a wannan talifin.

^ sakin layi na 57 BAYANI A KAN HOTO: Wata ’yar’uwa ta nemi ta sasanta da wata. Da farko ba ta yi nasara ba amma ta ci gaba da yin ƙoƙari su sasanta. Sun zama abokai don ta ci gaba da nuna mata ƙauna.

^ sakin layi na 59 BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗan’uwa tsoho yana ganin cewa ’yan’uwa a ikilisiya ba sa son yin cuɗanya da shi.

^ sakin layi na 61 BAYANI A KAN HOTO: Wata ’yar’uwa da ba ta son karɓan baƙi a dā ta canja ra’ayinta, kuma hakan ya sa ta farin ciki matuƙa.