Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Zama Abokin Kirki a Lokacin Matsala

Ka Zama Abokin Kirki a Lokacin Matsala

Gianni da Maurizio sun yi shekaru hamsin suna abokantaka. Amma akwai lokacin da suka sami matsala. Maurizio ya ce: “Akwai lokacin da na yi wani kuskure babba kuma hakan ya sa muka daina abokantaka.” Gianni ya ƙara da cewa: “Maurizio ne ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Ina koyi da shi. Ban yarda cewa abokina zai iya yin wannan kuskuren ba. Na yi baƙin ciki sosai don na san cewa ba za mu ƙara zama abokai ba don abin da ya yi. Ban ji daɗi ba ko kaɗan.”

IDAN kana da abokan kirki, za ka ji daɗi, amma samun abokai na ƙwarai bai da sauƙi. Idan ka sami matsala da abokinka, me za ka iya yi don ku magance matsalar? Waɗanne darussa za mu iya koya daga labarin wasu a Littafi Mai Tsarki da suka kasance abokai na ƙwarai amma daga baya sun sami matsala?

SA’AD DA ABOKINKA YA YI KUSKURE

Dauda wanda shi makiyayi ne da kuma sarki yana da abokai na ƙwarai. Jonathan yana cikin abokansa. (1 Sam. 18:1) Amma Dauda yana da wasu abokai, kamar annabi Nathan. Littafi Mai Tsarki bai ambata lokacin da suka soma abokantakarsu ba. Duk da haka, akwai lokacin da Dauda ya nemi shawara daga abokinsa Nathan. Dauda yana so ya gina wa Jehobah haikali. Shi ya sa ya nemi shawarar Nathan don ya san cewa abokinsa ne kuma yana da ruhun Jehobah.2 Sam. 7:2, 3.

Amma akwai abin da ya faru da ya so ya ɓata abokantakarsu. Sarki Dauda ya yi zina da Bath-sheba kuma daga baya ya sa aka kashe maigidanta, Uriah. (2 Sam. 11:2-21) Dauda ya yi shekaru yana riƙe da aminci ga Jehobah kuma ya so yin adalci. Amma daga baya ya yi wannan zunubi mai tsanani. Me ya sa wannan nagarin sarkin ya yi haka? Bai san sakamakon laifinsa ba ne? Shin yana ganin zai iya ɓoye wa Allah zunubin ne?

To, mene ne Nathan zai yi? Shin zai aiki wani ne ya gaya wa sarkin laifin da ya yi? Wasu ma sun san yadda Dauda ya ƙulla don a kashe Uriah. Shin Nathan zai saka baki a wannan batun kuma ya ɓata abokantakarsa da Dauda ne? Wataƙila idan Nathan ya gaya wa Dauda laifin da ya yi, zai iya kashe shi. Balle ma, ya riga ya sami labarin yadda Dauda ya kashe Uriah da bai yi laifin kome ba.

Amma Nathan annabin Allah ne. Kuma ya san cewa idan ya yi shiru, zuciyarsa za ta riƙa damunsa kuma dangantakarsa da Dauda za ta yi tsami. Abokinsa Dauda ya yi babban laifi a gaban Jehobah. Saboda haka, yana bukatar taimako sosai kafin ya sake kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah. Hakika, Dauda yana bukatar aboki na ƙwarai a wannan lokacin kuma Nathan ne wannan abokin. Ya yi amfani da kwatanci mai kyau da ya dace da Dauda. Yadda Nathan ya ba da saƙon ya taimaka wa Dauda ya san yadda zunubinsa yake da muni. Bayan haka, Dauda ya tuba.2 Sam. 12:1-14.

Idan kana da aboki kuma ya yi kuskure ko kuma zunubi mai tsanani fa? Wataƙila za ka ɗauka cewa idan ka gaya masa kuskurensa, hakan zai ɓata abokantakarku. Ko kuma ka ɗauka cewa ka ci amanarsa idan ka kai ƙararsa wajen dattawan da za su taimaka masa. Idan ka ji hakan, me za ka yi?

Gianni da aka ambata ɗazu, ya ce: “Na lura cewa halin Maurizio ya canja. Ba ya gaya min abubuwa kamar yadda yake yi a dā. Sai na tsai da shawara cewa zan tambaye shi ko da yake yin hakan bai da sauƙi. Kafin in je, na yi ta tunani: ‘Me zan gaya masa da bai sani ba? Zai iya yin fushi da ni.’ Da yake mun yi nazari tare, na yi ƙarfin zuciyar yi masa magana. Na tuna cewa Maurizio ya taɓa ba ni shawara a lokacin da nake bukatar hakan. Ko da yake ba na son dangantakarmu ta yi tsami, ina so in taimaka masa don ina ƙaunarsa.”

Maurizio ya ce: “Abin da Gianni ya faɗa gaskiya ne. Na san cewa sakamakon kuskuren da na yi ba laifinsa ba ne ko laifin Jehobah ba ne. Saboda haka, na amince da horon da aka yi min kuma daga baya, na sake ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah.”

SA’AD DA ABOKINKA YAKE CIKIN MATSALA

Dauda yana da wasu abokai da suka taimaka masa sa’ad da yake shan wahala. Ɗaya daga cikin abokansa shi ne Hushai. Littafi Mai Tsarki ya ce Hushai: “Abokin Dauda” ne. (2 Sam. 16:16; 1 Laba. 27:33) Wataƙila ya yi aiki a fada kuma shi abokin sarki ne, mai yiwuwa sarkin yakan aike shi don ya kai saƙon da ya ƙunshi sirri.

A lokacin da Absalom ɗan Dauda yake son ya ƙwace sarautar ubansa, wasu Isra’ilawa sun goyi bayansa amma Hushai bai yi hakan ba. A lokacin da Dauda yake gudu, Hushai ya bi shi. Dauda ya yi baƙin ciki sosai don ɗansa da kuma wasu da ya amince da su sun ci amanarsa. Duk da haka, Hushai ya kasance da aminci kuma ya sadaukar da ransa da zuciya ɗaya don ya ɓata mugun ƙullin da aka yi ma Dauda. Hushai bai yi hakan kawai don yana aiki a fada ba, amma don shi abokin Dauda ne na ƙwarai.2 Sam. 15:13-17, 32-37; 16:15–17:16.

Abin farin ciki ne mu ga ‘yan’uwa maza da mata suna da haɗin kai ba don matsayinsu ba ko kuma hidimar da suke yi a ikilisiya ba, amma don suna ƙaunar juna. Halinsu yana nuna cewa su abokai ne na ƙwarai kuma sun damu da juna.

Abin da wani mai suna Federico ya fuskanta ke nan. Abokinsa Antonio ya taimaka masa sa’ad da yake cikin wata matsala. Federico ya ce: “Sa’ad da Antonio ya ƙauro ikilisiyarmu ne muka zama abokai. Mu bayi masu hidima ne a lokacin kuma mun ji daɗin yin aiki tare. Bayan wani lokaci, sai aka naɗa shi dattijo. Mu abokai ne sosai kuma ina yin koyi da shi.” Bayan wani lokaci, sai Federico ya yi wani zunubi mai tsanani. Nan da nan, ya nemi taimakon dattawa. An sauke shi daga hidimar majagaba da kuma bawa mai hidima. Ta yaya Antonio ya taimaka masa?

Sa’ad da Federico yake fuskantar matsala, amininsa Antonio ya saurare shi kuma ya ƙarfafa shi

Federico ya ce: “Na lura cewa Antonio ya yi baƙin ciki sosai don abin da ya faru da ni. Ya ƙarfafa ni sosai don in sake kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah.” Antonio ya ce: “Ina yawan tattaunawa da Federico domin ya saki jiki ya gaya min duk abin da ke damunsa.” Abin farin ciki, daga baya Federico ya dawo, kuma bayan wani lokaci, an sake naɗa shi majagaba da kuma bawa mai hidima. Antonio ya kammala da cewa: “Ko da yake yanzu ni da Federico ba ma ikilisiya ɗaya, mu aminai ne sosai.”

CIN AMANA NE KUWA?

Yaya za ka ji idan wani amininka ya yi watsi da kai sa’ad da ka shiga cikin wata matsala? Hakan zai ba ka haushi. Shin za ka iya gafarta masa kuwa? Shin dangantakarku za ta yi danƙo kamar yadda take a dā?

Ka yi la’akari da abin da ya sami Yesu kafin a kashe shi. Ya daɗe yana tare da manzanninsa masu aminci kuma sun kasance da haɗin kai. Har ma Yesu ya kira su abokansa. (Yoh. 15:15) Amma me ya faru sa’ad da aka kama shi? Manzannin sun gudu. Bitrus ya cika baki cewa ba zai taɓa barin Yesu ba. Amma a wannan daren, Bitrus ya yi musun sanin Yesu!Mat. 26:31-33, 56, 69-75.

Ko da yake Yesu ya san cewa shi kaɗai ne zai sha azaba, yana da hujjar yin fushi da almajiransa. Amma tattaunawar da suka yi da manzanninsa bayan da aka ta da shi daga matattu bai nuna cewa Yesu ya yi fushi da su ba. Yesu bai ambata kura-kuran almajiransa har da abubuwan da suka yi a daren da aka kama shi ba.

A maimakon haka, Yesu ya ƙarfafa Bitrus da wasu manzannin. Ya nuna cewa ya amince da su kuma ya ba su umurnin da za su riƙa bi sa’ad da suke wa’azi a faɗin duniya. Har ila Yesu ya ɗauke manzannin a matsayin abokansa, shi ya sa ba su manta da irin ƙaunar da ya nuna musu ba. Za su yi ƙoƙari don kada su sake cin amanarsa. Babu shakka, sun yi aiki tuƙuru don su idar da aikin da ya ba su.A. M. 1:8; Kol. 1:23.

Wata ‘yar’uwa mai suna Elvira ta tuna lokacin da ita da ƙawarta Giuliana suka sami saɓani. Ta ce: “A lokacin da Giuliana ta gaya min cewa ba ta ji daɗin abin da na yi mata ba, na yi baƙin ciki sosai. Tana da hujjar yin fushi. Amma abin da ya sa ni farin ciki sosai shi ne ta damu da ni da kuma abin da halina zai iya jefa ni ciki. Na ji daɗi cewa ba ta mai da hankali ga laifin da na yi mata ba, amma yadda hakan zai iya shafa na. Na gode wa Jehobah cewa na sami ƙawa da ta damu da ni sosai fiye da kanta.”

Saboda haka, me abokin kirki zai yi sa’ad da abokinsa ya yi wani babban kuskure ko laifi? Ya kamata ya gaya masa gaskiya in da hali amma da basira. Irin wannan abokin yana kama da Nathan da Hushai da suka kasance da aminci a mawuyacin lokaci. Ƙari ga haka, kamar Yesu muna bukatar mu riƙa gafarta wa mutane. Kai irin wannan abokin ne?